Kalaman barkwanci a soyyaya

 Kalaman barkwanci a soyayya

Abinda babba ya hango yaro ko ya hau tsauni bazai hango shi ba, taken kalaman barkwanci a soyayya kenan namu na yau.

Kalaman barkwanci a soyayya

A koda-yaushe ka kasance mai kula da budurwarka ko kuma matarka, domin hakan shine zai nuna mata irin kaunar da kake yi mata, kema haka karki bari wata ta kwace miki abinda kike alfahari dashi.

Section A

(1). Sonki tamkar wani fure-ne da idanu suke ƙawatawa da kallonsa, hanci yaji daddaɗan ƙamshinsa, ruhi kuma ya samu nutsuwa a kansa, Idan rayuwa ba zata yiwu ba tareda ruwa da iska ba, to haka nima ba zan iya rayuwa ba tareda ke ba.

(2). Masoyiyata gaskiya nayi nishaɗi da wayar-mu ta jiya sosai domin kuwa kin nunan cikakkiyar kulawa babyna. Love you so much!

(3). Idan rayuwa ba zata yiwu ba tareda abinci da abun sha ba, haka nima ba zan iya rayuwa ba tareda ke ba masoyiya. Jindaɗi da walwala ba zasu taɓa samuwa a tareda ni ba, idan babu soyayyarki a cikin raina. Kin zama tauraruwa dake haska ilahirin bishiyoyi da furannin da suke a gonar zuciyata.

(4). Na huɗu a jerin kalaman barkwanci a soyyaya, My lovely man kana a raina, pls ka faɗamin me kayi min na yarda da kai lokaci guda, bayan kuma ni ba haka nake yarda da maza lokaci guda ba, kuma da gaske kana sona kuwa? Nasan kana sona a baki amma bansan zuciya ba, amma fa idan har kana sona ya kamata ka nunamin kulawa aha.

(5). Hi yan'mata da fatan kina cikin jindaɗi da nutsuwa, kin sace zuciyata soyayyarki ta mamayeni tunanina, ya zama aikina kowane lokaci. Love you so much.

(6). Babbar yarinya kin sace zuciyata, tunaninki da kuma muryarki sune muradina, ina fatan ki wayi gari lafiya. Love you!

Jindaɗin soyayya da mace shine ku kasance tare a koda-yaushe, sannan kuna buƙatar wasu kalaman soyayya masu barkwanci, gajeru har ma da dogaye domin inganta soyayya.

Section B

(1). Kalaman barkwanci a soyyaya na farko, Mutane sun ce hoto yana nuni da kalmomi masu yawa, amma ni ba abinda na gani a ciki sai kalmomi uku: “I love you”

(2). Ina kewarki ldan bakya kusa dani, idan bana tareda ke ba abinda nake sai tunaninki, idan ina tunaninki sai naji kawai inason nayi rayuwa dake, idan na samu damar rayuwa dake shine mafarkina zai zama gaskiya.

(3). Naga cikar kamalarki, kuma nace ina sonki, yayinda naga rashin cikar kamalarki, sai naji na ƙara son ki sosai!

(4). Na huɗu a jerin kalaman barkwanci a soyyaya. Tunanina yana da damar zuwa ko ina, amma ina mamakin yadda yake zuwa ga naki tunanin koda-yaushe.

(5). Koda yaushe na kan faɗa soyayya a lokuta da dama saboda ke yar babyna, gaba ɗaya ilahirin jikina naki ne haka zalika zuciyata itama taki ce!

(6). Rayuwa babu ke tamkarr karyayyen alƙalami ne wanda bashi da wani amfani, amma rayuwa dake kamar rubataccen cikakken labari ne.

(7). Habibtee kin cancanci mallakar komai a wannar duniyar, duk da cewa bazan iya baki ita ba, amma zan iya baki duniyata.

(8). Kafin na gamu dake, ban taba sanin daɗin da ake ji, har yasa murmushi amma yanzu na gane daɗin rayuwa dake, shiyasa ba zan iya rayuwa babu ke ba.

(9). Na tara a kalaman barkwanci a soyyaya, A wasu lokutan idan na tuna dake idan bakya-nan, sai nayi murmushi, sai mutane sumin zaton ko na haukace ne.

(10). Zuciyata tana tafiya yawon duniya ne, da zarar tayi arba da kyawawan idanunki, maslaha da kwanciyar hankalina shine na sameki matsayin mata a rayuwata.

Section C

(1). Sauraron zazzaƙar muryarki, shi ke tada hankali, tashin hankalina daga gareki shi ke sanya zuciyata farinciki, kuma naji sanyi a cikin zuciyata.

(2). Nakan samu nutsuwa, nutsuwa mai sanyi sosai idan ina kusa dake, Ni fa na bayar da rai da Zuciyata domin ganin farinciki.

(3). Ina sonki sosai, ba dan yadda kike ba, sai dan yadda nake ji idan ina tareda ke, ke ta musamman ce a duk wani fanni a wannan duniya.

(4). Wani lokaci sai naji cewa zan iya jarraba rayuwa ba tareda ke ba, amma nasan a hanya zan faɗi matacce.

(5). Ɗaruruwan zuciyoyi sunyi kaɗan, su ɗauki soyayyar da nake miki.

(6). Nakan faɗa kogin soyayya sabuwa a duk lokacin dana kalleki!

(7). Koda-yaushe kece amsata, idan har aka tambayeni wa nake tunawa.

(8). Na takwas a jerin kalaman barkwanci a soyayya. Zan iya haura dutse duk girmanshi, kawai domin na haɗu dake, zan iya tafiyar kilomita dubu domin na zauna dake, ke wata jindaɗi ce ga ruhina. Ina sonki.

(9). Ke gimbiya ce a zuciyata; Sakan ɗaya baya wucewa ba tareda nayi tunaninki ba, koda-yaushe cikin begenki nake.

(10). Taya mace zata iya mallakar duk wasu abubuwan dake cikin zuciyata, ina mamakin hakan. Kece mafarkina. Kyakkyawar zuciyarki da murmushinki mai daɗi sune mafi kyawun bangarorin jikinki.

(11). Nakan tsinci kaina ina tunanin lokacin dana fara sanyaka a idanuwa na. Tun a wannan lokacin nasan na haɗu da mahaɗin annurin zuciyata. 

(12). Tun daga wannan lokacin, iya abinda nake so a rayuwata shine kasancewa tare da kai. Duk yadda rayuwa tayi tsanani, duhu ya mamayeni kallon fuskarka kaɗai, yana haskakani ya kuma wanke duhun daya rufeni. 

(13).  Kalaman barkwanci a soyyaya na sha uku, Babu komai a cikin zuciya sai kai, kai kaɗai ne, tareda tunaninka kuka taru kuka cikamin zuciya. 

(14). A cikin dubban miliyoyin mataye, idanuna ke kaɗai suke nema. Ki sani babyna ke zara ce a cikin miliyoyin taurarin mata, kece tauraruwarsu kece kuma ƴar autarsu, kuma kece kike haskaka su in-dai a cikin zuciyata ne. 

(15). Inaso kasan cewa: babu wanda zai iya canjaka ya ɗauke matsayinka a zuciyata ya canja shi. jerin kalaman barkwanci a soyyaya, Tunaninka daban-ne a cikin zuciyata. Kallon cikin idanunka yana sanyaya ruhina, begenka shine abincin zuciyata.

Post a Comment

0 Comments