Gyaran nono da makilin

Gyaran nono da makilin 

Nono wani bangare ne na jikin mata wanda ke da muhimmanci kwarai da gaske, ko ban fada dama wannan batu haka yake. Wasu daga cikin muhimman abubuwa ko tasirin nonuwa shine shayarwa, wato mata iyaye suna amfani da wannan nonuwa nasu domin shayar da jariransu madarar uwa, karaw mace kyau nonuwa musamman tsayayyu suna matukar karawa mace kyau, da wannan nonuwa mace koda bata da kyau takan iya janyo hankali maza. 

Kai tsaye wannan rubutu nawa nayi shine akan yadda ake gyaran nono da makilin. Da farko dai abinda zaki nema sune kamar haka;

1. makilin (ya danganta da irin wanda kike so)

2. man kadanya

Matakin gyaran nono da makilin;

A hankali zaki dan mammatsa nononki da hannu, domin bawa jijiyoyin nonon damar saki sannan shima kuma nonon ya saki yadda ya kamata, sai ki lakuci man kadanyar ki shafe nonuwanki tas, wato abun nufi ko ina ya samu tun daga sama zuwa kasa, musamman kan nonuwan, sai kuma ki dakko makilin dinki wato bayan gari ya waye ki wanke nonon sosai. 

Gyaran nono da makilin

Wannan shine yadda ya kamata kiyi wannan gyara na kirjinki. Daga nan kuma sai ki cigaba da yin haka duk lokacin da kika lokaci, ke da kanki zaki ga canji, daga nan in yaso sai ki daina. 

Akwai wasu hanyoyi na gyaran nono ga matan aure da zawarawa wanda nazo dashi a cikin wannan rubutu nawa, watau baya ga yadda ake gyaran nono da makilin ga wasu karin hanyoyi kyauta shima ki kara.

Wannan hadi ne na matan aure dama yanmata;

A binciken da masana suka yi, sun tabbatar da cewa nonon mace zai iya kaiwa sama da shekara arba'in bai zube ba, musamman idan ya samu kulawa yadda ake so, shiyasa koda yaushe yanada kyau ki dinga yawan kula da abinki domin cigaban farin cikin masoyinki dama karin lafiyarki gaba daya. Gaskiya sakarci mace tabar nononta ya zube, karshen shirme kuwa shine kina budurwa kibar nononki ya zube. Ke koda ke zawara ce bai kamata kibar kirjinki ya zuba ba, saboda ina tabbatar miki da cewa ba wanda zai kula ki ballema ya aura, dan haka sai a kara kulawa. Yanada kyau saka bireziyya koda yaushe domin tare daraja da kimar nononki su zauna a tsaye wannan shawara ce kyauta.

Meke kawo zubewar nonon mace?

1. rashin saka rigar nono

2. yawan saka a dame wanda basa da breastcup

3. yawan yin daurin kirji ga mace

4. fitar da nononki ra saman wuyan riga

5. Zukar taba sigari

6. rashin ci da sha mai gina jiki

7. tsalle tsalle marasa amfani

8. wanka da ruwan sanyi

Yadda zaki hana nononki zubewa;

1. saka rigar nono size dinki

2. saka kaya masu breastcup

3. ki rage daurin kirji lokacin zaman gida

4. karki kuskura ku soma shan taba sigari

5. ki dinga wanka da ruwan dumi

6. cin abinci mai gina jiki

bayan bin hanyar yadda ake gyaran nono da makilin to ga wata sabuwar hanyar;

wannan hadine wanda mace zata iya yinsa domin nonuwanta su girma wato su kara cikowa. a wannan hadi kina bukatar

1. masara musamman ja

2. shinkafa fara

3. wheat wato alkama

4. sai kuma gero 

5. nonon saniya kindirmo

bayan duk kin samo duk wadannan abubuwa sai ki hade jar masararki, shinkafa da kuma alkama da geron a niko su. Sai ki dinga yin kunu ki hade da kindirmon kina sha.

Domin kuma nonuwa su tsaya bayan kinyi gyaran nono da makilin;

1. Aloe vera gels

2. danyen kwai

3. cucumber

4. vaseline

ga yanda zaki hada, zaki samu aloe vera naki, ki yanke fatar saman ki debi abin cikin, sai kuma ki fasa kwanki shima ki kwashe farin ruwan ciki, banda kwanduwar cikin kwan, sannan kuma sai ki markada cucumber ki tace ruwansa, wannan ruwa dashi zaki hade duka sauran kayan hadin wato aloe vera da wannan farin ruwan kwan. Ki dinga shafawa da daddare kafin kiyi bacci bayan gari ya waye kuma sai ki wanke da ruwan dumi, daga karshe kuma sai kiyi amfani da vaseline ki shafe nonon tas, bayan kamar minti shida kya iya gogewa. 

duka dai a wannan rubutu nawa na gyaran nono da makilin, akwai kuma wani samfurin kunu da zaki iya hadawa ki dinga sha, shi wannan kunu yana bukatar kayan hadi kamar haka,

1. habbatus-sauda

2. hulba

3. shinkafa

4. sai kuma madara

zaki hada wadannan kayan hadi duka a bokitinki akai miki nika, kiyi amfani da ruwan zafi kinayin kunu koda kofi biyu kullum, wayyo zaki sha mamaki bayan kamar sati biyu.

Anan nazo karshen wannan rubutu nawa wanda wata mutuniyar kirki ta bani bayanai. Muna godiya sosai.

Post a Comment

0 Comments