Gyaran nono a sati daya

Gyaran nono a sati daya

Gyaran nono a sati daya

Da izinin mai duka yau zamu yi wannan rubutu ne akan hanyoyin da mata ko yan-mata ya kamata suyi amfani domin gyaran nono a sati daya, duk da cewa babu lallai dole sai nonuwanki sun gyaru a cikin mako guda. Amma koda basu dawo yadda kike so ba, hakan zai kara inganta lafiyar nonuwan, kuma kema kanki zaki samu karin kariya daga cututtuka. Matan wannan zamani kama daga yan-mata zuwa matan aure, kai hatta zawarawa ba'a barsu a baya ba wajen gyaran nono domin janyo hankalin mazajensu ko domin samun karin ni'ima. Gaskiya ne mu maza munason ganin mace da tsayayyun nonuwa masu kyau, domin hakan yana matukar burgemu kuma munajin cewa eh lallai munyi dace, kuma dama haka yake wato hajiya duk mace mai cikakkun nonuwa tafi kyan gani na rantse da girman ubangiji. Kuma ko ba'a fada ba, yawancin matan da zaka gansu da cikakkun damatsa tofa suna gyara ne akai-akai watau kirji na cin Naira. A kowace mahanga gyaran nono yanada muhimmanci domin koda biki yi hakan domin maza ba, to zaki yi domin inganta lafiyarki. 

Muhimmancin gyaran nono a sati daya

(1). Zai bayar da damar maganin cutar jejin mama

(2). kariya daga cutar dake kama fatar mama

(3). kara girman nono ya fito fes

(4). cire duk wata karamar guba wacce batai tasiri ba da wurwuri

(5). samun karin lafiya ga gaba daya ilahirin jiki

Me rashin gyaran nono kan iya haifarwa

(1). saurin kamuwa da cuta

(2). kankancewar nonuwa

(3). rashin gyaran nono na kawo damuwa 

(4). kan iya haifar da cutar da zata taba gaba daya ilahirin jiki

(5). jin zafi ko radadi hakanan kina zaune

Hanyoyin da budurwa ko ke uwargida zaki iya bi domin gyaran kirjinki, kuma da yardar ubangiji cikin sati daya gyaran nonon zai kammalu, muna fatan haka. Wannan wani hadi ne na musamman ga matan aure harma da zawarawa suma zasu iya amafani dashi, kuma yan-mata ba'a barku a baya ba, abubuwan da kike bukata domin wannan gyaran nono a sati daya sun hada da;

(1). ana bukatar garin waken suya

(2). garin alkama nikakke

(3). sai kuma garin zogale

(4). lemun zaki za'a samu garin bawonsa

(5). zuma farar saka

Gaba daya wannan abubuwa da muka lissafo a sama, zaki hadasu a waje guda ki cakudesu sai ki dinga shafawa akan nononki duk bayan mintuna talatin (30) ko sama da haka sannan sai ki wanke, dadin dadawa ki dinga shan kunun alkama, yar'uwa zaki sha mamaki cikin makon nan guda. Domin hadi na gyaran nono a sati daya yanada yabo da yawa daga wajen matan za suka yi amfani dashi.

Sannan domin dawo da martabar nono cikin sati daya harma da girmansa, to yanada kyau mace tabi wannan hanya ta biyu ta zamu kawo a kasa domin gyaran nono a sati daya; abubuwan da muke bukata; sune kamar haka.

(1). ganyen sabara

(2). sai kuma yayan alkama masu kyau

wadannan abubuwa guda biyu dana fada a sama zaki yi amfani dasu wajen yin kunu ne walau kunun gyada, kunun shinkafa, ko na alkama ke koma na gero zaki iya zuba su a ciki a nika da sauran kayan hadin, ki dinga amfani dashi kullum koda kamar sau biyu ne a rana. Shima wannan zaiyi gyaran nono a sati daya a mana godiya daga baya.

To shi kuma wannan na manyan mata ne masu ji da kansu dama mazajensu, domin hadi shine mai kara dankon soyayya ga ma'aurata da kara janyo maigida kusa, wato oga zai dinga son kasancewa da ke koda yaushe. a wannan hadi na gyaran nono a sati daya na manyan mata, abinda ake bukata sune kamar haka;

(1). Ya'yan kankana

(2). a samu gyada danya mai kyau

(3). busasshen dabino 

(4). Alkama

(4). sai kuma ya'yan zogale

Suma dai gaba daya za'a hadesu a nike a waje guda, kullum da safe ki dinga shan cokali guda da madara ta ruwa haka zalika da yamma ma haka. Shima idan da bukata mijinki zai iya sha. 

Na kawo da kyar domin na gaji a wannan rubutu nawa na gyaran nono a sati daya.

Post a Comment

0 Comments