Gyaran nono su tsaya

Gyaran nono su tsaya

Gareku mata. Yau gidan naku ne kamar ko yaushe, ku kunsan cewa muna yinku mata. Tafiyar dole sai daku. A saboda haka muka ga ya dace muzo muku da wannan babbar tsarabar "ta yadda zaku yi gyaran nono su tsaya"

Gyaran nono su tsaya

Gaba ɗaya wannan maudu'in zai yi dubane haɗe da cikakken bayanin da akayi tata aka kuma yi rairaya aka tace sannan aka kawo muku shi. 

Yake ɗiya mace ki gane cewa dole kina buƙatar kula ko gyara fitilun ki na gaba ako da yaushe. Nonuwanki sune fitilun ki na gaba. Idan har kina so mazaje su kula da motarki, su kalli motarki kuma su yaba da kyan motarki harma sukai ga kokarin fara hawa motar taki, to dolene ki riƙa inganta ta. Ki kula da nonuwanki sune fitulinki. Wani namijin nononki kawai zai kalla yaji kan kaciyarsa ya fara motsi. Yaku mata da kunsan yadda maza suke son nonuwanku da kunfi kula da nonuwan naku fiye da yadda kuke yi a yanzu. Kamar dai yacce nake yawan fada nono shine kadararki ta farko akan idon ɗa namiji.

Yake ɗiya mace nonuwanki martabarki ne. Kuma kowace mace da irin tata baiwar nonon, kar kice ko kiyi tunanin ni nonuwana ƙanana ne ko kuma kiyi tunanin ke kinyi aure ai yanzu shayarwa kikeyi ke babu ruwanki da wani gyaran nono, tunani irin wannan ba ƙaramin kuskure bane. Ki riƙa gyara nonon ki saboda mai gida yana da buƙatar hakan. 

Idan ke irin waɗannan matan ne masu ƙananan nonuwa, ko kuma nonuwanki sun fara zubewa amma kina son su koma su cika taf su kuma tsaya a tsaye to ina mai yi miki albishir, goro fari ƙal. Kin samu kanki a dai dai wurin da zaki samu abinda kikeso watau dai right place at the right time inji masu jajayen kunnuwa watau turawan yamma. 

Da farko dai kafin komai dolene ki kiyaye lafiyar nononki musamman a yanayin kwanciya. Kwanciyar rub da ciki ba taki bace indai kina son nonuwanki suyi karko kuma suyi inganci. A iyakar sanina babu macen da zata so nonuwanta su zube su kwanta kamar silifas duk da dai yau da gobe bata barin komai, sannan ko babu komai akwai tsufa. Amma idan ana kiyayewa sai kiga nonon naki ya jima kafin ki daina cin gajiyar wannan kadarar ta nononki a wurin maigida.

Abu na biyu dole ne ki kiyayewa yin ɗaurin ƙirji. Ɗaurin ƙirji shima ba naki bane matuƙar kin ɗaura ɗamarar kula da nononki. 

Idan kina da aure kuma ke mai jego ce nasan zakiyi goyo, to amma a goyon ma akwai irin abubuwan daza ki kiyaye ki kuma kula dasu duk a domin kiyaye lafiya da martarbar nonuwan naki. Ki riƙa sassauta goyon kuma karki riƙa barin goyon nan na tsahon lokaci musamman ma idan babyn naki yayi bacci sai ki sauke goyon ki kwantar dashi. 

Hanyoyin gyaran nono su tsaya sune kamar haka;

-Haɗa shayin kayan marmari

Ki samu kankana, gwanda da abarbarki ki yayyanka su kanana ki zuba a ruwa mai zafi. Idan sukaji ruwan zafin nan zasuyi laushi sai ki shanye. Ki lazumci haɗa shayin kankana, gwanda da abarbar nan domin yana ƙara ni'ima a nonuwa. 

Ki riƙa yin wannan shayin na kayan marmari na tsahon mako ɗaya zaki ga abun mamaki. 

-Man hulba da zuma

Idan kin kasance kina shayarwa ne to sai ki sami man hulba ki riƙa sha cokali biyu, duk lokacin da kika sha man hulbar nan cokali biyu, sai kisha cokalin zuma ɗaya, yin hakan zai hana nonuwanki zubewa bayan kin gama shayarwa. 

-shafa man hulba

Idan kuma nonon naki ya zube ne sai ki samu hulba ki riƙa dafawa, idan ya dahu sai ki tace ki sha sannan kuma ki riƙa kwaɓa wannan dafaffiyar hulbar da kwan salwa ki riƙa shafawa akan nononki. Idan kin shafa sai ki bashi kamar na tsahon mintuna talatin sannan ki wanke. 

Ki juri yin hakan na tsahon sati ɗaya kiga abun mamaki. 

Ga karin wasu hanyoyi domin gyaran nono su tsaya;

Man shafawa na nononki

shima wannan wani haɗine na musamman da akeyi don gyaran nono kuma yanada muhimmanci sosai, yanda akeyi shine za'a samu

garin kuɓewa

da garin sallaja

tumatur

kindirmo

lemun tsami

Zaki fara samu ki matse lemon tsami mai yawa, sannan ki samu tumatir dinnan shima ki matse ruwan ki kuma jajjagashi, ki kawo kindirmonki ki haɗa a ciki, daga nan kuma sai ki zuba garin kuɓewar nan da kuma garin sallaja duk a cikin haɗin. Ki haɗa sosai ki kwaɓasu ki riƙa shafe jikin nononki da wannan haɗin, bayan kamar tsahon awa ɗaya ko mintuna talatin sai ki wanke ki kuma shafe nonon da man riɗi. Kiyi shi na tsahon sati ɗaya, shima zaki ga abun mamaki. 

Ingantaccciyar hanyar da zaki bi wurin gyaran nononki.Wannan haɗin yana ƙarawa mace girman nono kuma sam ba ya faɗuwa.

Koda a ce tana shayarwa ne idan har tana amfani da wannan haɗin sai dai muce san barka.

Farar shinkafa

Garin Alkama

Garin habbatus sauda

Garin Ayaba (Plantain).

Gyada mai malfa (mai zaɓo)

Aya 

Madarar gari.

Zuma

Idan kika samu plantain sai ki ɓare  shi sannan ki yayyanka shi, ki shanya ya bushe, sai ki daka, kar ki manta cewa garin plantain ɗin ake buƙata.  Daga nan kuma sai ki haɗa garin alkama da garin farar shinkafa, sai  ki  kuma haɗa aya da gyadar a markaɗa a tace ruwan. Bayan nan, sai a ɗora kan wuta a zuba garin plantain da alkama da farar shinkafar da kika haɗe a guri ɗaya, sai kuma ku zuba garin madara da zuma, ki dama shi yayi kauri sai ki riƙa sha safe da yamma. 

Ga mai shayarwa wacce take shirin yaye

Idan kina shirin yin yaye ne, to ki sha sati biyu kafin yaye, kuma idan ba kya shayarwa, zaki iya sha, sai ki tanadi rigar nono watau breziya. Brazier mai kyau, wacce zata riƙa tallafawa nononki su tsaya sosai, ki riƙa sakawa.

Kiyi haka na tsawon sati biyu, ni'imarki zata dawo fiye da yadda kike da ita baya.

Idan kuma baki da halin samo duka waɗannan kayayyakin da aka lissafo to kina iya yin kunun alkama ki riƙa sha sau biyu a rana, amma za ki riƙa sa madarar gari, wato kunun alkama da madara ke nan.

Domin kanana ga yadda ake gyaran nono su tsaya kam;

Idan nononki ƙanana ne kina so suyi manya su girma su cika ƙirjinki taf kamar yadda kikeso dai-dai kina iya yin wannan haɗi domin samun cikar nononki

cukwul

garin alkama

aya

nonon saniya

madara

garin hulba.

Ki samu cukwul wanda yawansa zai kai guda uku sai ki samu garin alkama gwangwani ɗaya sai aya itama gwangwani ɗaya sai ki daka su har su zama gari ki tankaɗe ki samu nonon saniya idan kuma ba kyashan nonon saniya ki samu madara ki zuba wannan garin kamar cokali  uku (3) ki dama kina shan kullum sau ɗaya (1) sannan ki lura lokacin da zakiyi wanka ki tafasa ruwa da garin hulba a ciki ki bari yayi sanyi sai ki wanke nonon da shi sannan kiyi wankan.

___________________________

Gyaran nono su tsaya domin yanmata:

Wannan wani hadine da akeyi don gyaran nono musamman ga budurwa, shi wannan haɗin kuma kowace mace indan tana da buƙata zata iya amfani dashi saboda tasirinsa, yanda akeyi shine.

garin waken soya.

garin alkama.

garin zogale.

garin ɓawon lemun zaƙi

kunfan maliya

da zuma

sai kica kuɗasu guri ɗaya sai ki riƙa shafawa a nonon bayan mintuna talatin ko sama da haka sai ki wanke,sannan kuma ki riƙa shan kunun alkama zaki sha mamaki

Gyaran nono domin dawo da martabarsu su tsaya da karin girmansu:.

Ga matar da take son ta dawo da martabar nononta ko girmansa yanda zatayi shine zata samu. 

ganyen sabara mai kyau

da ƴaƴan alkama suma masu kyau

sai ki rinƙa kunu dasu, ko kunun gyaɗa, ko kunun alkama, ko kunun shinkafa, ko kunun gero, ko koko duk dai wanda yasamu sai ki dafashi da wannan haɗin mai albarka.

Post a Comment

0 Comments