Yadda ake matsi da tumfafiya

 Yadda ake matsi da tumfafiya 

Calotropis procera tumfafiya kenan, wani nau'in tsire-tsire ne na fure a cikin dangin Apocynaceae wanda ya fito ne daga Arewacin Afirka, Pakistan, sassan, Yammacin Asiya, Kudancin Asiya, Isra'ila, da Indonesia. 

Yawanci tana girma zuwa tsayin ƙafafu 6 (1.8m) zuwa ƙafa 8 (2.4m) (da wuya ta kai ƙafa 15 (4.6m)) a cikin rana da wani yanki mai inuwa, gami da wuraren kiwo, filayen kiwo, bakin titi, filayen kogi. da magudanar ruwa. Koren yayan itacen sa yana ɗauke da ruwan madara mai guba watau poison wanda yake da ɗaci sosai kuma yana juyewa ya zama manne wanda ke jure wa sabulu.

Sunaye gama-gari na shukar sun haɗa da tufar saduma, watau sodom apple, itacen zakaru, kambun sarki, ƙaramin furen kambi, katuwar madara,  daji na roba, ko itacen roba.

Sunayen "Apple of Saduma" da Tekun Gishiri" sun samo asali ne daga tsoffin marubutan Josephus da Tacitus, waɗanda suka kwatanta shukar dake girma a yankin Saduma a littafi mai tsarki. Ko da yake ba ƴan asalin yankunan ba ne, shukar tana ciyar da ma'auni na malaman buɗe ido a California, Hawaii da tsibirin Caribbean na Puerto Rico.

Kamar dai yadda kowa ya sani ana sarrafa furen tumfafiya ta ko wacce hanya, domin samun biyan buƙata musamman ga 'yan uwa mata, da ke son gyaran jiki. 

Kafin nayi bayani kan yadda zaki yi matsi da tumfafiya zan so na fara jan hankali ko kuma tunantarwa akan abubuwan da suke kawo illoli ko cututtuka a gaban mace;

Rashin sanya pant. 

Barin pant yayi dauɗa sosai ba a canja ba. Ana so inda hali kullum a canja pant sau biyu a wanke. 

Saka pant a jiƙe da ruwa. 

Yawan tsarki da ruwan sanyi. 

Yawan tsarki da ruwan da zafinsa yayi yawa. 

Rashin aski. 

Wasa da gaba. 

Yawan cin ɗanyar albasa. 

Yin amfani da magungunan mata marasa inganci. 

Daɗewa akan masai ko toilet. 

Rashin shan iska.

Musanyar tufafi. 

Saduwa da mai cutar. 

Cutar aljanu, wato jinnul ashiq. Su ma suna sanyawa mace infection mai wuyar magani. 

Illolin da sanyi ko infection yake yiwa mata;

Yana sa rashin sha'awa. 

Yana sa ciwon mara mai tsanani. 

Yana haifar da ƙurajen bakin mahaifa ko ya toshe mahaifar baki ɗaya. 

Yana sa mace ta ɗinga jinin al'ada baƙi ƙirin mai wari. 

Yana sanya farin ruwa mai wari ya ɗinga fito mata. 

Yana sanyawa a ɗinga jin mace tana wari mara daɗi kuma a rasa ta ina yake fitowa duk wankanta. 

Yana sa jin zafi yayin saduwar aure ko kuma ganin jini a maimakon ruwa. Yana rikitawa mace kwanakin al'adarta, su ɗinga ƙaruwa ko raguwa ko jinin ya ɗinga wasa. 

Yana sanyawa mace tusar gaba, wato iska ta ɗinga fita ta gabanta. 

Yana sanyawa mace yawan ɓarin ciki ko kuma rashin shigar cikin kwata-kwata. 

In yayi ƙarfi yana hana mace haihuwa. 

Wani infection ɗin alama ce ta zaman aljanu a jikin mace, musamman idan tana mafarkin namiji dare ko jarirai.

Abin lura:- 

Idan mace tayi magungunan asibiti da kuma irin waɗannan dana  ambata amma infection din bai warke ba, To ta nemi maganin jinnul ashiq, wato magungunan aljanu don zai iya yiwuwa matsalarsu ce. Ɗaya daga cikin manya manyan magunguna na irin matsalolin dana jero a sama ana sarrafa sune da saiwa, ko ganye ko kuma furen tumfafiya, wanda bayan magance miki matsalarki da zaiyi, zai kuma taimaka wurin tsukewa ko matsewar farjinki da kuma ƙarin ni'ima. Ana sarrafa shi ta hanyoyi da dama kamar haka;

MAGANIN SANYIN MATA KO INFECTION 

Idan mace tana fama da ƙaiƙayi ko ƙuraje ko fitar farin ruwa mai wari ko bushewa ko ɗaukewa ko buɗewa da kwailewa da rashin sha'awa ko gamsuwa da sauran cututtukan sanyi, sai a gwada ɗaya daga cikin waɗannan hanyoyin;

A samu saiwar  tumfafiya da sassaƙen magarya, sai a tafasa, idan ya ɗan huce sai mace ta ɗinga kama ruwa da shi. Kullum sau ɗaya. Yana maganin buɗewar gaba da ƙaiƙayi. 

A samu garafuni da sassaƙen tumfafiya sai a tafasa, Sai mace ta ɗinga shan rabin kofi da safe, rabi da yamma. Yana fitar da dattin mara da maganin farin ruwa mai wari. 

A samu furen tumfafiya, sai a shanya ya bushe, a daka a ɗinga zubawa a cikin nono ana sha. Yana magance matsalar ruwan infection. 

A samu kwallon tumfafiya, lalle da ganyen magarya da kanumfari, a haɗa waje ɗaya a daka sannan a tafasa a zuba farin miski a ciki. Idan ya ɗan huce sai ta shiga ciki ta zauna tsawon kamar minti goma. Yin hakan yana maganin ƙaiƙayi da ƙuraje da buɗewar gaba da ɗaɗewar gaba. 

A dafa ganyen tumfafiya da  zogale, idan suka dahu sai a murje su ko a dama, a tace, ayi lemon juice da shi. Yana maganin fitar farin ruwa mai wari da cushewar mara kuma yana ƙara ni'ima.  

A samu kwallon tumfafiya da albabunaj a tafasa a zuba man hulba a ciki. Sai ta ɗan tsuguna tururin ya ɗinga shigarta. Idan ya ɗan huce kuma sai ta shiga ciki ta zauna. Zai magance mata ƙaiƙayi da ƙuraje kuma yana sa matsewar farji sosai. 

A samu ɗan kwallon tumfafiya da farar albasa da kanumfari da citta da malmo da barkono da raihatul hubbi, sai a dake su ayi yaji a ɗinga cin abinci da shi. Yana saukar da ni'ima da magance duk matasalolin sanyi.

A samu saiwar tumfafiya da ciyawar kashe-zaƙi da farin magani sai a haɗa waje ɗaya a ɗinga jiƙa rabin ƙaramin cokali ana sha. Sannan a ɗinga shan man zaitun cokali ɗaya kullum kafin a karya. Wannan yana maganin dattin mara da wanke dauɗar mahaifa.

Ki ɗinga goga furen a ƙofar farjinki, wannan danshi danshin ruwan ake so. Ki saka kaɗa kina murza ruwan a wurin. Idan kin tabbatar da ruwan sun mamaye ilahirin farjinki, sai ki jira zuwa minti biyar sa'annan ki saka ruwan ɗumi ki wanke. Wannan maganin infection da sauran cututtukan sanyi haka kuma zai miki matsi sosai. 

Yadda ake matsi da tumfafiya
Yadda ake matsi da tumfafiya.

A nemi ganyen gamji dai dai misali,sai a nemo saiwar tumfafiya a tafin hannu haka ba yawa,sai a shanya su bushe,idan sun bushe sai a nemi garwashi a kasko a tirarawa farji. Wannan ma na matsi ne sadidan. 

Zaki nemo ƙwallon tumfafiya, ba tare da an fashe shi ba, za a shanya shi (kuma a guje wa yin abinda zai fashe kafin a shanya shi), sai ya bushe sosai, kafin a dake shi ya koma gari.

Za a iya tankaɗewa, amma abinda ya fi, za a cire wani farin abu mai kama da kaɗa, wanda shi ba zai daku ba, sannan a nemo man shanu mai kyau, shi ma ɗanye wanda ba a soya ba.

Za a haɗa waɗannan ababe biyu a wuri guda, a cakuɗe su sosai, sai a samu mazubi mai marfi, a saka, a rufe.

Za ki ɗinga shafawa farjinki, amma zai kasance kina murzawa tsayin lokaci, ba iya shafawa ba. Ma’ana, idan ki ka shafa, za ki ɗinga sanya hannu kina matsawa, tamkar dai kina fatan ki shigar da maganin ga cikin fatar ba iya samanta ba.

Wannan haɗin zai ƙarawa mace ni'ima sosai, ya kuma matse mata gabanta. 

Abin lura:

Sanin mu ne man shanu ɗanye na da ƙamshin da ba kowa ne yake sha’awar jinsa a jikinsa ko jikin matarshi ba, don haka yake da muhimmanci uwargida ta san lokuta da suka fi dacewa ta yi amfani da wannan haɗin, da kuma yadda zata kula da jikinta bayan ta tabbatar haɗin ya gama shigewa a inda aka saka shi.

Ma’ana dai, ta tanadi turare musamman don tabbatar da idan ta yi wanka za ta iya ɓatar da warin man daga jikinta.

Post a Comment

0 Comments