Romantic Hausa novels complete
An_Cuci_Hijabi
Barka da shigowa wannan farfajiyar gida namu, inda muka zabo littafi Mai zafi guda ɗaya na romantic Hausa novels complete mai taken abinda muka rubuta a sama, muna fatan asha karatu lafiya mun gode.
Tana shiga ta hau rafka sallama, amma ba wanda ya amsa mata. Hakan yasa ta danne kai ta shiga. Amina ta gani a tsakiyar gida tana jibge kayan kwalliya, tana kwaliya cike da iyayi. Kusa da ita, Ummi ta samu wuri ta zauna tana cewa, "Au, dan baki da mutunci ne? Ina tafaman rafka sallama amma kika yi banza dani?"
Sai a lokacin Amina ta dago kai ta kalli Ummi kafin tace, "Toh, ba ki ga kwalliya nake yi ba? Kuma sallamarki har wata sallama ce da zan amsa?"
Sosai Ummi ta ji haushin maganar, tace, "Kamarya? Ban gane sallamata ba, sallama bace." Ta fadi hakan tana kallon Amina. "Ni dai ba ma haka, ki fada abin da ya kawoki, dan ban so Inna ta dawo ta sameki a nan."
Jiki asace, Ummi tace, "Yauwa, ina wancan atamfarki naki?"
"Tananan," Amina ta amsa a dakile.
"Yauwa, ita nake so ki ara min. Gobe, insha Allah, zan dawo miki da ita," Ummi ta fada da murna.
Wani wulaƙantaccen kallo Amina ta watsa wa Ummi kafin tace, "Tabdijam! Ba ki da hankali? Kayan da suka fi kowane kaya kyau a cikin kayana zan baki? Hankali nema kwata-kwata Allah bai hore miki ba."
Ummi ta kalle ta cikin takaici tana cewa, "Yanzu, Amina, ka ce ki ara min kaya shine kike yin kunfar baki?"
"Ina yi d'in! Idan fitsari wasa ne, za ki zama cikin ku sai dai qaryar makaranta ma sai ace private za a yi. Kalli gidanku, babu mai kyanshi a wannan layin, amma dai ga kayan sawo za ku ara."
"Toh ba zan bayar ba, dan uban mutum," Amina ta fadi cikin tsananin kishi.
Nan take Ummi ta mike tana cewa, "Kutumar uba! Amina, ubana fa kika ambata? Ai kuwa sai na ci ubanki, kuma wallahi yau a cikin garin nan sai na ga uban da zai tsaya miki, dan uwarki."
Tafadi hakan ne tare da cin d'amara da dan karamin hijabin kanta. Ganin cewa Ummi da gaske take, kuma tana da karfi, yasa Amina ta sassauta murya tana cewa, "Ke, nifa ba musifa nake neman ki da ita ba. Dan Allah, kitashi ki fita daga gidan nan, kar Innata ta dawo ta sameki, wallahi duka zata miki."
"Bazan fita ba!" Ummi ta amsa tana kallon Amina da zafin rai. "Sai dai kafin uwar taki ta dakeki, ni zan fara cin ubanki har ma da uwarki."
Ta karasa maganar sanda ta cakumo wuyan rigar Amina! Nan da nan kokuwa ta kaure, kasancewar gidan babu kowa. Da kyar Amina ta samu ta qwace kanta, da gudu ta fita daga gidan ba tare da d’an kwali a kanta ba. Itama Ummi_da_gudu_tabi_bayanta da_d’amararta.
Wani kukan kura Ummi tai tana dakawa Amina wawura, ta turmusheta. Haka suka dunga kokuwa a kasa, suna tasowa da faduwa. Nan take wajen ya cika da yara. Da kyar Amina ta samu qwatar kanta karo na biyu, ta kuma yi hanyar gidansu Ummi domin tasan can kadai zata tsira.
romantic Hausa novels complete part 2
A lokacin itama Ummi da gudu tabi bayanta, haka ma yaran kallon kokuwa suka biyo bayansu. Dama dai-dai kofar gidan su Ummi ne Amina ta zube a kasa, inda Ummi ta daka tsalle ta fada kan cikinta.
A wannan lokacin kuwa, motar su Hassina ta iso kofar gidan. Yara sai tafi suke suna cewa, "Kucasu! Arna! Ku casu, bamai rabaku."
Da sauri dady ya fito daga mota ya hango jini sai bulbula yake akan yarinyar da ake duka. Tare suka iso wajen, su Imran da su Abba. Hanyar da su Ammi ke ji ya sa suka yi tsit, suna so su ji wanne irin rikici ake musu a kofar gida.
Jin muryar su Imran ne ya tabbatar musu da Ummi ake fada. Cike da jarumta, da kyar Imran ya yi nasarar d’aga Ummi daga kan Amina. Inda Amina ko numfashi ba tayi, cike da firgici Alhaji Yusuf ke tambayar wa cece yarinyar, domin harga Allah bai gane taba.
A lokacin kuwa Ummi tana ta tiriri, furu-furu kamar mahaukaciya. Sai cika take tana batsewa, tana cewa, "Akame za'a rabani da ita?"
Imran ya daka mata tsawa yace, "Ke jaka, inace kashe yar mutane zaki yi?"
Nan take tsanar Imran ta cika zuciyar Ummi. Tayi tsalle tace, "Ni ba_jaka_bace, kaje_ka nemo_jakarka."
Mamaki ya kama Alhaji Yusuf da su Hassina gaba d'aya. Abba ko juyawa yayi domin baya tunanin zai iya magana. Wani lafiyayyen mari Imran ya d’auke Ummi dashi, take ta rike kunci tana kuka wasu zafafan hawaye suna biyo bayan kuncinta.
Imran yace, "Idan kina cin qasa ki kiyaye rashin kunyarki, kada ki kuskura ki raina ni!"
Ummi ta ji kamar an fasa mata bokiti na tsanar Imran. Ta runtse ido tana kuka da tsawa tace, "Uwarka ce jaka, kuma ubankane mahaukaci! Kai ne banza, amma ni ba haka bane!"
Ummi ta fashe da kuka mai tsanani. Cak! Imran ya tsaya yana kallon ta, wani mahaukacin mari ya ƙara wanketa dashi. Tsabar azaba yasa Ummi kasa tsayuwa, tana durƙushewa a ƙasa. Imran ya ɗaga hannunsa zai ƙara wanketa da wani marin, amma da sauri Dady ya riƙe hannunshi.
"Haba ɗan saurayi, kayi haƙuri mana. Ka dubi wannan yarinyar ƙaramace, tsayawa ka kula ta ba shi ne jarumtarka ba. Kai fa namiji ne, kuma namiji yana nuna juriya da girma," Dady ya fada cikin lallashi.
romantic Hausa novels complete part 3
Imran ya aje hannunsa cikin takaici yana cewa, "Wannan yarinyar fa ba ƙaramar ba ce! Tsananin dabbanci da rashin tarbiyya ne ya dame ta, ba yarinta ba. Kuma wallahi sai na koya mata zama."
Yana kai wannan maganar, sai ya juya fuuu! zuciyarsa cike da kunar rai. A wannan lokaci, Khadijat ta fito daga gida tare da Ammi, amma baƙin cikin halin Ummi ya hana su fitowa tun da farko. Baba kuwa tana sallar La’asar ne.
Khadijat ta tsaya bakin ƙofa tana kallon budurwar da ta gani a cikin mutane. Kyakkyawar yarinya ce, duk da haka, tana jin cewa akwai wata kama tsakaninsu. A hankali ta ƙarasa inda Ummi take, suna hada ido da Hassina da Dady. Ba shakka, Khadijat ta gane yarinyar – y'ar uwarta ce. Kukan Ummi ne ya dawo da ita daga tunanin da ta shiga.
Cike da jin haushin halaye da d'abi'un Ummi, Khadijat ta kama ta da karfi, tana ja da ita cikin gida. Amina kuwa, wasu mata suka d'auke ta suna cewa, "Allah yasa ba kashe ta tayiba..."
A take haka su Hassina suka shiga gida, zuciyoyinsu acinkushe da baƙin ciki. Da zarar Khadijat ta shiga gida da Ummi, ta wanke ta da wani lafiyayyen mari sannan ta tura ta wajan bandaki tana cewa, "Je ki wanke kanki, mahaukaciya kawai."
Ummi ko, aduniya, ta ƙi jin cewa ana daura mata wata halitta mai kama da ita. Haka ta yi wanka tana kuka, zuciyarta cike da takaici.
Su Dady kuwa, basu shiga gidan ba, kai tsaye asibitin da aka kwantar da Amina suka tafi.
"Ina ikon Allah! Yanzu Hassana, kece kika girma haka?" Baba ta furta cikin mamaki. Hassana ta sunkuyar da kanta tana murmushi, domin ba ta son nuna girman kai.
Ammi tai murmushi lokacin da take cewa, "Gata da hankali, tubarkallah! Ba irin wannan yarinya mai rashin ji ba."
Baba ta yi magana cikin fushi, "Ai naga gaɗa ta yi a wajanku, shi yasa nake cewa ku daina ta kurawa yarinyar nan." Tana mai nuna rashin jin daɗi.
romantic Hausa novels complete last part
"Sai na je na same shi wancan ɗan iska," Baba ta ƙara da fushi, "na tambayi dalilin da yasa zai taɓa min jika."
Ammi cikin ladabi ta ce, "Ai ke ki dubi abin da jikarki ta yi, ko kuma ba ta ganin abin da ta aikata?"
"Allah ya sa ba ta ji wa yarinyar nan ciwo ba..." Baba ta ce, cikin takaici.
"Ai haka za ki ce. Ku d'in ba ku daura wa mutane irin wannan gindi ba? Wallahi a ƙarshe za a ga bajinta! Kowa ya san halin yaran nan!"
Khadijat dai tana gefe, tsabar baƙin ciki ko magana bata iya yi ba. Mom kuwa tana jinsu, ita abin dariya ma yake bata. Sai alokacin da Ammi take hira da Baba kamar ƙawayenta ne.
Bayan Ummi ta fito daga wanka, ko kallon inda suke bata yi ba. Ta ratse ta gefensu ta d’au kayan ta, ta shiga d'akin Ammi ta sa su. Cikin zuciyarta, ta ji tsantsar tsana ga mutanen garin, tana cewa kowa ya fita mata a rai tunda suke kira gareta "mahaukaciya," duk kuwa da ita ta san tana da hankalinta.
Anan muka kawo abinda ya sawwaka na wannan romantic Hausa novels complete, kuma littafin da muka dauka shine an cuci hijabi, idan ba buƙata zaka iya neman cikakken labarin akan internet ko social media.
0 Comments