Yadda ake hirar soyayya

Yadda ake hirar soyayya

Kafin nakai ga shiga cikin asalin topic ɗin nan watau yadda ake hirar soyayya zan so nayi waiwaye domin shi waiwaye inji masu iya magana suka ce; adon tafiya ne. Zan waiwayo baya domin na fara lissafo hanyoyin hirar soyayyar kanta, wanda hakan ne zai bawa mai karatu damar fahimta da kuma gane wace hanyar ce tafi dacewa da shi ko kuma tafi masa sauƙi domin jin daɗin zuma da madarar soyayya. 

Hanyoyin na yadda ake hirar soyayya 

-Zance ko taɗi tsakanin masoya saurayi da budurwa 

-Hira a waya 

-Hira ta rubutu ko murya watau abin nufi chat ko voice notes kamar yadda bature ya zaɓi ya faɗa. 

Waɗannan kwararan hanyoyin guda uku dana lissafowa mai karatu zaiyi wuya ace ya fita daga cikin su ta fannin hirar soyayyarsa. Idan kuna tare dani makaranta, zan ɗauki ko wace hanya ɗaya bayan ɗaya na faɗaɗa ta na kuma yi bayani dalla dalla haɗe da sanin tasirin kowace kwaya ɗaya daga cikinsu. 

-Zance ko taɗi tsakanin masoya saurayi da budurwa 

Hira tsakanin masoya, zance ko taɗi itace hanyar farko da aka sani a al'adance. Ta wannan hanyar ce saurayi da budurwa za sufi samun damar nazartar masoyi/masoyiya.

A wannan zamanin da muke ciki har yanzu wannan hanya ba'a yada ita ba, haka kuma tana taka rawar gani har yanzu a tsakanin masoyan juna. Kamar yadda na faɗa a wannan zamanin, wannan hanyar dai tana amfani ga masoya kuma ma irin wannan hirar tana iya farawa tun daga yammaci har zuwa dare. 

Saurayi zai iya zuwa gun budurwarsa a lokacin yammaci haka kuma zai iya fita da iya wani wurin shaƙatawa kamar garden ko wurin cin abinci, su zauna su zanta duk domin ƙara danƙon soyayyarsu. Haka kuma saurayi zai iya zuwa zance wurin budurwarsa da dare, nan ma su samu su zanta su ƙara samun danshin soyayya. 

-Hira a waya 

Yin magana ko soyayya da yarinya a waya, wasu suna ɗaukarsa abu mai wahala ko tsoratarwa. Wanda kuma hakan bai kamata ba ace masoya suna jinsa.

Yawancin samari sun yi imanin cewa hanyar da tafi sauƙi gurin yin hirar soyayya da mace shine a waya, kamar yadda matan suma suka yarda da wannan hanyar. Saboda irin hakane ta hirar soyayya a waya koda zance ya wuce sai kaji budurwa tana tambayar saurayi me kake tunani?

Kamar wani batu da kuka fara, idan ba kace komai ba, ta yarda cewa kana ɓoye wani abu. Ku sani wannan hanyar haɗi mai karfi ne domin gina dangantaka mai zurfi da ma’ana ba matsala bace.

Amma, ga mutumin da ya sami wahalar magana game da tunaninsa da yadda yake jin yarinya ko ince mata, wannan hanyar gina dangantaka ce mai zurfi da ma’ana kuma tana iya maida mafarkin ka gaske!

Tabbas ya kamata duk wani saurayi ko budurwa su san yadda ake hirar soyayya a waya, domin kuwa hakan yana da amfani. Saboda ta hakane koda tanajin kunyarka idan kuna zaune, to idan kuna ta waya ka kirata zaka ga hirar tafi yawa, sannan itama za tafi sakin jiki kuma da bayyana soyayyar ta a gareka, sannan haka wurin furta kalaman soyayya zata samu sauƙi.

-Hira ta rubutu ko murya watau abin nufi chat ko voice notes. 

Wannan ma wata hanya ce ta hira a soyayya wadda zamani yake tafiya da ita. A cikinta akwai sakin jiki ayi hira haka kuma ayi nishaɗi daga duka ɓangarori biyu na masoyan. Hanya ce kuma wadda idan masoyi ko masoyiya na cikin kewar junansu ta kan taimaka musu domin shi chat ko voice note akwai su a memory da za'a iya komawa a ziyarcesu domin karantawa ko kuma saurarawa aji. Wannan kenan! 

Yadda Ake Hirar Soyayya #

Yanzu na ƙaraso kan zancen; watau yadda hirar soyayya take ko kuma nace yadda ake hirar soyayya. Kai tsaye zan shiga bayani akan irin abubuwan da ingantacciyar hirar soyayya ta ƙunsa. 

Idan kana zuwa zance, dake kuma da ake zuwa zance wurin ki, ai nasan kunsan abinda yake tara ku ko ? Nasan kasan me kaje yi, kuma nasan kin san me aka zo yi wurinki ko nace gidanku ? To ku biyo ni a sannu. 

A hirar soyayya;

-A kullum akaje zance kai namiji ka tanadi kalamai masu kyau masu aminci da zasu ke nunawa babynka ko nace budurwarka, tafi ko wace mace kyau a wurin ka. Ko kuma duk lokacin da kuka yi waya ko kuna tare ka riƙa ƙoƙarin nuna mata komai nata daban ne dana sauran mata. Kasa ta riƙa ji ita ɗin gimbiya ce. 

-Budurwa daga naki ɓangaren ko ban faɗa miki ba, nasan you'll cherish all those moments, domin haka ne za kike son kasancewa tare da wannan masoyin naki, after all you can't help it. Can you? Ita zuciya dama, tana son mai kyautata mata. A haka aka halicce ta. To ke kuma zuciyar taki tana tare da saurayinki kuma shi saurayin naki yana kyautata miki, yaya kenan? 

-Ka nuna mata yadda muryarta tafi muryar duk wata mace daɗi, idan kuna tare wasu lokutan har da ƙarya ƙarya ka riƙa haɗa mata kamar irin; "baby idan har fa banji muryarki ba, bana iya yin barci, kuma bana iya cin abinci, kaga irin haka zai sa take jinta tamkar sarauniya, wannan ɗin ba yaudara bace ba. Sam! Kasa a ranka kai ɗin kana ƙoƙarin farantawa abar ƙaunarka ne, haka kuma turawa masu iya magana suna cewa; "everything is fair between love and war".. Ka gane. 

-Ita soyayya dole sai da kyauta, duk abinda zai farantawa masoyi shi akeyi a soyayya, ita kuwa kyauta tana sanya zuciya farin ciki. Ka riƙa samu kana mata kyaututtuka ko da kuwa tafi ƙarfin wannan abin da zaka bata. Note; za taji daɗi. 

Yadda ake hirar soyayya
Yadda ake hirar soyayya post#

Tsada ko girman kyautar da zaka bata bashi ne zaisa taji daɗi ba, kayi mata kyauta mai sawa taji irin muhimmancinta a zuciyar ka. Turaruka da kayan kwalliya da irin katunan nan masu ɗauke da kalaman soyayya duk misalai ne na irin waɗannan kyaututtukan. 

-Kada ka zurfafa kishi, idan kana so mace ta soka, watau kada ka zama mai nuna kishi da yawa. Mata basa son maza masu tsananin kishi. Kuma kada ka zaƙe wurin takura mata akan abubuwan da basu kai a damu dasu ba. 

-Haƙuri da kau da kai daga laifin da tayi maka, musamman idan kuna hira yana ƙara sa mace taji matuƙar son ka, da kunyarka haɗe da kwarjini a idanuwanta. A irin haka koda ita ma an kawo mata gulmarka daga ƴan gutsiri tsoma to itama ba zata riƙa saurararsu ba. 

A dunƙule duka waɗannan bayanan, suna nuna muku ne cewar; ita hirar soyayya a sauƙaƙe watau in simple terms ana yinta ne dan jin daɗin masoya. 

Yadda ake hirar soyayya post#

Post a Comment

0 Comments