Yadda ake matsi da gishiri

 Yadda ake matsi da gishiri 

Shin ko kunsan yadda amfanin gishiri yake a gaban mace? Kamar yadda aka sani gishiri na maganin cututtuka da dama musamman cutuka irin na Bacteria da suke damun mata. 

Ana yin amfani da gishiri haka don magance kaikayin gaban mace domin yana aiki sosai wajen kashe dukkan wasu cutuka na bacteria. Yin amfani da gishiri a gaban mace yana iya Kawar da duk wasu cututtuka dake damun gaban mace.

Yadda ake matsi da gishiri
Yadda ake matsi da gishiri.

Yin amfani da gishiri a gaban mace ba wai kawai saka shi ba. Kada a shafa gishiri kai tsaye a kan gaban mace, sannan a kula sosai a yayin da za'a yi amfani da gishiri a gaban mace, kada a yi amfani da shi idan akwai ciwo a gaban mace.

Yadda Amfanin Gishiri Yake A Gaban Mace 

Idan mace na fama da kaikayin gaba, ta samu  gishiri a zuba a mazubi mai kyau a kara ruwa, an fi son a yi amfani ruwan dumi domin gaban mace ya fi son ruwan dumi, sai a zuba gishiri kadan, za a dibi wannan ruwan ana yin tsarki dashi a gaba mace.  Sannan kuma, ana iya samun ruwan dumi a zuba gishiri a ciki, sai a zauna a cikin ruwan na tsawon mintuna 15 zuwa 20

Baya ga maganin kaikayin gaba, yin amfani da ruwan gishiri a gaban mace na kuma bada kariya na hana kananan cutuka zama a gaban mace. Sannan a kiyaye, kada a yi amfani da sabulu, ko wasu mai da ba likita ne yace a yi amfani dasu ba wajen wanke gaban mace, yin hakan ka iya kara yawan kaikayin da ake ji. 

Gishiri Æ™unshe yake da sindarin dake yaÆ™i da cututtuka da bunÆ™asa garkuwar jiki. White blood cells, watau wasu kwayoyin halittu dake da alhakin yaÆ™i da cututtuka a jikin É—an adam suna Æ™ara Æ™arfi ne sosai idan mutum ya jiÉ“anci amfani da gishiri. 

A riÆ™e wannan. 

Shan ruwan gishiri kuwa yana taimakawa kwarai wurin narkar da abinci cikin sauri da daƙile cutar ulcer.

Shan ruwan gishiri na yin maganin cutar kwalara, da jiri, da saisaita sukari a cikin jini, ga masu cutar sikari kenan, watau diabetes da kuma masu lafiyar ma, yana kuma tabbatar da lafiyar hanta.

Gishiri na ƙara lafiyar ƙashi, da daƙile kamuwa da cutar sanƙarau ko ciwon cancer.

Haƙika amfanin gishiri a jikin ɗan adam yana da matuƙar yawan da idan lissafi za'a yi, to sai ayi littafi guda a kansa. Anan dai zan tsaya a nan domin shiga wani babin.

Gishiri (ruwansa) na da matuƙar amfani ga mata. Shi yasa zai kyautu mace ta rinƙa shansa [ko da jifa-jifa ne] domin irin alfanun da yake da shi.

Daga cikin amfanin gishiri ga mata akwai ƙarin ni'ima; duk macen data juri shan ruwan gishiri to lallai zata yi ni'ima kuma maigida zai ji daɗin mu'amalar jima'i da ita.

Ga macen da kuma take fama da matsalar rashin kwakkwaran kwan haihuwa [wanda shi ke jawo rashin É—aukar ciki] to ta juri shan ruwan gishiri. 

Bugu-da-ƙari gishiri na rage saurin tsufa. Kai yana ma taimakawa wurin rage ƙiba da ƙarin kuzarin mata yayin jima'i.

Ga macen da take fama da ciwon mara yayin jinin al'ada ko kuma kwanakin da take shafewa tana al'ada suke tsayi, to ta juri shan ruwan gishiri domin yana rage tsayin kwanaki da ciwon mara yayin al'ada.

Yadda Ake Matsi Da Kanunfari.. 

Idan mace ta jiÉ“anci yin matsi da ruwan dumi mai kauri na gishiri to lallai zata sha mamakin irin yadda zata magance matsalolin da take fuskanta a gabanta. Gishiri da kuke ji da gani yana Æ™arawa mace ni'ima. Yawan shan ruwansa zai saukar miki da yalwar flora a gabanki. 

Menene flora a jikin mace? 

Flora shine wannan ruwan da zaki ga yana fitowa a gabanki wanda zaisa gabanki ya kasance cikin danshi kusan ko yaushe. Wannan danshin na flora alama ce babba dake nuna cewa ke É—in kina da ni'ima. Tare da haka kuma, wannan flora É—in zata riÆ™a taimakawa wurin yi miki kariya daga wasu infections É—in. Zuwa yanzu nasan kun fahimci irin muhimmancin rubutun nan a gareku, har ila yau dai ku biyo ni a sannu domin jin yadda zaku yi matsi da kanunfari. 

Matsi Da Gishiri 

Zaki samu gishiri ki jika shi ya jiku sai ki samu É“aure ko nace arabic gum ki cakwuÉ—e shi da wannan jikakken gishirin. Idan kika haÉ—asu kika cakwuÉ—asu sosai, sai ki samu zumar ki farar saÆ™a, a duk lokacin da zakiyi amfani da wannan haÉ—in ki zuba babban cokali biyu ki juyata da wannan haÉ—in jikakken gishirin da arabic gum. Idan haÉ—in nan ya haÉ—u sosai za kiga yayi danÆ™o sosai to haka dama akeso yayi. Lakata zaki riÆ™ayi kina shafawa a gabanki, amma ki lura da lokacin daya kamata ki riÆ™a shafa shi a gabanki. 

Lokacin daya dace shine awa É—aya zuwa biyu kafin kiyi wanka, sannan kuma zaki iya applying wannan gagarumin haÉ—in ki kwanta dashi, dakin tashi daga bacci sai ki wanke. 

Wannan haÉ—in dana gama bayanin sa a sama "manta uwa" kenan. Idan baki sanshi ba to yau kin samu labarinsa, kuma ina mai baki shawarar lallai ki hanzarta zuwa ki haÉ—a shi, ki kuma jarraba amfani dashi. Wannan haÉ—in haÉ—ine na gaske indai ta É“angaren matsi ne. Idan kika juri shafa shi a gabanki zaki sha mamakin yadda zaki koma ki haÉ—e gam gam. 

Hulba da Gishiri 

Shin ko kin san cewa yin haÉ—in gishiri da hulba na Æ™arawa mace ni'ima ta Æ™ololuwa kuwa? To ga haÉ—in, "Ki samu gishirin ki da hulbar ki sai kisa a mazubi ki jiÆ™a su. Bayan sun tsumu sai ki na É—iban ruwansu kina sa zuma a ciki kina sha. Hakan zai Æ™ara miki ni'ima kwarai da gaske. 

Shin ko kin san cewa gishiri ba iya matsin gaba ake yi da shi ba? 

To in baki sani ba ana amfani da shi wurin ciko gaba.

Ta yaya ake yi? Ga bayanin nan kasa.

Domin ciko gaba da gishiri, sai ki samu gishiri ki yayyafa masa ruwa sama-sama, sai ki samu garwashi ki kai daki, ki debo gishirin nan idan ya bushe nan ki zuba akan garwashin. Daga nan sai ki tsugunna a kan hayakin.

Kamar yadda aka shaida mana, yana maganin warin gaba da matsin gaba.

Kuma shan gishiri [in an jiƙa shi] yana sa gaban mace ya ciko, sannan yana maganin sanyi.

Amfanin Tsarki da Gishiri

Ana yawan samun mutane waÉ—anda ke yin tambaya game da tsarki da gishiri, shin ko menene amfaninsa?

Tabbas in dai tambayarki kenan, to yau nazo miki da cikakkiyar amsa.

Ruwan gishiri ana yin tsarki da shi ne domin magance infection na mata. Da fari dai za ki samu gishirinki da ganyen magarya sai ki zuba su a mazubi, ki kawo ruwa ki zuba musu, sai ki barsu su yi kamar [ko fiye da] sa'a ɗaya ma'ana dai awa ɗaya. Bayan lokacin ya cika, sai ki ɗebi ruwan ki rinƙa tsarki da shi, in son samu ne ki yini kina yi.

Kuma ba sau É—aya za kiyi ki dena ba, ki cigaba har sai kin tabbatar kin rabu da infection É—in.

Wannan shi ne amfanin tsarki da gishiri. Da fatan kun amfana da wallafawar nan tamu.

Mata ku jiÉ“anci amfani da ruwan gishiri zaku sha mamaki 

A karanta a fahimta sosai sannan a aikata shi a aikace domin neman yayewar matsalolin gaba da neman ni'ima. 

Post a Comment

0 Comments