Karshen wahala

Karshen wahala part 1

Tafiya take dagwas dagwas tamkar wata sabuwar amarya. Ita kanta tafiyar abin kallo ce musamman ta yanda take naga kafarta tamkar yar gwal, sassarfa take a hakan fa, amma idan ka gani sai kayi tsammani bata son taka kafar ne. Fatima kenan tana tafiya cike a zuciyarta kuwa cewa take gobe dai karshen wahala yazo tunda Abba zai dawo daga tafiyar da yayi. Ace wai ni kullum za'a dinga aike daga inje nan sai in tafi nan kamar wata wacce ba'a so.

Domin a yanzu haka bata ga karshen wahala ba, saboda yanzu ma mama ce ta aike ta siyan goruba. Wai goruba, ace wai kamar ita za'a aika siyan goruba. Da girmanta uhum-uhum sai kace wata yar aiki. Nan Fatima ta cigaba da tafiya ta tunkari kasuwa.

Haba malam shifa kyau abun sone agun kowa sai dai kuma wanda dan baÆ™in ciki ne. Fatima ta kasance irin matan nan ce, masu matukar kyau, tanada dogon tsayi mai jan hankali. Fuskarta mai dan fadi sannan tanada doguwar fuska. Bari dai na rage maka karshen wahala ta karatu, hancinta yana da tsini gashi pointed nose mai kyan kalla. 

Bakinta dan karami coi dashi, fararen idanuwanta kuwa to ko nonon saniya sai haka. idan ko na soma magana akan duga duganta to karshen wahala kenan. Domin tanada faffadan kwankwaso fankacece, wanda saboda fadinsa sai kace tray ne, nonuwanta kuwa ranka shi daÉ—e, ko nunannen mangwaro haka ya gansu saboda farinsu da tsininsu, gashi sunyi cif cif akan kirjinta. 

Karshen wahala
Karshen wahala 1

Yan matasan jam'iyyun nonuwanta sune abin kallo a wajen samari masu son kawo karshen wahala ta burarsu. Amma fa hakan bazai yiwu ba domin Fatima akwai tarbiyya sannan gata yar masu hali dai dai kwarkwado, kowane saurayi na kaunar ace fatima na sonsa, amma yarinyar ba abinda ke hadata da samari illla gaisuwa kawai shina sai wanda ta sani.

Ni sunana Sultan wanda na kasance karamin dan kasuwa mai abun hannunsa kuma gaba daya ilahirin rayuwata ba wacce nake so illla Fatima. Kuma ina sonta ne tun muna sakandare amma har yanzu taki amincewa da soyayya ta.

Bayan da Fatima ta shiga kasuwa da tunanin gobe babanta ze dawo domin ta kawo karshen wahala ta aike, sai akayi sa'a domin nima naje kasuwa domin siyan abu, can ina cikin cinikayya kawai kamar ance kallo nan, ina juyawa na hango, a lokacin naga wani Æ™ara kyau sosai yarinyar tamkar an tsamota daga ruwan kyau. Domin kuwa har wani gizo idona keyi domin kallon ta. Domin kawo karshen wahala shine sai kawai na yanke ciniki na nufi inda take. 

Karshen wahala part 2

Da zuwana nayi mata sallama, ta amsa sallama gamida juyowa domin taga me yin hakan, cikin mamaki naga ta kuramin ido tace Aliyu! Na'am Fatima, ya kike , tayi murmushi sannan tace lafiya kalau kaifa, nace ya rayuwa kuma. Fatima ta kara kallona tace yau kusan shekara hudu kenan rabon da ince na ganka. Nima haka Fatima ina fata kina cikin farin ciki? ta girgiza kai alamar eh, amma me kike anan, tayi dariya sannan tace wallahi mamana nazo siyawa goruba, Aliyu yace 0k. Muje na rakaki nayi hakan ne domin na kawo karshen wahala yawonta a kasuwar domin da alama bata san inda ya kamata taje siyan gorubar ba.

Haka muka taka tare tamkar wasu masoya wanda suka shaku da juna, muna tafiya muna hira cikin natsuwa, har muka isa wajen wani dan tsoho mai siyar da goruba, na siya mata nace ta bar kuÉ—inta. Nifa Aliyu abin ya bani mamaki domin gaba daya naga ta canja sosai yarinyar da lokacin da muna makaranta ko kallona bata fiye yi ba, amma yai gashi har mun musayar lamba. Ko dan haka ne dama zata iya faruwa wata kila ma tun lokacin dana nuna mata ina sonta itama ta fara sona amma saboda taurin kai taki amincewa. Amma bansanin mata ba

Fatima ta kara kyau sosai musamman girman da naga ta kara ya matukar tsaya min a kwanya, lokaci guda naji sabon sonta a zuciyata, ta bangaren Fatima itama abin haka domin har ta shiga tana tunanin Aliyu a ranta. 

Karshen wahala
Karshen wahala 2

Cewa take gaskiya Aliyu ya canja da yawa, naga duk ya zama babban mutum, motar da yake hawa kuwa ko abbana sai haka. To me karatu kayi sani cewa sufa mata yan bin nasara ne, ko kadan basasan abu mara amfani ga namiji, idan kanada abu mai tasiri to fa cikin sauki zaka iya shanyo kansu. Dan haka a shawarce wallahi ka nemi kuÉ—i iya iyawarka ko don ka gujewa rainin hankali. To a kawo karshen wahala bari mu cigaba.

Fatima kusan raba dare tayi tana jiran wai Aliyu zai kirata amma ina shiru kake ji kamar shaho yaci shirwa, nan fa ta soma tunanin irin wulakanta Aliyu da ta taÉ“a yi a makaranta lokacin da yace yana sonta, cikin jama'a ta gaggaya masa magana amma duk da haka Aliyu bai daina sonta ba, ita ta sani har suka bar makaranta. 

Yau kuma saboda kirkin daya nuna mata, sai ta soma jin kamar ta soma son Aliyu, a haka har tayi bacci. Washe gari bayan tayi Sallah haka ta duba wayan wai ko ya kirata cikin dare amma ina, ba ko alamar kira.

Karshen wahala last part 

Cikin yan kwanakin nan mahaifinta ya dawo amma gaba daya hankalinta ya karkarta zuwa wani waje, tayi farin ciki da taga babanta amma yanzu ba fatanta karshen wahalar aike ba. Illa iyaka son wahala ma take yanzu, saboda wahalan aiken ita ta kara hadata da mutumin kirki wato Aliyu. Ana neman karshen wahala saiga sabuwar wahala ta danno kai.

Cikin kwanakin da basu wuce uku ba, Fatima duk ta canja idonta duk suka faÉ—a, tun bata gane cewa son Aliyu take ba, har ta fahimta da kanta, amma kuma gashi ba yanda ta iya. Har tambayar kanta take wai su dama maza haka suke? sai su karbi lambar mace kuma suki kira. 

Ta bangaren Aliyu shima yana cikin wata rigima ne, domin iyayensa sun saka shi a gaba akan dole sai ya nemi matar aure yayi tunda ya gama digirinsa, shiyasa gaba daya ya manta da wata Fatima ya shiga harkokin gabansa. Tun dama shi ya riga yasan cewa Fatima bata sonsa shiyasa ko kadan bai sa a ransa ba. Bayan kusan kamar sati guda Aliyu na kwance akan gadonsa ya tuna da cewa kwanakin baya sun hadu da Fatima a kasuwa, har ya karbi lamba. Amma kuma a yanzu haka bai san dame yayi saving lambarta ba, haka ya janyo wayar da sauri ya hau bincike.

Kamar wasa lamba ta bata domin ya rasa inda take, domin baiyi saving ba, kamar yayi kuka haka ya hakura, can kuma sai ya tuna da karamar wayarsa daya saka caji ya tashi da sauri ya nufi gefen gado ai kuwa ya cire da dubawa da ganin lambar. Allah Sarki ashe a karamar wayata ne, kai tsaye ya rangadawa Fatima kira. Kirr kirr ba'a dauka ba, ta kara ringing amma shiru, saura kadan ta katse..

Karshen wahala
Karshen wahala last

Lamarin Fatima yan-mata mai neman karshen wahala ya girmama domin ko abinci bata iya ci yacce ya kamata musamman idan ta tuna irin cin mutuncin data yiwa Aliyu, itama tasan yanzu bata ita yake ba. Tana cikin bayan gida tana wanka da kyar saboda zafin da jikinta ya dauka, yau kusan wuni tayi da zazzaÉ“i a jikinta, karan ruwa ya hana taji karan wayarta, sai can kuma ta jiyo rurin wayar, ai kamar ba mai zazzaÉ“i ba, haka ta fito da gudu zuwa kan wayarta, kyakkyawan jikinta ba ko tawul. 

Ta daga da sauri HALO, taji ance salamu-alaikum cikin wata shakakkiyar murya, hakan yasa bata gane waye ba, nine Aliyu""""" haba kawai Fatima ta hau KUKA hum hum wiyi wiyi fa tamkar wata mahaukaciya. Aliyu hankali ya tashi wayyo Fatima me ya sameki?? tace dan Allah kana ina? yace ina gida, faÉ—a min menene kina son ganina ne tace eh, ai kafin kyaftawa ya fice da gudu waje kamar wani sha tara, mamansa da babansa suna falo bai ma gansu ba, ya hau mota yayi gaba. 

Bai san inda zai je ba, ya ƙara kiranta tace mu hadu a kofar gidanmu tayi masa kwatance. Aliyu da zuwansa ya hango Fatima a tsaye a bakin layi, yarinya fa ta haukace domin ruga tayi da gudu ta rungume Aliyu.

Shi kanshi yayi mamaki dama haka Fatima ke sona, wannan shine karshen wahala ta, haka ya faÉ—a a ransa.  ai cikin kwana uku a kayi biki,  aka kai amarya gidanta. Suna can suna shan soyyaya mara karewa.

Post a Comment

0 Comments