Yadda ake tsara budurwa
Tunkarar mace a wurin ɗa namiji ba abu bane mai sauƙi, duk yadda maza suka kai ga musa wannan zancen to amma a cikin zukatan nasu sun san iyakar gaskiyar ɗaya ce.
Na sani kamar yadda kowa ya sani a tsakanin maza, za kuga akwai namijin da tunkarar mace da tsara mata kalamai har ta faɗa komar kifinsa, abu ne mai matuƙar sauƙi a gareshi. Amma yayin da duk ka samu ɗa namiji irin wannan, watau wanda baya shayin tare yarinya haɗe da tsarata to ka lura ka gani, sai ka samu aƙalla maza biyar da ba zasu iya tunkarar mace kamar yadda wannan ɗayan yake yi ba.
Ma'ana dai, maza waɗanda basa iya tunkarar macen da suka ga tayi musu sun nunnunka mazan dake iya tunkarar mace kai tsaye ba tare da wani shiri ko tunanin yadda zai tsara zancen sa ba. Ya kai mai karatu idan kasan kana ɗaya daga cikin irin mazan nan da suke tsawaita tunani kan yadda zasu tunkari yarinya budurwa wacce suka kyalla ido suka hango tayi musu, amma basu san yadda zasu tunkareta ba, tare da hakan kuma suna kokwanton irin lafuzan da zasu yi mata amfani dasu wanda suke fatan tasirin kalaman nasu yasa yarinyar nan ta shigo cikin komar su, to ina maka albishir wannan rubutun anyi shine kacokan domin irinku, idan kai ka iya hannunka to lallai ka faɗawa wannan abokin naka ko nace amininka daka san yana da irin wannan matsalar, to gareshi.
Zanyi bayani akan yadda saurayi zai tunkari budurwa kai tsaye da maganar soyayya ko kuma zai bayyana soyayyar sa ga wacce yake so ba tare da yaji tsoro ko wata fargaba a cikin zuciyarsa ba.
Amma kafin nan akwai wani jan hankali da nake so nayi wa ɗan uwa namiji da yake yin soyayya ko kuma kai dake shirin fara soyayya domin kaucewa wasu abubuwan da idan aka faɗa cikinsu a duniyar soyayya to komai yana iya faruwa.
Akwai wasu tarin hanyoyi masu yawa da zaka iya amfani dasu wajen sace zuciyar wacce kake so, wasu daga cikin waɗannan hanyoyin ma ba sai ka tunkari budurwa kai tsaye ba, ita da kanta zata iya zuwa ta faɗa maka tana son ka, duk da dai su mata an san su da yanga, kunya da kuma jan aji.
Amfani da kalaman soyayya masu daɗi da matuƙar inganci a lokacin da kake gwagwarmayar neman soyayyar mace ko kuma nace neman amincewar zuciyarta.
Ka riƙa tauna duk wata magana kafin ka furta ta, hakan yana da matuƙar muhimmanci domin kuwa bahaushe yana cewa; magana zarar bunu ce idan har ta fita to ba'a dawo da ita.
Kasance mai lissafi tare da tabbatar da cewa kana tauna duka wata kalma da zata riƙa fitowa daga bakin ka kafin ka furta ta zuwa ga wacce kake so.
Idan har ya zamana kullum kana amayar da maganganu ko kalamai marasa daɗi to tabbas za kaci karo da babbar matsala a rayuwarka ta soyayya gaba ɗaya.
Kada ka kasance mai tsauri da takura mata akan ra'ayoyin ka domin hakan zai sa ta riƙa kosawa da kai kuma ta daina marmarin yin hira da kai, kar ka manta saurayinta ne kai kawai, ba malaminta ba, ba ubanta ko mai ɗungurumgum wato mijinta.
Haka kuma kayi ƙoƙarin zama mai yarda akan duk abinda tazo maka dashi, idan ya kama nayin gyara ne to sai kayi mata gyaran cikin siyasa da wasa ba tare da taji ba daɗi ba.
Yadda Saurayi Zai Tsara Budurwa
Da zarar kaga budurwar da kake so ko wacce ka daɗe kana sonta kada ka tsaya kokwanto haka kuma kar kayi ƙasa a guiwa. Idan a taron jama'a ne to kar ka tsayar da ita domin ba zata wani saurareka ba, ko kuma baka wata dama tayin magana da ita. Yayin da kake tunkarar ta, ka kasance cikin tsabta, dressing mai kyau, irin na birni ko kuma dai wani naka salon da kasan yana yi maka kyau.
Sai kabi ta sannu a hankali a baya, kuma lallai ka gyara, ka kuma daidaita takun ka ta yadda ko da ta juyo ba zata gane cewar ita kake bibiya ba. Idan kaga anzo wurin da yake a nutse ba kan hanya ba, wuri mara hayaniya, wurin da babu idanun jama'a a kanku, kowa harkar gabansa yake, abokina rangaɗa mata sallama.
"Assalamu alaikum.. Ita kuma zata amsa maka tare da kallon ka ta gefen ido. Wannan ɗan kallon gefen idon da zata yi maka na wasu ƴan sakanni, za kayi mamakin lissafin irin abubuwan data karanta a tattare da kai.
"Ƴanmata idan ba zaki damu ba, ki ɗan bani mintuna biyu zuwa uku cikin lokacin ki (zata nemi tayi maka musu, ko tace ita sauri take ana jiranta ko kuma zaka ɓata mata lokaci) kar ka wani damu da wannan.
" Kiyi haƙuri wani ɗan saƙo ne zan isar miki daga wurin abokina, cikin sauri za kaga ta nemi sanin wanene ya bada saƙo wurin ta kuma menene saƙon.
Daga nan kai kuma sai ka nutsu sosai ka bayyana mata abokin nan naka ya kamu da soyayyar ta mai tsanani da daɗewa, kawai dai yadda zai zo ya tunkare tane ya faɗa mata ya kasa har yanzu. To amma yau kai a matsayinka na amininsa kuma babban abokinsa kazo ka bayyana mata komai ayi ta ta ƙare domin idan ka bari to shi kuma abokin naka zai cigaba da cutar da kansa ne (dama ka bayyana mata yana cikin damuwa saboda soyayyar ta). Ka bayyana mata cewa idan har wannan abokin naka ya cigaba da shiga damuwar ta, za'a iya samun matsala sosai koma ya rasa rayuwar sa gaba ɗaya.
Da zarar taji haka cikin hanzari zata nemi tasan wanene wannan abokin naka. Zama ta tambayeka ya sunansa? (trust me, we know how they think after years of studying them). Tana yi maka wannan tambayar kai kuma ɗan uwa, dama kana tafe da wayarka a hannunka ɗauke da hotonka akan screen ɗin wayar, nuna mata fuskar wayarka.
Zata yi mamaki tare da jeho maka tambayar wannan ai hoton ka nake gani. Kai kuma sai ka faɗa mata cewa eh, haka ne, dama kaine abokin naka kuma kai ne kake cikin mawuyacin halin nan da kake faɗa mata saboda soyayyarta data cika maka zuciya.
Hakan da kayi zai sa taji mamaki, kunya har ma da dariya wanda kuma hakan ne zai burgeta da kai kuma ya bata nishaɗi, kar ka manta sufa nisa'u inji balarabe kenan watau mata, mutane ne ƴan nishaɗi. Idan kazo da irin salon dana gama misalta maka to ko baka samu yadda kake so ba sosai, amma wannan haɗuwar taku ta farko dai, kar ka manta domin ka bata nishaɗi ka kuma saka ta dariya.
Kana da hanyoyi da dabaru masu tarin yawa domin tunkarar wacce kake so, sai dai kuma kar ka manta, a tare da hakan ka zama mai tunano irin sharuɗɗan dana gindaya maka a can sama matuƙar kana son cikar burin ka na samun soyayya ko kuma ingancin ta.
Samari na barku lafiya!
0 Comments