Kalaman so

 Kalaman So

Kalaman So domin jin daÉ—in lovers watau masoya. 

Ke kamar hasken wata ki ke mai hasken da ke haske idaniya, haka kuma kalamanki tamkar siga suke ma’abocin zaaÆ™i, tabbas kin yi kama da kanki hakan ya sanya na ji ina son ki.

A lokacin da kika ji kina son wani, to yi maza ki adana sunan shi a cikin ɗaya daga cikin kogunan da ke a cikin zuciyarki, domin kuwa ita zuciya takan iya raunata a koda wane lokaci amma shi kogon zuciya ya kan kasance tare da ajiyar da aka yi a cikin shi har abada. Ina fatan zan kasance ni ne wanda za ki adana a maɓoya mafi sirrinta soyayya da masoyi? Ina son ki.

Sau da yawan lokaci idanuwana sukan yi kishi da zuciyata!!! Kin kuwa san dalili? Saboda a koda yaushe kece abu mafi kusanci da zuciyar tawa su kuma idanuwa kin kasance mai yin nesa da su. Ina son ki sosai da zuciya É—aya.

Na kasance ma’abocin soyayya zuciyata ma ta gasgata hakan, lokaci na shuÉ—ewa soyayyar ki na Æ™aruwa a cikin zuciyata, a lokacin da ki ke cikin farin ciki kyakkyawar fuskar ki na bayyanar da murmushi mai taushi da tausasa zuciyar ma’abocin kallonta, kece wadda nake so a cikin zuciyata babu wata da zata iya canja matsayin ki a wajena. Ina Æ™aunar ki.

So tamkar rayuwane, ba ko yaushe yake zamowa abu mai sauÆ™i ba haka kuma ba a koda yaushe yake wanzar da farin ciki ba, to amma menene zai sa matsawar muna raye da rai da lafiya zamu yanke alaÆ™ar soyayya a tsakanin mu? Har zuwa yau babu kamar ki a cikin zuciyata domin kuwa jin muryar ki a kullum na ruÉ“anya adadin soyayyar da nake yi miki a cikin ko wane dare ko safiya. 

So tamkar kurɓar ruwan shayi yake mai tsananin zafi, a karon farko zaka kasance cikin shauƙin begen shi wanda daga bisani kuma zai ƙona maka harshe na tsawan lokacin da zaka shafe kana yin jinyar shi.

Soyayyar da nake yi miki tamkar tafiyace mai nisa da na fara yinta wadda bata da lokacin yankewa har abada. Na san burina zai cika matsawar ina tare dake domin kuwa dukkanin burina yanzu bai wuce na samun ki a matsayin matata uwar Æ´aÆ´ana ba. Ina son ki fiye da gwal ko kuÉ—i.

Kalaman So
Kalaman So pic#

Kada ki faÉ—awa kowa kalaman sirrin buÉ—e soyayya da Æ™awancen dake tsakanin mu, domin kuwa a dukkan lokacin da kika furta waÉ—annan kalaman sirri ga wani wato “INA SON KA” hakan na nuni da cewa zai yi amfani da shi wajen buÉ—e mana akwatin soyayyar mu ta sirri wanda hakan zai bashi damar yi mana gagarumar sata har ya yi sanadiyar raba ni da ke har abada. Ina son ki.

Na yi shiri tare da niyar turo miki da dukkanin soyayyata amma sai dai wanda zan turo da saÆ™on nawa gareki ta hannun shi ya bayyana hakan a matsayin wani babban abu da zai gagari bil’adama É—auka, amma kada ki damu zan zo nan bada daÉ—ewa ba domin ki tabbatar da abun da nake faÉ—a gaskiyane dama an ce zuwa da kai ya fi saÆ™o. Ki huta lafiya farin cikin zuciyata. Ina son ki.

Ina neman wata kalma wadda babu wanda ya santa. Ina neman wata kalma da zan furta miki cewa…..ke ta daban ce, ke kyakkyawa ce, kin zarce sauran mata. Zuciya ta da taki ba za su taÉ“a rabuwa ba har abada. Ina son ki sinadarin rayuwata. 

So shine abun da ya dunƙule zuciyoyinmu waje guda har muka tsinci kanmu a cikin soyayya, ina fatan ba zaki bari wani ɗan ƙaramin abu ya zo ya raba tsakaninmu ba? Ina son ki. Ke tamkar gishiri ce a cikin rayuwa ta, idan na rasa ki zan yi rayuwa ne da babu armashi a cikinta. Ki huta Lafiya.

Da akwai wasu tarin tsintsaye da suke wuni suna tattauna batutuwa a kan irin matsayin dana baki a cikin zuciya ta. Zan so kiji irin abun da suke cewa, domin kuwa a lokacin ne zaki tabbatar da irin son da nake yi miki. Ina Son Ki!

Da akwai miliyoyin furanni a cikin lambun masoya a wannan duniya. Da a ce zan tsunko kowanne fure na baki shi a hannunki, hakan bai isa ya bayyanar da adadin yadda nake son ki ba. Kece murmushi na, kuma kece farin-ciki na. Ina Son Ki.

Da akwai wasu lokuta da nake zubar da hawaye saboda ke, na san za kice saboda me?…..Da akwai wani lokaci da yake zuwa naji tamkar nayi fukafukai na tashi sama…..Kin kuwa san duk saboda mene ne? Saboda motsawar sonki a cikin zuciya ta da tsintar kaina a cikin matsanancin shauÆ™i a dukkan lokacin da naji muryarki ko na tuna da ke…..Ina fatan za ki amince mu rayu a tare har abada. Ina Son Ki!

A dukkan lokacin da dare ya yi, ki É—aga kanki sama ki kalli sararin samaniya, zaki ga wani tauraro yana saukowa izuwa gare ki, kada ki yi mamakin me ya sa haka ya faru? Ki yarda da ni, hakan zai iya faruwa a zahiri domin kuwa ni ma na yi hakan har ta kai ga na same ki. Hmm! Ki Huta Lafiya.

A lokacin da na samu soyayyarki sai na ji tamkar ni ne na fi kowa sa’a a duniya. A dukkan sanda na rintse idanuwa na sai na hango ni tare da ke muna tafiya a bisa gajimare. Idan na kwanta bacci sai nayi mafarkin mun zama mata da miji. Ina sonki, tare da son kasancewa a tare da ke har abada. Ki huta lafiya.

Sama cike take da taurari masu hasken da ke haske duniya a cikin kowanne dare. Amma haske mafi haskaka fuska da yaye duhun zuciya, na gan shi ne a cikin idanuwanki. Ki Kula Min Da Kanki. Ina Son ki.

Furanni na furta kalmomin yabo a kanki a dukkan lokacin da na shiga lambu mai ɗauke da ƙorama gami da korayen ciyayi da bishiyu masu ɗauke da tsintsaye. Sukan rera baitukan yabo a gare ki, cikin harshen da zuciya ce kawai ke iya fahimtarsa. Ina Son Ki.

A mafarki da kuma a cikin soyayya babu abun da ba zai iya faruwa ba. Ina son ki sosai hakan ya sa nake ji tamkar ba zan iya rayuwa idan ba tare da ke ba. Ba na fatan rasa ki a rayuwa ta, domin kuwa a dukkan lokacin da na rasa ki, na tabbatar da rayuwata zata shiga garari. Ina Son Ki kuma ba zan taɓa canjawa a kan hakan ba.

Tsuntsaye na buƙatar fukafukai domin tashi, kifi na buƙatar ruwa domin ya yi rayuwa, ni kuma ina buƙatarka domin nayi rayuwar farin-ciki. Ina son ka masoyi na!

Ina son jinka a kusa da ni, ta yadda numfashi na da naka zasu gauraya, ta yadda zan ke juyo sautin bugun zuciyoyinmu na fita a tare. Mu kasance a tare har abada. Ina Son Ka!

A kullum na kwanta bacci, na kan yi mafarkin ka zama uban Æ´aÆ´ana na, ni kuma na zama mata a gare ka. Sai dai na san iya mafarki ba zai wadatar da ni ba a bisa kulawar da nake tunanin samu daga wajenka. A saboda haka nake fatan mafarki na ya zama gaskiya wata rana. Ina Son Ka! 

MASOYI NA.

Ina Son Ka, zan kuma cigaba da sonka tun daga fitowar rana har izuwa faÉ—uwarta a cikin kowace rana har abada. Ka Huta Lafiya.

Ina fatan ka fahimci manufa ta? ina fatan ka gane nufi na a kanka? Zan rayu ne cikin sonka har zuwa ranar ƙarshe, saboda kai ba saurayi ne kawai a waje na ba, ka zama ruhi na, sonka na yawo ne a cikin jinin da ke gudana a jiki na. Ina Son Ka!

Ba zan iya misalta adadin yadda sonki yake ninkuwa a zuciyata ba a cikin kowace rana. Ina son ki matata. Babu wani abinci da yake yi min daɗi a baki na matuƙar ba ke kika girka shi ba. Ina nan tafe izuwa gare ki da shirin zuwa cin abincinki mai daɗi. Ki kula min da kanki.

Zuciya TA NA CIKE DA KEWARKI MATA TA.

Mata ta uwar Æ´aÆ´a na. Na kan yi kewarki sosai a dukkan lokacin da na duba gefe na ban gan ki ba. kamar kullum, yanzu haka ina zaune cikin tunaninki. Zuciyata na cike da kewarki, zan samu sassauci ne kawai idan na jiki a kusa da ni. Ki kula min da kanki har zuwa lokacin da zan dawo kulawarki ta dawo hannu na. Ina Son Ki. BA NI DA KAMAR KI.

Kalaman So#

Post a Comment

0 Comments