Yadda ake wankan haila a musulunci

Yadda ake wankan haila a musulunci

Barka da zuwa wannan gida wanda ba'a munafunci a cikinsa, a yau idan mai duka ya nufa zamu yi rubutu ne akan yadda ake wankan haila a musulunci, kunga kenan kai tsaye rubutun ya ta'allaka ne akan mata ko nace iyayen gida. Fatan ubangiji mai ruwa da iska ya amfanar dasu da ilimi mai albarka. 

Ayi sani cewa wannan wanka na tsarki duka shi ake yi idan da faruwar wadannan abubuwa kamar haka;

1. zuwa juma'a

2. janaba

3. haila

4. biki (jinin haihuwa)

5. zuwa idi.

Yadda ake wankan haila a musulunci

Yadda ake wankan haila a musulunci, da sauran wanda muka lissafo a sama duka iri daya ne, sai dai kuma duk da cewa wankan iri daya ne, amma akwai banbamcin niyya lokacin da za'a yi wankan.

1. Wankan zuwa masallacin juma'a; Addini ya bada umarnin ayi wankan tsafta na tsarki a duk ranar juma'a idan za'a je masallaci. Anso ka fara wankan tsarki kafin kayi na yau da kullum, amma wasu scholars sunce ka iya yi bayan kayi wankanka. 

2. Wankan janaba; Tambaya > Menene janaba? Amsa > Janaba shine fitar wani farin ruwa mai dunkudar juna wanda yake fita bayan jin sha'awa mai karfi ko kuma yayin saduwa, wanda fitarsa ke sanya jindadi. Kowane baligi ko baliga ana bukatar yayi wankan tsarki a duk lokacin daya fitar da maniyyi, walau yayi mafarki ne ko kuma ya sadu da iyalinsa, koda kuwa wasa yayi da gabansa indai an samu fitar maniyyi tofa wankan tsarki ya kama shi. 

3. Wankan haila; dama dai wannan rubutu namu munyi shine takamaimai akan yadda ake wankan haila a musulunci, amma tunda ya kasance dukkanin wankan iri daya ne, kawai niyya ce banbamci to kawai kinga kenan sai mu yisu a waje guda. Haila shine jinin al'ada wanda mata kanyi duk karshen wata ko kuma duk karshen wani lokaci, wannan jini na haila yanada matukar amfani sosai da tasiri a rayuwar kowace mace, kuma yana da kyau kowace mace tasan yadda ake wankan haila a musulunci.

4. Wankan biki (jinin haihuwa); Shi kuma wankan biki wanka ne wanda mai jego keyi bayan daukewar jinin haihuwa, wato bayan kin haihu dole ne za'a samu fitar wani jini wanda muke cewa biki a hausa, to a duk lokacin da aka samu wannan jini ya tsaya to maijego ya kamata tayi wankan tsarki, yin wankan tsraki shi zai bata dama ta cigaba da ibadarta yadda ya kamata.

5. Wankan zuwa masallacin idi; kamar yadda sunan ya nuna, wanka ne wadda kowane musulmi ya kamata yayi kafin ya tafi zuwa masallacin idi, wato lokacin karamar sallah ko babbar sallah yanada kyau kayi wankan tsarki wanda a yanzu zamu ce masa wankan idi, domin kayi tsaf ka gaida ubangijinmu. 

Yadda ake wankan haila a musulunci daki-daki 

Zamu yi amfani da fatawar wani babban scholar na hausa, yadda yayi bayanin yadda ake wankan haila a musulunci cikin sauki, kamar yadda yace, yadda ake wankan haila na tsarki na ya rabu gida biyu; akwai 

1. Siffar wadata

2. Siffar kamala

(1) Yadda ake wankan haila a musulunci a siffar wadata; Nima kaina nafi son wannan siffa ta wanka domin babu wani stress a tattare da ita, ga yadda ake yin wannan wanka.

Zaki samu ruwa mai tsarki, sannan ki shiga bayi, karki manta da yin addu'ar shiga bandaki, kuma da kafar dama. Ki cire tufafinki sannan kiyi niyyar soma wanka, ki debi ruwa ki watsa yabi ko'ina a jikinki. idan kuma swimming pool ne sai ki fada bayan kinyi niyya. ki kurkure baki, sannan ki shaka ruwa a hanci, bayan kinyi duk hakan shikenan kin gama wanka. idan ruwa normal ne wato a bikiti sai ki watsa a jikinki ko'ina ya samu ci cuccuda shikenan ki cigaba da ibadarki.

(2) Yadda ake wankan haila a musulunci a siffar kamala;

1. Bayan kin samu ruwa mai tsarki a bokiti ko mazubin ruwa, sai kiyi niyya

2. Ki karkato bakin bokiti ki zuba ruwa ki wanke hannunki sau uku, sai ki saka hannu cikin mazubin ruwa ki debo ki wanke gabanki

3. Daga nan sai kuma kiyi alwala amma banda wanke kafafu su sai karshen wanka ake yi

4. Sai ki saka hannunki a ruwan ki cire sannan ki mummurza kanki da hannun ko ina da ina haka har sau uku

5. Ki debi ruwa ki game ko'ina a jikinki ko ina da ina yadda ya kamata, daga karshe kuma sai ki koma wanke kafarki ta dama sannan sai ki wanke ta hagu. 

Amfanin wankan haila a musulunci ga mata iyayenmu;

1. samun damar cigaba da ibada 

2. tsafta cikon addini

Post a Comment

0 Comments