Mallaka da tumfafiya
A magana ta gaskiya babu wata sahihiyar hanya wacce ake amfani da tumfafiya domin mallakar wanda ake so ko kuma wacce ake so, wato kunga kenan duk wasu maganganu da zasu zo akan mallaka da tumfafiya zai iya kasancewa aiki ne wanda ake yi da sihiri ko kuma wani asiri, wanda idan ba'a yi wasa ba zata iya kama wata hanya marar kyau, wato a iya yin shirka, sai dai kuma wasu abubuwan wanda muma binkicen mu be kai nan ba, amma dai iya bincikenmu akan wannan maudu'i na mallaka da tumfafiya babu wani ko wata hanya wacce zatayi amfani domin mallakar, dan haka sai ayi aiki da hankali yayin amfani da duk wata hanya wacce aka samu daga wata kafa, nagode.
Tumfafiya wata bishiya ce ko wani tsiro wanda ke fitowa a jeji ko yankin arewacin najeriya, wacce ke fitar da wani farin ruwa mai diga tamkar yadda jini ke fita jikin mutum, sai dai shi wannan ruwa fari ne. Wasu hausawan ma suna alakanta tumfafiya da mutanen boye amma duka dai soki burutsu ne, ba wani tabbaci akwai zaman mutanen boye. kunga kenan idan da tabbacin akwai mutanen boye a jikinta tofa yin mallaka da tumfafiya sai iya zama da sihiri.
Tumfafiya nada muhimmanci da yawa haka zalika amfani, a wannan rubutu zan kawo wasu daga ciki; misali
1. domin kara ruwan maniyyi
2. don maganin mayu
3. don maganin lalata duk wani sihiri
4. don kara ni'ima
5. domin farin jini
To wannan abubuwa na sama sune amfanin da bincikenmu ya samo na amfanin tumfafiya; yanzu kuma zamu yi bayanin kowane daya a cikinsu.
1. domin kara ruwan maniyyi; a samu furen tumfafiyar a shanya ya bushe, sannan a daka shi da turmi, asa rariya a tankade. a samu madara ko nono a dinga zuba cokali daya ana sha kamar sau biyu a rana. za'a samu karin ruwan ni'ma a jiki.
2. Domin yin maganin mayu; za'a samu danyen furen tumfafiya guda bakwai a rika taunawa ana cinyewa har na tsawon kwana bakwai, za'a samu waraka daga mayu idan mai duka yaso.
3. Domin lalata sihiri; a wannan bangare kuma za'a samu furen tumfafiya da sassaken tsamiya gamida sassaken gamji a daka a tankade a rika shan cokali daya a ruwa, sannan ayi amfani da cokali daya a ruwan wanka, a haka har tsawon kwana bakwai.
4. Domin karin ni'ima; shima a samu furenta da sassaken marke da kaji-ji da kanumfari da kimba gamida masoro da citta gaba daya a hada a dake, a tankade, a rika shan cokali daya a madara ko nono ko kuma a ruwa koda sau biyu ne a rana.
5. Domin farin jini; ganyen gamji da tumfafiya a daka a tankade a rinka shan cokali daya a cikin nono sau biyu a rana har izuwa kwana bakwai.
0 Comments