Romantic hausa novels complete download part 1
A_gidanmu_take
Labarin da muka gabatar a wannan shafi domin nishadantar daku yana daya daga cikin mafi kyawun romantic Hausa novels complete download wanda zaka iya samu a wannan gida, asha karatu lafiya. Kar a manta da sharing.
"Haba Ahmad, me ya sa ba za ka amince da kaddara ba? Ka sani kowane ɗan Adam yana da nasa kaddarar, na wasu ma fiye da na wasu. Amma kai sam ba ka taɓa karɓar kaddararka ba."
Ahmad, wanda aka kira da suna, ya ɗago kansa yayin da hawaye ke zuba masa. Fuskar sa ta yi jajur, ya buɗe baki da niyyar magana, amma ya kasa furta komai. Sai kawai ya fashe da kuka mai tsanani, kamar mace, har yana shesheka. A ƙarshe, cikin wahala ya ce, "Haba Habeeb, me zai hana in yi kuka? Ai kasan halin da nake ciki. Idan ban yi kuka ba, me zan yi?"
Habeeb ya gyara zamansa sannan ya ce, "Ya kamata ka tashi ka yi addu'a Ahmad. A lokacin da mutum ya tsinci kansa cikin matsanancin hali, addu’a ita ce mafita ga kowane musulmi."
Ahmad ya ɗaga hannu cikin rashin jin daɗi, "Ka bari Habeeb! Ka bar ni kawai in ji da abinda ke damuna, ba surutunka nake bukata ba. Kasani na yi babban rashi a rayuwata, wanda ba zan manta da shi ba har abada. Tun da na rasa Fateemah, komai ya yi min wuya. Na zalunce ta, na wulaƙanta ta, na yi mata abin da ba za ta manta da ni ba har abada. Ina Fateemah? Shin tana raye, ko ta mutu?" Ya dakata na ɗan lokaci kafin ya cigaba da cewa, "Idan tana raye, ya Allah, Ka bayyana min ita. Idan kuma ta mutu, Allah Ka sa haske kabarinta!" Ya ƙarasa maganar tare da fashewa da kuka mai ƙarfi.
Habeeb, duk da dauriya, shima ya yi hawaye tare da nuna tausayin abokinsa. "Wai Bintu, kina ina? Ki yi sauri mana, kin san fa Mommy tana jiranki a mota!" Habeeba ta kira cikin gaggawa. "Ganinan Sis, gyalena nake nema, ban gan shi ba," wata murya mai laushi ta amsa daga daki.
"Ki ɗauki nawa mana daga wardrobe, ki bari mu tafi." Habeeba ta ce cikin rashin haƙuri.
"To, ai na ɗauka. Ganinan_zuwa." Bintu tace yayinda_take_yafa_gyalenta a jikinta.
"Ai dama nasan ko ban ce ba, za ki ɗauka." Habeeba ta ce tana ɗan harar Bintu.
Bintu ta fito daga matakalar step, tana tafiya cikin nutsuwa. Kyakkyawa ce, fara, doguwa kuma siririya, tana da manyan idanuwa da ƙaramin baki. Tana ƙoƙarin gyara gyalen da ta ɗora.
"Haba Hussaina, kinsan bamu cika faɗa dake ba. Ni kuma ai naga kema kin ɗauki abuna." Bintu ta faɗa tana murmushi.
"Kullum haka za ki ce. Sai ki yi laifi sannan ki dawo da sanyi murya. To yanzu dai muje, kinga Mommy ta yi min missed calls guda shida." Habeeba ta ce tana duba wayarta. "To, muje." Bintu ta amsa.
Daga nan suka fito duka biyun daga falo cikin sauri, suna nufin motar da Mommy ke jira.
Suna fitowa daga falon, Habeeba ta kira direba cikin sauri, "Driver!" Ya amsa, "Gani, Hajiya."
"Ina Mommy?" Habeeba ta tambaya. Direban ya ce, "Ai Hajiya ta dade da tafiya, ta ce ba za ta iya jiran ku ba. Idan kun gama, ku sameta a gidan abinci."
Romantic Hausa novels complete download part 2
"To shikenan, ka muje," Habeeba ta ce. Direban ya amsa da "to," suka shiga mota suka tafi. Bayan sun isa, direba ya yi parking, sai na ga sun shiga wani wuri mai kyau. Ma’aikata sanye da uniform suna rabawa mutane abinci, wasu kuma suna dafawa. Wasu na wanke kwanuka. Daga dukkan alamu gidan abinci ne mai suna a garin Adamawa. Na ɗaga kaina, sai naga an rubuta Hassy and Hussy’s Kitchen a bakin ƙofar.
Suna fitowa daga mota, idanun mutane suka koma kansu. Mutane suna ta faɗin, "Kaga 'yan biyun Hajiya, ba ku da kamunku." Wasu suka ce, "Ku je gida, ku ce ta faɗi." Habeeba ce kadai ta amsa da, "Sannunku," yayin da samari ke cewa, "Barka da war haka." Ita kuma Bintu sai murmushi take.
Na ga sun nufi wata mata kyakkyawa da za ta kai shekara 40. Habeeba ta faɗa kan cinyarta tana cewa, "Mommy, shine kika tafi kika barmu."
Matar da ake kira da Mommy ta murmusa, tsananin kamanta da Habeeba ya bayyana a fili. Tace, "Ai ba dole in tafi ba, kun tsaya kuna ɓata lokaci, kuma kun san yau ranar biyan ma’aikata ne."
"Mommy, ai Bintu ce ta tsayar da mu. Kinsan yadda take, tana yin abu kamar karkashi," Habeeba ta yi dariya.
"A’a, kar ki sake ki zagamin ya zo maya, My Bintu. Zo ki zauna anan," Mommy ta ce da kulawa.
Bintu ta yi murmushi tana cewa, "Mommy, yau ni zan dafa stew da kaina." Mommy ta kalli Bintu cikin tausayi, "Haba Bintu, me yasa za ki gaji da kanki? Zauna ki huta, kin ji, My Bintu."
Bintu ta sake murmushi, "A’a, Mommy, kibari kawai, zan yi." "To shikenan, ba zan hanaki ba. Jeki yi," Mommy ta amince.
Ahmad ya kalli Habeeb cikin damuwa, "Dama na yi niyyar tafiya yau, amma ba zan iya tafiya na bar ka cikin wannan halin ba."
Nagode, Habeeb. Allah ya barmin kai. Dan Allah, Habeeb, ko bayan na mutu, idan ka samu My Teemah, ka aureta. Kai kaɗai na yarda da kai, kai kaɗai na san za ka riƙe ta da amana. Ka san irin wahalar da ta sha a hannuna, ka san na zalunceta, na ci amanarta. Dan Allah kayi min wannan alƙawari."
"Ahmad, ka daina irin waɗannan maganganun. Ba su da daɗi a ji. Me ya sa kake maganar mutuwa alhalin ba ka ga Fateemah ba tukuna?"
"Habeeb, insha_Allahu, bazaka mutu_ba har sai_kaga_Fateemah. Ka nemi yafiyarta, sannan ku gina rayuwa mai kyau tare. Ina da yakinin cewa Fateemah za ta yafe maka."
Ahmad ya girgiza kai cike da damuwa, ya ce, "Habeeb, bana tunanin My Teemah za ta iya yafe min, ko bayan raina ne. Babu wani abu da yake damuna kamar yadda Mommy ta ɗauki wannan al’amarin da tsanani. Ka duba fa, shekara ɗaya kenan ban ga Mommy ba. Yaya zan ci gaba da rayuwata?" Ya ƙare maganar yana fashewa da kuka mai tsanani, abin tausayi.
Habeeb kuwa ya kasa furta ko da kalma ɗaya. Mamaki ya mamaye shi, ganin Ahmad, wanda ya saba da ɗaukar abubuwa da ƙarfin zuciya, yana kuka haka. Yana jin damuwar Ahmad sosai, kuma yana son taimaka masa, amma bai san ta ina zai fara ba. A ƙarshe, ya ɗaga hannu sama yana addu'a, "Ya Allah, ka kawo mana ƙarshen wannan matsalar. Ameen."
BINTU
"Mommy, me yasa Bintu ke zubar mana da kima? Ki duba fa, yanzu tana tare da ma’aikata tana yi musu aiki. Gaskiya, wannan abin kunya ne."
Romantic Hausa novels complete download part 3
Mommy ta yi murmushi ta ce, "Habeeba, ki bi rayuwa a hankali. Rayuwar duniya tana tafiya ne da hankali. Wanda ba ta zo gare shi ba, tana jiransa."
Habeeba ta tabe baki tana cewa, "Gaskiya, Mommy, kina fifita Bintu. Dama na san ba ni kike so ba."
Mommy ta girgiza kai cike da tausayawa. "Habeeba, ba haka ba ne. Babu wanda zai haifi ɗa ya ƙi shi, sai idan kaddara ce. Ki daina jin haka."
Idanunta suka fara cika da hawaye, amma ta juya a hankali ta goge su domin kar Bintu ta gan su.
Bintu kuwa tana cikin girki tare da ma’aikatan gidan, tana ɗan hira da su, duk da cewa ba ta cika son magana ba.
Wata daga cikin ma’aikatan, Nabeela, ta ce, "Bintu, ina son yi miki wata tambaya." Bintu ta kalle ta cikin kulawa, "To, Nabeela, ina jin ki."
"Amma Allah ya sa ba za ki ji haushi ba." Bintu ta ce, "Aa, ba komai, yi tambayarki."Nabeela ta ɗanyi jinkiri, sannan ta ce, "Hajiyarki ce ta haife ki?"
Bintu ta ɗan tsuke fuska. "Haba Nabeela! Wane irin tambaya ce wannan? Ai kin san mu 'yan biyu ne, ni ce babba!"
Nabeela ta girgiza kai, ta ce, "Gaskiya Bintu, ba kowa zai yarda da hakan ba. Ki duba yadda Habeeba take kama da Hajiya sosai, amma ke babu wata alaƙa tsakanin ki da ita, ko a kamanni ko halayya."
"What are you saying, Nabeela?" muryar Mommy ta tsinkayo daga gefe. Tun farko tana jin duk hirar su. Ta taso ta tambayi Bintu, "Ko kin gama haɗin stew ɗin?"
Nan take suka juyo da sauri, ganin yadda Mommy tayi magana da karfi. Jikin Nabeela yayi sanyi sosai, ganin yadda yanayin Mommy ya sauya cikin kankanin lokaci.
"Haba Nabeela, wannan wace irin magana ce? Me yasa kike son sa shakku a zuciyar yar da na haifeta a cikina? Shin baki san akwai ‘yan biyun da ba su cika kama da juna ba?"
"Meyasa mutane ba ku gane ba? Da ace ba ni na haifi Bintu ba, da ba za a taba cewa ni na hada ta ba." Saikuma tayi shiru da bacin rai. "Gaskiya bana son irin wannan tambayar."
"Nan da yau kada ki sake haduwa da Bintu, domin ba zan iya sanin me zaki ce mata gaba ba."
"Kiyi hakuri Hajiya, insha Allahu hakan ba zai sake faruwa ba," inji Nabeela cike da nadama.
"Banason dogon magana, Nabeela, na riga na gama magana," Hajiya ta mayar mata da tsawa. "Bintu, wuce mu tafi," Mommy ta fada cikin bacin rai.
"To, Mommy," inji Bintu, wacce tun farko take sunkuyar da kanta lokacin da Mommy ke fada. Da zasu tafi ne sai ta daga kai ta dube Nabeela, wacce kunyar Mommy ta gama isarta.
AHMAD
Da kyar Habeeb ya samu ya lallashe shi yayi shiru.
"Ahmad, gobe idan Allah ya kaimu kafin in tafi, dan Allah inason muje asibiti a duba lafiyarka, dubi yadda kake karami," inji Habeeb.
"Ba sai na je asibiti ba. Maganin cutana ba a asibiti yake ba, maganin cutana My Teemah ne. Idan na same ta zan warke, insha Allahu," Ahmad ya amsa.
"To shikenan, yanzu dai ka kwanta ka huta sannan ka rage damuwa saboda zata iya haifar maka da cuta," inji Habeeb.
"Nima bari na kira gida in fada musu ba zan samu dawowa ba sai gobe." Da Mommy ta iso wajen Beebah, ta samu kujera ta zauna tana cike da damuwa. Beebah bata ga fuskar tambaya ba, sai ta karasa wajen Bintu tace, "Bintu, me yasa ran Mommy ya bace haka?"
Romantic Hausa novels complete download part 4
"Ba komai sis," inji Bintu, saboda tasan idan Beebah ta ji maganar, ba za ta dauka da sauki ba. "Yaya zaki ce ba komai bayan gashi ranta a matukar bace?" "Nace miki ba komai, ke meyasa kin fiye naci ne?" inji Bintu. "Ko zaki dake ni ne?" cewar Beebah.
"Niban ce zan dake ki ba, dan haka ki matsa min anan," Bintu ta mayar mata da martani. "Zaki fara ko Beebah? Meyasa baki girmama ni ba? Ai kin girmeta," inji Mommy cikin kulawa.
Beebah ta tabe baki tana cewa, "Wai da nayi magana sai ace na girmeta." "Yanzu dai ku tashi mu tafi gida, yau yayanku zai dawo," cewar Mommy.
"Yee, Mommy, dagaske kike?" cewar Beebah da murna. "Dama nataba miki karya ne?" Nan wayar Mommy ta fara ringing. "Yawwa, ga shi yana kira," Mommy ta amsa wayar.
"Hello, my son, ya kake? Ok, sai gobe? Amma me yasa yau ba zaka dawo ba? Ok, to Allah ya kaimu goben." Sai ta kashe wayar. "Kun ga yayanku yace sai gobe zai dawo," Mommy ta fada musu.
"Kai amma naji haushi, Mommy," cewar Beebah. Mommy ta ce, "Yau da gobe duk daya ne, Beebah. Kawai muyi addu'a Allah ya dawo dashi lafiya."
"Ameen," cewar Bintu.
Washe gari bayan sun gama breakfast, Habeeb ya ke cewa Ahmad, "To, kaga ni yau zan tafi kuma ba zan dawo nan da wuri ba. Saboda wannan zuwan dakyar Mommy ta barni. Acewarta bata son na yi nesa da ita."
"Dan Allah, Ahmad, ka da ka saka damuwa a ranka sannan kuma kada ka gaji da zuwa gidan ku neman tuba a wajen Mommynka."
"Aa, Habeeb, ba zan iya zuwa inda Mom take ba gaskiya. Saboda idan ta gan ni, bacin ranta karuwa yake. Har tana barazanar tsine min idan har na sake zuwa ba tare da Fateemah ba."
"Innalillahi wa'inna ilaihiraji'un. Ahmad, abun har ya kai haka ne?" "Wlh, Habeeb, shiyasa kaga damuwata tayi yawa, na rasa yadda zanyi. Yanzu ma tafiyar da zakayi ba na so ba, koba komai kana rage min kewa."
"Amma yana iya, idan ka je ka gaishe da Mommy da kannen ka duka. Allah ya bar zumunci." Habeeb yace, "Ameen."
Ahmad_yace, "Kashirya_na_kaika_airport, karka_makara_ka_rasa_jirgin.""Beebah, kin san yau bro zai dawo. Kizo mu shiga kitchen, dukanmu mu hada masa delicious abinci."
Romantic Hausa novels complete download last part
Bintu tace, "Ok sis, karki samu damuwa, muje."
Suka tashi suka shiga kitchen suna hira. Mommy tana kallonsu tana murmushi, tana addu’a cikin zuciyarta, "Allah ya kara hada kan my twins."
Tafiya suke a mota suna hira shida Habeeb. Habeeb yana kara jaddada masa akan ya kula da kanshi, ya daina yawan damuwa.
Ahmad yace, "Kaga, karka dameni. Tun jiya kana maimaita abu daya kamar karatu."
"Ohh, dama_nasan_bazaka taba_canza halinka_ba, Ahmad."
"Eh, naji, ba zan canza ba." Da haka har suka isa airport.
Bintu tana aiki a kitchen, Beebah kuma tana ta surutu. Banda "eh", "aa", "to", babu abinda Bintu take cewa har suka gama hada fried rice da kaza.
Bintu ta hada sobo mai cucumber. Mommy ta ce, "Yanzu_na tura_driver ya_tafi_dauko_shi a airport. Wai_ya_karaso."
"Yeeeee, Mommy, ai da kin fada min da tare zamu tafi," Beebah ta fada da murna. "Kai Beebah kin fiye gaggawa."
"Haba, Mommy, ya zanyi gaggawa? Yau fa kusan mako biyu ban gan shi ba, sai waya." Bintu kuma murmushi kawai take yi.
Horn suka ji a bakin gate. Nan take Beebah ta fita da gudu tana "Oyoyo yaya! Oyoyo!" Kafin driver ya gama parking harta fara buga motar. Sai da ya fito da sauri yana "Oyoyo my sis."
Nan ta rungume shi sosai tana murna. "Ina dayarki?" Ya tambaya. "Tana falo ita da Mommy.""Ok, mu shiga daga ciki."
Suna tafiya tana rike da waist dinsa har suka shiga falon. Tana_cewa, "Yaya ka_kawo_min tsaraba_toh?"
"Mu shiga gida tukunna, kinsan tsarabarki ta daban ce." Mommy ta ce, "Oyoyo my son, sannu da zuwa." Nan itama ta rungume shi tana murna. Bintu ta tsaya tana murmushi.
Kina gani fa ‘yar uwarki tazo tayi min oyoyo, amma ke kina tsaye." Daga nan Bintu taje ta rungume shi, yahada su uku yana murna.
Wannan shine ɗan abinda zamu iya kawowa, domin haka ka iya binciken ragowar a wannan gida namu. A gidanmu romantic Hausa novels complete download ne domin kowa da kowa ya amfana
0 Comments