Yadda ake tsara mace a waya
Da farko dai kaga yarinya tsaleliya, a tashin farko kaga tayi maka. Kaji duk duniyan nan kana son ka sace zuciyar yarinyar nan.
Kuma sai ya zamana ƙila yarinyar nan bai mai kula samari bace, ko kuma irin matan nan ne da idan kayi musu magana akan hanya bazasu saurareka ba idan bakai sa'a bama sai ta buga maka ƙusa. Kasan bature yana cewa;
"A person who want something will find a way. A person who doesn't will find an excuse.
To kamar hakane gareka, idan har da gaske kake kana son wannan ƴar talikar daka gani akan hanya, har kaji kanason sace mata zuciya, ma'ana dai kanason taso ka. To kai ne zaka bi duk hanyar daza kabi ka samu lambar yayinyar nan wato tauraruwar zuciyarka. Yarinyar data shiga zuciyarka tayi kane kane ta hana tunaninka sakat.
Lambar wayarta zaka samo domin tsarata. Abubuwa mafi muhimmanci da zaka farayi kafin kiranta a waya shine sanin basic informations akanta. Misali dolene kasan sunan wannan yarinyar, haka kuma kasan irin matakin rayuwar da take at present ma'ana a wannan lokacin.
Ina nufin kana buƙatar sanin ita ɗin ƴar makaranta ce, yanayin dabi'unta, gidansu ko unguwarsu duk da hakan bai zama dole ba. Amma zai iya taimaka maka wurin tsara abar ƙaunar taka.
Da zarar ka gama gamsuwa da bincikenka akanta. Abokina sai ka ɗaura niyar kiran yayrinyar nan. Irin kiran daza kayi mata yana buƙatar lokacin da yafi dacewa kayi shi. Take note !..
Idan har zaka daidaici dare, amma bafa can cikin dare irin ƙarfe sha ɗaya ko sha biyu na dare ba. A'a. Misali kamar ƙarfe takwas, tara ko ƙarfe goma haka. Saboda mai yiwuwa daga kai har ita a wannan lokacin baku da wani muhimmin aiki a ranar, sai dai kawai ya zamana ana ɗan hutawa ne kafin a kwanta bacci.
Idan ka dokawa talikar nan kira ka fara dayi mata sallama..misali;
"Assalamu alaiki yake ma'abociyar kyau, nutsuwa da sanyaya zuciya.
Duk wata mace ko wacece ita, komai jin kanta, ɗagawa ko tsiwarta tana son yabo, tana son namiji mai tattausan lafazi wanda ya iya sarrafa kalamansa kamar yadda shima namiji yake son mace don iya kalamanta da kuma tausasan lafuzanta.
Tasirin sallamarka a gareta zai saka ta amsaka. Amma fa daga nan kasa a ranka, kuma kayi expecting tambayar daza ta biyo amsawar tata.
Cikin irin wannan maƙewar muryar tasu ta mata da iyayi, zaka ji tace; Pls dawa nake magana ?
Kaga wannan tambayar tata ? Karkayi sakaci da ita domin tamkar tarko ce a gareka. Amsar da zaka bata ba wata mai wuya bace amma ka kula saboda daga nan ne tasirinka a wurin yarinyar zai ginu ko kuma ya rushe baki ɗaya. Kuma ba haka aka so ba.
_________________________________________
Yadda ake tsara mace a waya second edit
Kamar yadda na faɗa a sama, wannan tambayar tata;
"Pls dawa nake magana? zaka iya amsa mata ta hanyoyi masu yawa idan ka iya wasanka kenan, amma daga cikin hanyoyin da suka fi tasiri zaka iya amsa mata kamar haka;
"Kina magana da mai yi miki fatan alheri a koyaushe. Kina magana da mutum ne ɗan uwanki ba aljani ba yake sarauniyar kyau.
Irin wannan amsar zaiyi wuya bai saka yayrinyar nan darawa ba. Ma'ana zata iya yin dariya. Kasan Mace nason namiji mai barkwanci. Su mata mafi yawansu ƴan nishaɗi ne.
Daga nan kuma kayi expecting wata tambayar daga yarinyar nan kamar haka;
"To a ina ka samu number na ?..
Karka manta kai namijin duniya ne. Koma ta wace hanyar kabi ka samu numberta karka sake ka faɗa mata, domin yin hakan raunine daga ɓangarenka. Kuma idan ka faɗa mata yadda akayi ka samu numbernta zata ji haushin wanda ya bada numbern, kuma kai ma zata ɗauke ka lusari, daga nan in bakai sa'a ba za kaji tace maka malam sai anjima.
Amsar da yafi dacewa ka bata itace;
"Lambar wayarki abace mai tsada. Kamar yadda ake neman karatu, ko kuɗi da duk wani abu mai ƙima haka na ɓata lokacina na nemo lambarki yake sarauniyar mata.
Wannan amsar taka ina mai tabbatar maka cewa yarinyar zata ji kanta ya fashe, zata ji duk duniya babu ya ita saboda ka gama hura mata kai da zugar nan da kake yi mata.
Daga nan zata tambayeka dalilin kiran nan naka. Nan ma saika daidaita lafazinka, kuma sai ka iya wasanka sosai. Mutumina cenewa yarinyar nan;
"Na kiraki ne domin nemo nutsuwar da zuciyata ta rasa. Na kiraki ne domin hakan kamar yayyafawa raina ruwan sanyine saboda zafin da nakeji a cikinsa.
Zakaji tace hmmmm ! Alamun ta afka ramin ka.
Ina mai tabbatar maka wannan amsar zata kashe mata jikinta. Ina nufin idan ma da farko bata da niyyar saurararka to a yanzu wannan amsar taka zata canja mata ra'ayi ne.
Daga nan Mutumina sai kaci gaba da suburɓudo mata zafafan kalamai masu narkar da zuciyar ƴan mata. Ka bayyana mata daki daki ma'ana in details inji masu jajayen kunnuwa irin tasirin ƙaunar da kake mata a zuciyarka. Ka faɗa mata cewa ta sace maka zuciyarka a tun ranar daka fara kyalla ido ka ganta.
Mission ɗinka bai wuce yarinyar nan ta saurareka a wayar nan ba. A saboda haka yabon kyawun halittarta, yawan bata dariya da zuga da kambamata sune ginshiƙin amsa tayin soyayyarka ya kai ɗa namiji.
______________________________________
Yadda ake tsara mace a waya last edit
Bayanin daka karanta a sama karka manta bayanine na yadda zakayi idan ka kira yarinya a waya ba tare data sanka ba. Idan kuma dama yayrinyar budurwarkace to kai tsaye zaka riƙa amfani da kalaman nan naka dana ambata a baya irin kalaman da zaka narkar mata da zuciya.
Ka bayyana mata yadda zazzaƙar muryarta take kwantar maka da hankali tare da sama maka nutsuwa idan kana jin muryar tata.
Ka zayyano mata yadda hoton kyakkyawar fuskarta take maka gizo a duk lokacin daka rufe idanunka. Kai a taƙaice ma dai ka faɗa mata tunanin tane aikinka dare da rana. Haka zalika itace topic ɗin mafarkinka a duk lokacin daka kwanta bacci.
Yana da matuƙar muhimmanci ka rika turance yarinyar mutane idan har kana son ta faɗa cikin komar kifinka. Kalamai irinsu;
"You are the queen of my heart.
" You rule my heart baby.
Idan irin an kwana biyun nan ba a haɗu da masoyiya ba kuma ka riƙa mata kalamai irinsu "I miss you sooo much baby.. Idan irin ana waya ne ko a chat na hanyoyin sadarwa kamar whatsapp ana iya tura mata saƙo kamar haka" hugs and kisses"..
Mutumina ina gaya maka da wannan blue print ɗin ma'ana taswirar bayanin dake sama. Dashi tabbas haƙiƙa zaka sace zuciyar babyn ka !
0 Comments