Gyaran fuska da manja

Menene gyaran fuska?

Gyaran fuska shine yin amfani da wasu hanyoyi ko a hada wasu abubuwa domin mayar da fuska tayi fes, tayi kyau wanda hakan yana karawa mace ko namiji kyau sosai musamman idan anbi hanyar data dace. A wannan zamani da muke ciki na yanzu wasu matan suna bin kowace irin hanya domin gyaran wannan fuska da abubuwa marasa kyau, kamar yin bleaching da wasu sinadarai wanda ke dafar da fatar fuskar tayi haske, hakan kuma yana kashe duk kwayoyin halittun fuska masu amfani. Dan haka a kula sosai wajen amfani da wannan creams. 

Gyaran fuska da manja

Menene amfanin gyaran fuska 

1. kashe cututtukan dake kan fatar fuska

2. kara kyau ga fuska

3. karawa fatar fuskan kwari (quality)

4. saurin jan hankalin samari

5. karin kwarjini

6. karawa mace farinjini

7. kawo saurin auruwa

Rashin amfanin gyaran fuska

1. kawo kwarjinin samari; suna so suna tsoro

2. gyaran fuska idan yayi yawa na iya kawo rashin auruwa

3. na iya kawo mace ta raina samari

4. idan yayi yawa na iya kawo kodewar fata

To a yanzu kuma zamu koma kai tsaye akan dalilin da yasa nake wannan rubutu wato yadda ake gyaran fuska da manja. Ayi sani cewa amfani da manja yanada nasa irin amfanin wajen gyaran fuska, sai dai kuma kar a cika amfani dashi da yawa saboda gujewa wata matsalar. 

Gyaran fuska da manja

Akwai hanyoyi masu yawan gaske da ake amfani dasu domin gyaran fuska, daya daga cikin wannan hanyoyi shine amfani da manja wajen gyaran fuska. Ana amfani da manja da hanyoyi da dama domin gyaran fuska, wasu daga cikin hanyoyin sun hada da;

1. Shafa manja a fuska;

da farko zaki samu ruwan dumi mai kyau ki wanke fuskarki, ki tabbatar kin wanke fuskar fes wato kin fitar da duk wani datti dake kan fuskarki.

sai ki samu tsumma mai kyau shima ki goge fuskar bayan ruwa ya tsane kenan.

ki samu manja musamman danye wato wanda ba'a soya shi ba, danyensa, sai ki shafe fuskan tas ko ina da ina, bayan ya dauki kamar minti biyar sannan sai ki goge da tsumma.

hakan na kawo hasken fata ta hanyar fitar da duk wani duhun fata.

sannan na daga yadda ake gyaran fuska da manja zuba manjan a cikin man shafawa, ki cakudesu ki dinga shafawa a fuska duk lokacin da kike so.

manja na iya amfani wajen goge tabon dake kan fuska wanda baiyi zurfi ba, gamida goge tabon kuraje wanda baiyi yawa ba.

Gyaran fuska da manja yana iya yiwuwa idan manja ya samu fuskar mace mai taushi, kuma yana kara cire duk wani kirci kircin dake fuska domin ingantayya da tsarayyar fuska. 

A cigaba da gyaran fuska da manja, dama sauran hanyoyi domin janyo hankalin mijinki ko saurayinki. idan baki dashi idan kina gyaran fuska da manja ko sauran kayan gyara cikin sauki zaki iya janyo hankalin samari. 

Amma abi a hankali da kulawa yayin gyaran fuska kada a dinga yi da yawa domin hakan na iya kawo matsala, kuma a dinga ziyartar likitan fata a lokaci bayan lokaci domin duba fatar dama bayar da shawarwari.

Baya ga gyaran fuska da manja ga wasu abubuwan da za'a iya amfani dasu domin gyaran fuskar;

1. kurkur

2. creams

3. makilin

4. cin abinci mai gina jiki

5. da kuma shan ruwa akai akai

Idan bai duka ya yadda wannan blog namu zai cigaba da kawo muku duk wasu abubuwa da zaku iya amfana dasu domin gyaran jiki, domin cigaban soyayyarku da masoyanku, anan muka kawo karshen wannan rubutu mai taken yadda ake gyaran fuska da manja.

Post a Comment

0 Comments