gyaran fuska da haske

Gyaran fuska da haske article 

A yau mun zo da jawabi na sirrin gyaran jiki komai da komai da kuke da buƙatar sani akan gyaran fuska da haske, yana cikin wannan rubutun, domin haka sai ku garzayo ku karanta sannan ku fahimci wannan rubutu domin gyaran jiki a sauƙaƙe.

gyaran fuska da haske

Hanyoyin gyaran fuska da haske dama jiki gaba daya na mata suna nan da yawa wanda zan lissafo muku su kuma in faɗa muku yadda zakuyi daki daki sannu a hankali idan kun biyoni a cikin wannan rubutun. 

Ina mai jan hankulanku yaku mata daku tabbatar cewar da zarar kun fara gyaran nan acikin wata guda ku fara ganin changes a jikinku idan har babu chanji to gaskiya ku canza zuwa wani, kunsan shi kala kala ne. Idan wannan nau'in gyaran baiyi miki ba sai kiga idan kika chanja an dace. 

Abu na farko da zaku fara magancewa shine sanyi domin shine ke haddasa matsaloli ga lafiyarku harma da aurenku, ga masu auren cikinku kenan.

Shan ruwa domin gyaran fuska da haske:

Idan ana maganar gyaran fuska da haskenta to abu na farko daya kamata yazo tunaninki shine shan ruwa; indai kinason gyaran kyanki dama jiki dazai sa laushin jiki da kyawun fuska to dole ne a fara da maganar ƙara level ɗin shan ruwa da mace zatayi a kullum koda ace kina sha to ya kamata a wannan karon ya ƙaru kamar da cup uku zuwa huɗu a kowacce rana. 

Zai fi kyau ace kina iya shan kofi takwas zuwa goma, cups na ruwa kowacce rana bawai dole sai anci abinci ba a'a koda babu abinda kikaci ma zaki iya kiyi tasha wanda kuma shi ruwan nan anason idan kina da hali kisamu asalin bottle water watau ruwan roba kenan mai tsafta ki ɗinga shansa saiki ajiyeshi carton-carton idan da hali kina sha sosai saboda shi bai sa yawan fitsari hakanan bai sa cuttutuka kinga ga tsafta ga rashin fitsari.

Lallai kina da buƙatar ki zage dantse ki ƙara akan ruwan da kike sha, idan kuma kinga shan ruwa sosai zai ɗinga baki wahala se ki ɗinga markaɗa ƴaƴan itatuwa watau fruits  zallansu da ruwa kar kisa sugar aciki sai ya zamana shine ruwan shanki. Ki samu ki riƙa sha kofi shida zuwa takwas a rana. 

Shima wannan gaskiya zai gyara miki fata sosai idan har kika jiɓanci shansa dayawa kullum kullum amma kar kice zaki riƙa shan lemo irin na kwali ko kwalba ko na roba. Lemo irin waɗannan ba naki bane yake ɗiya mace, ire iren lemunan nan duk kayan cuta ne idan kina amfani dasu kuma to lallai zasu sa kiyi ƙaton tumbi suna kuma janyo matsalar basir, idan mace mai aure ce sai kiga tana ta bada matsala a wurin auratayya to duk irin wannan cimar ce take haddasa matsaloli irin wannan. 

Mace tasa aranta cewa idan zatayi gyaran jikinta, abu na farko shine ta ƙara yawan ruwan shanta ta kuma kiyaye sosai akan irin nau'in lemo da zata riƙa sha. 

Duk wani abu da zaki kai cikinki to ki kiyaye banda duk wani abu da aka ƙara musu sinadarai, ya zamana duk abinda za kici to natural ne abubuwan da zaki ɗinga sha. Sannan dole ki guji sugar domin tabbas shi sugar cuta ne. Sugar ze ɗinga cinki ta ƙasa ne a hankali yana ƙulle miki mara, idan kina da aure, shima lokacin auratayya zaki riƙa shan wahala kina kasa jurewa duk waɗannan matsaloli ne da sugar yake haifar dasu sai a kula. 

Maganin gyaran jiki da haske:

Sai kuma ɓangaren ingantatun magungunan islamic chemist wanda lallai wajibine kiyi amfani dasu domin maganin sanyi da duk wasu ɓoyayyun cututtuka zaki maganinsu cikin sauƙi tare da wankin mara gaba ɗaya, sune kamar haka;

Habbatus-sauda

Hulba

Kanunfari

Kistil hindi

Citta

Tafarnuwa

Habbatu-rashad

Yansun

Zi'itir

Ruman

Tumeric

Za'a siye su a tanada kamar gwangwani ɗaya ko rabin gwangwani sai a haɗe su waje ɗaya a dakasu ko a niƙasu, za'a ɗinga dafa cokali ɗaya babba watau table spoon a kofi ɗaya na ruwa sai asa zuma ko sugar a shanye kullum kamar na wata ɗaya, ina mai tabbatar miki, ke ajikin kima zakiji canji yadda zakiji kin samu lafiya ga ni'ima na ƙara saukar miki nasha-nasha. 

Abinci na gyaran mai gina jiki:

Shi gyara ko wane iri ne indai gyaran gaske ne to daga ciki ake fara yinsa zuwa waje. Misali kamar gida ne kiga wajensa ƙal ƙal abin sha'awa amma daka shiga ciki ba kyan gani to irin wannan gidan sunansa ƙyal ƙyal banza saboda a waje kawai yake da kyau a ciki babu labari. To kamar haka ne yake ɗiya mace indai kinason gyaran fuska da kyau mai ƙarƙo dole ki fara ta ciki. 

Ki riƙa cin abinci da kyau banda wasa da cikinki, karki manta shi gyaran jikin nan kaso tamanin a cikinsa kamar kina inganta lafiyarki ne, ga mata masu aure kuma ku gane wannan ni'imar da kuke nema zata samu ne ɗari bisa ɗari idan akwai ƙoshin lafiya. Saboda haka ki samu balance diet a abincin ki. Kuma kamar yadda na ambata a sama, lallai karki riƙa wasa da abinci. 

Abubuwa masu mahimmacin da ya kamata su zama abincinki: Tuffa, Ɓaure, Inibi suna taimakawa wurin ƙarawa mutum bodily fluids watau ruwan jiki, ita kuwa ni'ima sai da ruwan jiki ake samota saboda haka a kula sosai ayi aiki da wannan. 

Sinadarin gyaran jiki:

A wannan gaɓar akwai abinda mata da yawa har yanzu basu gane ba. Idan mace ta kiyaye yanayin ruwan daza ta riƙa sha a rana ta kuma kiyaye cimarta da shanta kamar yadda akayi bayani a sama, to duk wani abu da zatayi amfani dashi kuma a gaba babu abinda yakai abin nan da ake kira supplements muhimmanci watau food supplements. Sune sinadaran da zasu ke tallafa miki idan kin rasa balance diet kuma sune zasu taimaka miki kiga jikinki ko ina ya ciko yayi ɓul ɓul. Idan kika riƙi supplements masu kyau har a fatar jikinki sai kin gane hakan. Ki gwada ki gani. 

Shafe-shafe domin gyaran fuska da haske:

A wannan gaɓar ma ina kiran hankulanku mata. Da yawa a cikinku suna tunanin idan sunzo gyaran jiki zasu ta mulkawa fatarsu mayuka kala kala ne kuma anan ne matsalar take. Yake ɗiya mace ki sani cewa maintaining asalin kalar fatarki yana da muhimmanci matuƙa gaya. 

Abinda kawai kike buƙata shine mai ko mayuka masu kyau da inganci wanda basa saka bleaching ɗin fata. Shi bleaching ba gyara bane, a maimakon haka ma sai dai ya ɗinga koɗar dake yana rage miki ingancin fatarki. Duk iya kularki a wurin yin bleaching to zakiga wani wurin yafi wani yin fari, wanda a dalilin haka ne zaki ga nan yayi fari can yayi baki, sai kiga fuskarki kamar aljana. Don haka a kiyaye. 

Ki nemi ingantattun mayuka ki riƙe musu wuta kina amfani dasu consistently for greater result. Idan kikai haka kona tsahon wata ɗaya ne zuwa biyu zakiyi mamakin kyan da fatar ki zatayi. Zakiga ko babu fari akwai sheƙi. 

Dilka domin gyaran jiki gaba daya:

Lallai ki jiɓanci yin dilka domin tana kashe kaushin jiki. Zaki samu dilkarki cokali biyu ki jiƙa da ruwan ɗumi idan ta jiƙu ta kumburo sai ki saka mata kwanduwar kwai da peak ta ruwa kota gari, ki matse lemon tsami akai ki bubbugashi sosai zaki iya ƙara madarar turare saboda ki kashe ƙarnin sosai idan suka haɗu suka kwaɓu zaki iya shafe dukkan jikinki dashi ki zauna ya bushe kamar minti talatin amma ni irin wannan zan baki shawara daki zauna a banɗaki kina jiran ki bushe mai zai hana a lokacin ki fara yin gyaran tafin ƙafa da tafin hannu at the same time, a lokaci ɗaya kenan inji bature. Kina bushewa kinga kin samu kinyi abubuwa biyu a lokaci ɗaya kenan.

Idan kika jiɓinci yin dilka kowacce rana acikin wata biyu zuwa uku keda kanki zaki fara sha'awar yanda jikinki zaiyi taushi sosai hakanan saboda samun glowing skin ma zaki iya adding man riɗi a cikin haɗin dilka ɗin sai dai kirage yawo da zirga zirga.

Samun hutu domin gyaran jiki:

Lallai ne ki riƙa bawa kanki hutu. Anan ina nufin ishasshen hutu kimaida kanki cikin isasshen hutu. Idan baki sani ba yau zan faɗa miki yake ɗiya mace, kinsan cewa shi hutu mai kyau kaɗai yana chanja fata kuwa? kamar yadda yawan stress yake yankwanar da ita. yawan stress ko wasu abubuwan na daban, abinda yafi dacewa shine kibawa kanki hutu na musamman domin a wannan lokacin ne duk wani gyare gyare da kikeyi zai fi zama ajikinki yayi miki aiki sosai, saboda haka ko kayan shafe shafe ne yafi aiki alokacin da kike bacci, bayan baccin da kikeyi na dare a nason kowacce rana ki ɗinga ƙara wani baccin na musamman kamar da rana haka. 

Gyaran jiki da kamshi:

Yawanci wasu matan sun ɗauka wai shi ƙamshi se anzo biki daf ake sabawa dashi nan kuwa shima kamata yayi ki riƙa amfani dasu humra da sauran turaruka masu kyau da sassanyan ƙamshi na mata. Wanda zai saba da jikinki irin wannan za kiga koda kinyi kwana ɗaya bakiyi ba kina ƙamshi hatta kayan jikinki zai fara ƙamshi duk dattinsa. 

Post a Comment

0 Comments