Yadda ake soyayya

Yadda ake soyayya article

Soyayya halitta ce da take da matuƙar tasiri a rayuwar ɗan adam, jinsin namiji da mace baki ɗayansu.

Idan kuka duba za kuga akwai abin ban mamaki matuƙa gaya, ta yadda masoya ke ƙulluwa da junansu. Za kuga idan basu ga juna ba ko kuma idan basu ji muryar juna ba sai kuga sun kasa samun nutsuwa sun shiga wani hali na daban. 

Wannan irin shaƙuwar ta musamman ce, wacce a farko kafin a ginata ta ginu zaku ga kamar ba zata kai gaci ba, amma a yayin da zuciyoyin mutum biyu suka taru suka haɗe waje guda, watau zuciyar masoya kenan, sai kuga sun shiga kuma sunyi nisa a cikin so da mayen begen junan su ba don komai ba, sai domin giyar soyayya da suka sha ruwanta suka kwankwaɗa. 

Wannan rubutun da zanyi, a cikinsa idan kuna tare dani, zan zayyano muku hanyoyin yadda zaku shimfiɗa soyayya mai daɗi, haka kuma mai tsayawa a cikin zuciyoyin masoyan juna ta yadda idan masoyan sukayi nisa da juna kewar ɗayansu zai dami zuciyar masoyi ko masoyiya su shiga mararin abin ƙaunar zuciyarsu. 

Hanyoyin sauke nauyin masoya akan junansu. Na yadda ake soyayya.

-Ka/ki riƙa bata/bashi labarai masu daɗi da tsuma zuciya musamman ma labaran da suka shafi soyayya. 

Ta wannan hanyar ne idan masoya watau lovers, suka sakankance da bawa junansu labaran soyayya masu daɗi za kuga a hankali, haka kuma a aikace waɗannan masoyan ba tare da sun farga ba, zasu riƙa bi da junansu ta hanyoyin da suke bawa junansu na irin labaran soyayyar da suke jiyar da junan nasu ba, ba domin komai ba kuwa sai don farantawa ran juna haɗe da burge zuciyar junan nasu. Saboda me ? Saboda haka labaran soyayyar da suke baiwa junansu a cikin hirarrakin su ta koyar dasu. 

-Duk lokacin da kuka haɗa ido ka/ki sakar mata/masa tattausan murmushin love na musamman. 

Kallo da kuke gani a cikin love watau soyayya wani rukuni ne ko ginshiƙi mai zaman kansa a cikin ta. Kallo a soyayya farilla ne akan masoyan juna. Dole ne zuciyar masoyi taso idanunsa suke hasko masa abar begensa, haka kuma itama zuciyarta zata riƙa son idanunta su riƙa kallon masoyinta. Idan kuna jifan junanku da kallon soyayya to zaku riƙa samun kanku cikin shauƙi da farin ciki a lokacin da kuke tare. 

-Ƙannenta su zama abokanka, kake kyautata musu fiye da zatonsu ta yadda zasu damu kowa da zancenka a gidansu. 

Kamar yadda aka san mace da kunya da aji to ka sani ya kai namiji, mata da yawa yawansu ba zasu riƙa maganar saurayinsu a cikin ahalin gidansu ba saboda kunya, shine yasa yawancin hirar da ƴanmata zasu ke yi akan samarinsu, zasu iya yinta ne kawai da ƙawaye ko abokanan wasa da aka taso tare. Idan ka kasance kana mai jan ƙannenta ko wasu nata a cikin makusanta, musamman ma dai ƙanne idan tana dasu, to waɗannan ƙannen nata zasu riƙa maganar ka a cikin gidansu masoyiyar ka 24/7, kuma hakan ba ƙaramin taɓa mata zuciyarta zai yi ba, kuma zai ƙarawa soyayarka ƙarfi da tasiri a zuciyarta. 

-Ka riƙa girmama iyayenta da ƴan gidansu. 

Duk wani mutum mai hankali a duniya idan ka kasance kana girmama iyayensa ai kuwa ina ganin wannan mutumin ya isa shima ka girmama shi, musamman ma kuma ace wannan mutumin masoyi ne ko masoyiya. Idan kuna girmama iyayen junanku yaku masoya, to ku sani hakan zai shafi albarkar soyayyarku wannan ko shakka babu. Ku lazimci girmamawa da kuma kyautatawa iyayen junanku yaku masoya, domin tatso albarkar soyayyarku. 

-Ka/ki riƙa yaba mata/masa koda batayi/baiyi abin yabon ba.

Misali in kunyi kiciɓus kace gaskiya kin haɗu, nutsuwarki tana birgeni, gaskiya duk wanda ya aure ki yayi sa'ar mace ta gari. Kema daga naki ɓangaren kike yaba masa kina mai nuna jin daɗinki akan duk wata kyautatawa daga masoyin zuciyarki. 

-Ka riƙa mutunta ta banda janta da musu amma kake sawo labarai na nishaɗi. 

Ya kai masoyi ka sani yadda kabi da masoyiyarka to fa haka zaka same ta acan gaba yayin da soyayyarku tayi nisa a cikin zukatan ku. Idan kana mutuntata dole ne itama zata mutuntaka saboda ka mutunta kanka ta hanyar mutunta ta da kayi. Remember, respect is reciprocal. Haka bature mai jajayen kunnuwa yace. 

Yadda ake soyayya
Yadda ake soyayya pic#

-Ka/ki yawaita kwalliya musamman duk sanda kasan/kika san zaku iya haɗuwa da ita/shi ko ƙawayenta/abokansa, domin mata/maza sun fi son ɗan gaye/ ƴar gayu. 

Idan kuna yiwa junanku kwalliya za kuke burge junanku, haka kuma zaku ke mararin haɗuwa da junan ku. Haka nan abokanka da ƙawayenta za suke kyankyasa muku irin kyan da suka ga ɗayan ku yayi. Kwalliya a soyayya itama farilla ce domin kuwa zata so saurayinta ya same ta fes fes a lokacin da yazo zance, kuma haka nan shima zai zo ne yana mai baza ƙamshi ya karkato hularsa ƙasan goshi duk domin burgewa. 

-Ka/ki riƙa tanadar kalmomi na musamman domin ita/shi. 

Au! Wai kuna nufin harma sai na faɗa muku irin tanadin kalaman soyayyar da zaku yi saboda junanku ku? Idan kuwa haka ne to lallai da sake, domin kuwa idan namiji ya faɗa kogin son wata baby ai baisan lokacin da zuciyarsa zata riƙa tsara masa zance mai kyau a kanta ba, a yayin da kwakwalwarsa zata shiga aikin tace wannan zancen na soyayya bakinsa kuma yana aikin furtawa. Idan har kana soyyaya ta gaskiya da ƴar babynka amma baka kai ga wannan matakin ba, to gaskiya soyayarka akwai saura. 

-Ka zama mayen saka turare koda yaushe zata riƙa son zama tare da jimawa da kai. 

Ƙamshi ma wani rukuni ne da masoya zasu tafi akan turbarsa har ya kaisu da cigaba da tafiya a haka yayin da suke amsa sunan ma'aurata. Ku karɓi ƙamshi kuyi aiki dashi domin shi ɗin abokin tafiya ne, haƙiƙa zaisa kuke mararin junan ku kuna jin daɗin kasancewa da juna. Idan taji ƙamshin turarenka mai daɗi da hancinta ya saba shaƙo mata idan kuna tare ai ba saina fadɗa maka outcome ɗin hakan ba ko? Abokina nasan kasan sauran. 

-Ka guji hantararta da kushe ta ko da wasa. Haka, ka guji zaginta da yi mata ƙarya, ko kula ƴanmata a gabanta. 

A soyayya babu ɗaga murya bare har akai ga hantara, ba'a kushe masoyi sai dai lallaɓa shi da faranta masa, haka kuma ba'a zagin masoyi sai dai a tsara masa kalamai masu tsada. Soyayyar da ake ƙarya kuwa a cikinta dama sunanta nakashasshiyar soyayya, ku riƙe wannan. 

-Ka riƙa sirkawa da kyauta koda ba zata karɓa ba ka riƙa mata. 

Kyauta farilla ce itama a cikin farillan soyayya, ba kwa buƙatar wani ƙarin bayani anan.

-Kar ka kuskura ka riƙa yi mata hirar kai ƴanmata da yawa na son ka, koda wasa. 

Chaɓ! Da sake, ba zata saɓu ba, wai bindiga a ruwa. Idan kana yi mata irin wannan zancen to ka tabbatarwa kanka cewa kana yiwa kanka foul ne, kuma tabbas hakan sai ya jawo maka fanareti!.. 

Wannan a dunƙule shine yadda soyayya take sa ran zaku bita ku shimfiɗa ta domin sauke haƙƙoƙin ita soyayyar dake kanku. 

Na barku lafiya.

Yadda ake soyayya post#

Post a Comment

0 Comments