Coca cola na zubar da ciki

Coca cola na zubar da ciki?

Tofa aka ce aiki ga mai kareka, da safiyar yau din nan muna zaune a ofis dinmu domin gudanar da ayyukan yau, saiga wata saukar wani sako a email dinmu na wannan shafi, wata budurwa ce kuma ta turo sakon. Wannan budurwa ta bukaci mu sakaya sunanta kuma tambayarta shine wai coca cola yana zubar da ciki. Mu kuma mun dauri aniyar yin rubutu akan hakan domin mai karatu ya amfana dama duniya gaba daya. 

Coca cola na zubar da ciki

Menene ciki ?

Tom juna biyu dai kamar yadda kowa ya sani shine ciki, wato samuwar halittar jariri ko jaririya a cikin mahaifiya, wannan jariri zai iya zama wanda ake bukatarsa ko kuma wanda ba'a bukata. Sau da dama wanda ake bukata shine wanda aka haifa ta hanyar aure wanda kuma aka haifa ta hanyar daba aure ba, wato ta hanyar banza akan titi wannan ba'a bukatarsa kawai zuwa yayi. Yanada kyau koda yaushe idan ka yiwa wata ciki ta hanyar banza to kaji tsoron Allah kar a zubar da wannan ciki, saboda ka ragewa kanka azabar ubangiji. Shawara ce ya rage ruwanka ko nace ya rage naki kuma. Kuma dama banzo nan domin wa'azi ba, nazo amsa tambayar shin coca cola yana zubar da ciki. Amma idan da bukatar dole sai an zubar da cikin to a iya amfani da wasu hanyoyin domin yin hakan kamar bin hanyoyin gargajiya, hanyoyin zamani ko kuma wanda za'a iya bi domin yin hakan.  

Menene coca cola ?

coca cola dai wani samfurin abin sha ne na cola wanda kamfanin coca cola suke samarwa domin mashaya. Babu wata kafa sahihiya wacce ta tabbatar da cewa coca cola yana zubar da ciki ga mai ciki, ina tabbatar da cewa duk wanda ya gaya miki cewa coca cola zai iya amfani wajen zubar da abinda ke cikinki wanda bakya bukata tofa ta dankara miki babbar karya. Kinsan dalilin da yasa nake gaya miki haka? toga dalili, a gaba daya ilahirin kayan hadin da akayi amfani dasu wajen hada coca cola babu wani abu da yake illatar da mahaifar mace ballema har a samu barin ciki. Yana da kyau na lissafo abubuwan da akayi amfani dasu wajen hada lemon coke na coca cola;

(1). akwai water wanda ya kasance carbonated, wato ruwa mai tsafta wanda aka saka masa sinadarin carbon domin fitar da kwayar cututtuka

(2). akwai sinadarin fructose wanda ya kasance suga ne

(3) sai kuma kalar caramel wacce ke bashi kalar baki

(4). sai sinadarin phospheric acid wanda keda amfani wajen markaden abinci a ciki 

(5). sai wani abu da muke cewa dan_zaki da hausa wanda shima kamar suga haka

(6). sinadarin caffeine wanda keda tasiri wajen rage bacci

(7). sai wani sinadi wanda ake iya samunsa a lemon tsami da kuma citric acid 

Muhimmancin shan coca cola 

(1). samar da kuzari da rage kasala

(2). samar da dadi a bakin mai sha 

(3). samar da kaifin kwanya da rage yawan bacci

(4). mukan iya samun coca cola a ko ina a fadin wannan duniya ba tareda wata wahala ba

Rashin muhimmancin coca cola 

(1). akwai yiwuwar samun kiba idan ana yawan shan coca cola

(2). kuma za'a iya samun lalacewar hakori saboda acid din dake cikinsa 

(3). matsalar sabo da sha wato zaka iya zama idan baka sha ba baka jindadi

(4). har izuwa yanzu a bincike na banga matsalar coca cola yana zubar da ciki ba, sai ma ka iya jawo kuzari ga jaririn

(5). shan sa na iya kawo kishin ruwa da wurwuri.

Maganar gaskiya dai, yan magana suka ce a fadeta to a gaskiya iya bincike munyi babu wata hujja dake tabbatar da cewa coca cola yana zubar da ciki. Sai dai kawai labarin kanzon kurege wanda ake yadawa a kafafen sada zumunta na facebook dama wasu marubuta a yanar gizo keyi wanda ba gaskiya bane. Wata kila an basu kwangila ne na bata sunan coca cola ko kuma son zuciyarsu. Muna kallonki kinje wani ya dankara miki ciki ya cuceki ya cutar da iyayenki shi kuma ba ruwansa yana can yana harkokin gabansa. Ina rantsuwa da girman ubangiji duk yarinyar daka lalata ubangiji ba zai barka ba. ke kuma koda yaushe ki manta da wata sha'awa ta son zuciya ki kame mutuncin kanki. Anan nazo karshen wannan rubutu na amsa tambayar coca cola yana zubar da ciki. wacce itace A'A saboda hujjoji da bincike ya tabbatar.

Post a Comment

0 Comments