Yadda ake gane cikin tagwaye

Yadda ake gane cikin tagwaye ko yan biyu

Yan magana suka ce da zuwa a makara gwanda zuwa a makare wannan haka yake, domin kowa na son lafiyarsa da cigaban rayuwarsa. A yau idan ubangijin Musa da Haruna ya nufa zamu yi bayani dalla dalla gwargwadon iko akan yadda ake gane cikin yan biyu har ma da wasu maÆ™aloli masu dangantaka da hakan.
Yadda ake gane cikin tagwaye

Menene cikin Tagwaye:

Cikin tagwaye yana nufin uwa tana dauke da juna biyu wanda take dauke da jarirai guda biyu a mahaifarta. Hakan kuwa na iya samuwa ne ta hanyoyi da dama kamar tushen ahali da kuma waÉ—ansu hanyoyi da ake iya amfani dasu na kimiyya da fasahar zamani. Likitoci sune kaÉ—ai sukan iya gane cikin tagwaye a cikin mahaifa ta amfani da fasahar zamani me suna ultrasound. Cikin tagwaye yana samuwa kawai idan akwai wasu tsokoki guda biyu a cikin mahaifa wanda muke cewa fetuses a turance kuma suna zaunuwa ne a cikin kwarmin zaman halitar jarirai mai suna uterus.

Damar samun cikin tagwaye:

Wannan katafariyar dama tana samuwa kawai cikin sa'a da taimakawar ubangiji. Bincike ya tabbatar da cewa a cikin mata É—ari biyu da hamsin masu juna biyu mace É—aya ce kaÉ—ai keda wannan sa'a. 

Alamomin yadda ake gane cikin tagwaye:

Alamomi na yadda muke iya gane cikin tagwaye a cikin mahaifiya sun haÉ—a da.

1. Motsawar ciki da wurwuri bayan yan satuttuka da samun juna biyu.

2. Samun wannan motsi a wurare daban daban a cikin mahaifiya.

3. Samun nauyin jiki da wurwuri.

4. Yawan samun tashin zuciya ba gaira ba dalili.

5. Mai ciki takan iya fuskantar bugun zuciya guda biyu a tareda abubuwan dake cikinta.

6. Yawan neman kayan kwaÉ—ai da yan lashe lashe.

Alamomin cikin tagwaye bayan wata biyu:

1. Jin zafi ko ciwon mama ga uwa: Mahaifiya mai É—auke da juna biyun tagwaye ka iya fuskantar ciwo a mamanta sakamakon wasu ayyukan sinadarai dake faruwa a jikinta.

2. Gajiya: Yawan samun gajiya ga mai juna biyu na É—aya daga yadda ake gane cikin tagwaye a tareda mace.

3. Yawaita fitsari: Yawan ziyartan ban-É—aki a tareda mai ciki domin yin fitsari yana daga cikin alamu na yadda ake gane cikin tagwaye.

4. Neman abinci akai akai: Yawan cin abinci da saurin jin yunwa ka iya bayuwa ga alamomin cikin tagwaye a tattare da mahaifiya.

5. Samun rashin lafiya da safiya: Samun yawan zazzaɓi da ciwon kai da dai sauran rashin lafiya ga mai ciki da safe bincike ya nuna cewa mukan iya samun dacewar samun juna biyu na tagwaye.

Taya zamu tabbatar da cikin tagwaye:

Hanya guda É—aya ta fasaha wacce ake amfani da ita wajen tabbatar da cikin tagwaye wato Ultrasound. Amma gaskiya babu wata sahihiyar hanya ta gargajiya da zamu ce ana amfani da ita na yadda ake gane cikin tagwaye, illa iyaka dai wasu alamomi kawai.

Ire iren tagwaye:

A binciken kimiyya da ilimin likitanci muna da ire iren tagwaye guda biyu, sune kamar haka:

1. Fraternal twins

2. Identical twins

1. Fraternal twins: tagwaye ne wanda suke samuwa ba'a tunÆ™ule ba kuma basa kama da juna kamar an tsaga kara, wato zaka iya ganin tagwaye a garinku wanda ko kaÉ—an basa kama da juna, wasu idan ka gansu saika rantse da Allah ko uwa basu haÉ—a ba.

2. Identical twins: Kuma koda ba'a faÉ—a make to kana ganinsu zaka gansu tamkar an tsaga kara, kamar su daya sak komai nasu iri É—aya, yadda suke tafiya, yanda suke magana da dai sauran halayen mutane.

Yadda zaki samu cikin tagwaye:

Al'amari na gaskiya shine ayi sani cewa babu wata hanya kai tsaye wadda za'a ce za'a bita domin dacewa da samun juna biyu na tagwaye, amma akwai wasu dalilai da ka iya kawo hakan.

1. Matan da suka haura shekara talatin da haihuwa sunfi kowa samun sa'ar cikin tagwaye. 

2. Gado daga ahali: Idan daga tarihin danginki kuna yawan samun haihuwar tagwaye to tabbas kema kinada wannan gado a jikinki amma duk da haka babu wani tabbas na cewa dole saikin samu. Komai na daga Allah saiki dage da yin addu'a.

3. Mata masu nauyin jiki ko muce ƙiba sunada damar samun cikin tagwaye sakamakon wasu bincike na kimiyya, musamman wanda suka haura shekara talatin da aihuwa. Kamar talatin da ɗoriya.

4. Idan kin taɓa aihuwar tagwaye to yana faruwa ki ƙara samun wasu cikin tagwaye domin hakan yana daga ma'auni na yadda ake gane cikin tagwaye koda kuwa bakya ɗauke da cikin a wannan lokaci.

Yadda ake gane cikin tagwaye

A wannan rubutu nawa ban tsaya kawai ga yadda ake gane cikin tagwaye ba a'a ta taɓa wasu hanyoyi da za'a iya samun cikin tagwaye a kimiyyar zamani ta amfani da wasu kwayoyin magunguna.

Kwayoyi da magunguna na samun cikin tagwaye:

Cikin gargadi kar ayi amfani da duk wani magani ko ƙwaya ba tareda tuntubar masana ko likita ba ayi hattara yadda ya kamata.

1. Tuntubar likita ko hadimin lafiya domin karbar ƙwayar daka iya sakin ƙwai na mace na haihuwa sama da guda ɗaya a lokaci guda. Ina fata an fahimci inda na dosa ina nufin akwai wasu magunguna da ake amfani dasu yanzu wanda idan mace tayi amfani dasu sazu iya janyo fitar da ƙwayoyi guda biyu na haihuwa.

2. Dashin É—an tayi a cikin mahaifa: za'a iya yi miki tiyata domin yi miki dashe na yara tagwaye a cikin mahaifarki.

Lokacin da ake ɗauka ciki zuwa aihuwa yana samun mako talatin da bakwai a kimiyyance sai kuma wasu yan saɓani daka iya faruwa ta bangaren macen. Su kuma cikin tagwaye yawanci yana ɗaukar mako talatin da biyar zuwa da shida kafin aihuwarsu.

A kammala wannan rubutu nawa ayi sani cewa a wannan zamani da muke ciki wanda ke ƙunshe da cigaba da yawa, hanya na yadda ake gane cikin tagwaye sunada matukar yawa amma wacce muka fi sani itace Ultrasound a fasahance sai kuma alamomi na gani da ido wanda suke faruwa ga uwa.

Post a Comment

0 Comments