Sakon soyyaya na dare

Sakon soyayya na dare 

Section A

Burinmu daɗaɗawa masoyan juna, munzo da sakon soyayya na dare, domin kyautatawa sahibinki ko kuma babynka. Asha soyayya lafiya.

Sakon soyayya na dare

Idan kana tareda budurwarka ko saurayinki, ya kasance kana yi mata ko kina yi masa kalamai masu daɗi da jan hankali musamman tura sakon soyyaya na dare, waɗanda zasu ɗinga faranta masa rai. A yau da izinin mai duka zaku samu duk abinda kuke buƙata dangane da yadda soyayyarku za'a ƙarfi har ma da armashi.

(1). Na daɗe ina kallon taurarin dake sararin samaniya da idanuna, Lokacin da naga wacce tafi kowacce haske, sai naga ba kowa bace nake gani ba sai ke masoyiyata. 

(2). So gamon jini ne, haƙiƙa son ki ya zamto jinin jikina. Kin fita daban a cikin yan'mata.

(3). Wannan shine sakon soyyaya na dare na uku, Duk lokacin dana kalle ki, sai naga tamkar babu kyakykyawar mace sai ke, ki kwantar da hankalinki masoyiya ta babu wata a zuciya sai ke kaɗai. Kula da amincewarki gareni, sune zasu tabbatar da soyayyarki ta gaskiya a tare dani.

(4). Farinciki baya ɗorewa a rayuwa sai tareda baƙinciki, dan haka kowane hali nake ba zan taɓa mantawa da kai ba masoyina. Nakan raba dare ina tunaninka abin begena. 

(5). Kamar yadda kowacce bishiya kanyi rashe a sama, kuma tayi saiwa a ƙasa, haka sonka ya mamaye ilahirin jikina.

(6). Da so samu ne na kasance dake a duk bugun zuciyata, ƙaunarki ce take ƙara tasiri a ruhina, babban burina shine naga bayyanar murmushinki a kan wannan kyakykyawar fuskarta taki, ya zamana kuma nine sanadin hakan.

(7). Sakon soyyaya na dare lamba ta bakwai, Kina da wadatar abinda mata da yawa suke nema kuma su rasa, ke kanki kinsan a cikin jinsin mata irinku kaɗan-ne, da a ce na iya rubuta labari da akan fuskarki kawai zan rubuta littafi mai suna Annurin Zuciyata. 

(8). Sararin samaniya cike da taurari, tekuna suna cike da ruwa, doran ƙasa kuma na cike da ciyayi, amma ni zuciyata cike take taf da soyayyarki, bata gushewa kamar yadda taurarin sama basa gushewa, bata ƙafewa tamkar yadda teku baya ƙafewa, haka zalika bata bushewa kamar yadda ciyayin doran ƙasa sukan bushe, soyayyarki dauwamammiya ce a cikin farfajiyar birnin zuciyata.

(9). Da za'a tsaga jikina da anga jininki yana gudana, a kan ƙaunarki ina iya manta kaina, ki kan hau ingarman doki domin ki taho mafarkina, wannan sunan dake ɓoye a tafin hannunki idan dare yayi, ki duba sararin samaniya zaki ga mai wannan sunan yana haska duniya masoyiyata, hakika na kasance mai bayyana a cikin mafarkinki, ke kuma kin kasance a fatar leɓena. 

(10). Duk wani taku da nayi a doran wannan duniya sai inji takun na iso ni zuwa gareki. So marurun zuciya yayimin saƙa tun asali, sonki ya shige zuciyata yanamin suka.

(11). Lamba ta sha ɗaya a sakon soyyaya na dare, Ganinki ne burina, idaniyata a cikin bacci ko na farka, ki riƙe soyayyata abadan, kada ki bari na koka, bani barinki cikin ƙunci har abada zo nayi miki tarba. 

Section B

(1). Daga motsin bugun zuciya kika ziyarci rayuwata a matsayin annurina, a duk zantukana sai na ambaceki. Damuwarki kullum tana cikin tunanina kuma bana sonta, kece jindaɗina kuma kece ɓacin raina, ke kaɗai ce a zuciyata, kalamaina, zaɓina, saboda dake kawai nake rayuwa, ƙaunarki ce ke kula dani, kuma ita ke kauda duk wata damuwa daga raina, koda a ce babu ni, kasantuwata zan zamana a tareda ke har abada. 

(2). Kamar yanda fatar baki ba zai furta ba, haka zalika jiki bai isa ya nuna ba, sannan tayi kaɗan ta kwatanta wato ita kanta zuciya, ruhi ne kaɗai yasan yadda nake ji, a sakamakon ziyartar da yake yiwa ruhina a kowane dare, ina sonki ba zan daina ba har gaban abada saboda ban isa na daina ba.

(3). Sakon soyyaya na dare lamba ta uku, Soyayyata dake bata mutuwa haka zalika bata tsoron mutuwa, koda za'a yi mana kwace, ko da zamu mutu kuma zamu lalace to soyayyarmu zata kasance a raye ne, na bayar da zuciyata na karɓina duka zuwa gareki. 

(4). Ki tallafi rayuwata data tsunduma cikin soyayyarki, ki tausayawa zuciyar data shagala a kan soyayyarki, kada rintsi ko zugar mahassada yasa ki gujeni ko kuma ki rage son da kikemin, sonki yana danƙare a zuciyata tamkar yadda kwakwalwa ke danƙare a kan ɗan adam, da a ce zan samu ikon fito miki dashi da nayi domin ki ƙara gasgata tsananin ƙaunar da nake miki.

(5). Na sanya jari wanda har yanzu nake samun riba, amma kuma babu asara. Asusun dana sanya jarin nawa kuwa ba ko wane asusu bane illa zuciyarki. 

(6). Sakon soyayya na dare lamba ta shida (6). Kinyimin miliyoyin ƙananan abubuwan da suka kawomin farinciki a raina. Kinyi ruwa kinyi tsaki a cikin birnin zuciyata yake masoyiyar ruhina. 

Zafafan kalaman soyayya idan suka shiga birnin zuciyar masoyi, sukan samu bigire mai yawa su kuma zauna daram. Tura mata kalamai na soyayya masu sururutar haɗe da shagaltar da zuciya kamar haka;

Section C

(1). Ya ma'abociyar kyan fuska da kamala ki buɗemin ƙofar zuciyarki na shiga ciki ko na samu na rayu a wannan duniya.

(2). Kina sawa na mance yadda ake numfashi. Haka zalika kece madubin dubawata.

(3). Ance kowa tara yake bai cika goma ba, amma ke kin zarce goman. Abinda kawai nake buƙata a yanzu ke ce.

(4). Ina sonki jiya amma nafi sonki yau, kuma zan fi sonki a gobe.

(5). Na ƙagu na dawo gida domin nayi katari da kyakkyawar fuskarki.

(6). Zuciyata tana son dukkanin taurarin da suke sama, amma du da haka ba za’a haɗa son da nake yi musu da wadda ke a cikin idanuwanki ba, domin shi wannan so na daban ne, ina sonki.

(7). Lambta ta bakwai a cikin sakon soyayya na dare, Lokaci na nan zuwa da zaki mallakawa wani zuciyarki, ina mai yin kira a gareki daki tabbatar da cewa kin mallakawa wanda ba zai raunata zuciyarki ta hanyar yaudara koma cin amana ba, Domin ita zuciya daya ce babu wadda zaki ɗauko ki sauya a lokacin da baƙinciki da damuwa suka mamaye zuciyarki.

(8). Yanzu haka ina cikin farinciki, shin kin san mene ne dalili? Hmm! saboda na kasance mai sa’a, kin kuwa san ta yaya? Saboda na samu wata babbar kyauta, kin san mene ne? ba komai bane ba face "KE" Sahibata.

(9). A koda-yaushe lokaci tashi yake tamkar tsuntsu, amma ita soyayyarmu kullum ginuwa take tareda ƙara samun wajen zama a cikin zuciyoyinmu, kada ki manta dani ki kasance mai yin tunanina kamar yadda nima na kasance a koda-yaushe.

(10). Abinda na keji a dangane da kai gaskiya ne, kaima nasan kasan da cewa ina sonka, a duk lokacin daka barni ba zan iya motsawa koda nan da can ba, wannan shine abunda zai faru dani a duk lokacin dana rasa ka.

(11). Sakon soyyaya na dare lamba ta sha ɗaya, So tamkar wata sarƙar zinare ce data ɗaure zuciyoyinmu a waje ɗaya, a duk lokacin daka tsinka wannan sarƙar to ka tabbatar da cewa tamkar ka kore farinciki ne daga cikin zuciyata.

(12). Ina sonka, meya sanya kake yin kokwanto a bisa kalmar so dana furta a gareka? Tabbas kaine mutum na farko da haɗuwa dashi ya koremin baƙinciki, ya wanzar da farinciki a zuciyata, ya yalwata murmushi a saman fuskata, dalilin da ya sanya nake kiranka da "SADAUKI".

(13). Na goma sha uku a section na ƙarshe sakon soyayya na dare, Kayi nasarar jan ra’ayin soyayyata akanka, kai ne na mallakawa linzamin zuciyata, kaine na farko dana taɓa furtawa kalmar "SO" kuma a yanzu ma zan kara maimaitawa a gareka, ina son ka.

(14). Ka amince muyi tsaftatacciyar soyayya. Sai yanzu na gano cewa a duniya babu abinda ya kai masoyi daɗi, a duk lokacin dana rasa ka bansan halin da zan shiga ba, daga ƙarshe ina sanar da kai cewa, burina yanzu bai wuce na ganin ranar da zaka zamto ango ni kuma mata a gare ka ba, ina alfahari da kai a duk inda nake, ka huta lafiya daga mai son ganin farincikinka a koda-yaushe.

(15). Sakon soyyaya na dare na ƙarshe, Sarauniyar yan'mata kyawawa mai cikar haɗuwa a matsayin cikakkiyar mace, ki sani cewa ina sonki sosai na kuma nayi missin ɗinki sosai tawan, love you.

Post a Comment

0 Comments