Yadda ake matsi da bagaruwa

Yadda ake matsi da bagaruwa 

Garin ƴaƴan bagaruwa

Garin kanunfari

Ganyen magarya

Miski

Yadda za’a haɗa

Zaki samu waɗannan kayan haɗin sai ki haɗe su guri ɗaya ki tafasa ki tace ruwan ki zuba miski ki ɗinga zama a cikin ruwan.

Yaya za mu yi amfani da bagaruwa da lalle don yin matsi?

Da farko dai ina son na baiwa mata shawara kan sanin abinda ya kamata su ɗinga yi a lokacin da suka ji labarin ana yin amfani da abu kaza don magance abu kaza, yana da kyau idan kuka ji irin wannan labarin ku ɗinga tuntuɓar masana don baku shawara ko kuma sanar daku yadda ake yi idan ya tabbata ana yi. 

Matsi da lalle da bagaruwa

Wani bincike ya bayyana cewa ana yin amfani da garin bagaruwa don matsi, bagaruwa na ɗauke da sinadaran dake taimakawa tsuke farjin mace. Wannan yasa suke tunanin tafasa garin bagaruwa da zama a cikinsa na tsawon lokaci na taimakawa matse gaba. 

Shima garin lalle ana yinsa ne daga ganyen lalle, shi dai galibi an fi yin amfani dashi don yin ƙunshi ko gyaran gashi, da canja launin gashi. Akwai bayanai daga wajen likitoci kan ko lalle yana matse gaban mace ko inganta lafiyar farji. Yin amfani da lalle don yin matsi kan iya tsuke farji.

Don haka bincike ya nuna ana yin matsi da lalle da bagaruwa. Saboda haka ina tunasar daku duk abinda kukaji ance yana matsi kafin ku yi shi yana da kyau ku tuntuɓi masana don jin shawarari akai, hakan zai taimaka muku. Ina fatan wannan bayanan za su gamsar daku musamman wanda ke son yin matsi da lalle da bagaruwa. 

Bagaruwa

Lalle

Da farko uwargida zaki haɗe kayayyakin nan kayan gaba ɗaya ki dafa idan suka dahu ki tace ki saka Zuma da mazarkwaila asha hmmm zakisha mamaki yadda ni'imarki zata sauka sosai.

Ana dafa ta da ganyen magarya ko ita kadai a rika wanke gaba dashi ko ki zuba a baho ki zauna a ciki da ɗumin kaman 30mins a kalla sau biyu a sati.

Akwai matsi wanda ake yinsa don mace farjinta ya tsuke ya zama a matse shi kuma wannan babu meyi sai wacce farjinta ya buɗe ko dalilin haihuwa ko kuma anyi mata fyaɗe ma'ana wacce ta rasa budurcinta to ita za tayi na tsuke farji to amma wasu ƴanmata suna kuskure wajen yin tsarki da ruwan bagaruwa da kuma matsi me matse gaban mace bayan suna da budurcinsu to

irin sune bayan anyi aure za kaga mijinta ya kasa shigarta da wuri saboda ƙofar ta matse da yawa wasu sai sunyi wata ɗaya ko biyu suna fama ga zafin da mace za taji idan suna jimai.

Sannan akwai matsi da ake yinsa don mace ta ƙara ɗanɗano wajen jima'i wato saka me gida kukan daɗi shi kuma wannan kowacce mace zata yi shi budurwa ko matar aure sai dai akwai sharaɗi dole sai farjinki ya zama a tsaftace kina tsarki da ruwan ɗumi lokacin da kika gama al'ada kuma kiyi da ruwan ɗumin da ganyen magarya a ciki sannan dama kina da sabulu na musamman wanda aka tanade shi don wanke farji domin ba aso mace ta rinƙa wanke gabanta da sabulun wanka sannan abinda zaki saka ya zama  yana da inganci ba komai kika ji labarinsa ki saka ba. Wato ita mace idan har zata iya kiyaye tsaftar gabanta babu ruwanta da saka abu wanda zai ƙara mata daɗi saboda da yawa shigar kwayoyin

cuta ne suke kashe gaban mace take zama babu ɗanɗano.

Sai kuma matsi wanda akeyin sa don magance cututtukan gaban mace kamar a saka garin hulba a cikin ruwan ɗumi a rinƙa zama a ciki da dai sauran hanyoyi da mace za tabi don ta kiyaye lafiyar gabanta..

A taƙaice dai kafin kiyi matsi dole sai kinsan matsayinsa a wajenki ta hakane zaki gane dacewar sa a wajenki sau da dama mata kuskure sukeyi wajen saka abu a gabansu kuma wani lokacin shine yakeyin musabbabin faruwar infection bazaiyu dama kina da matsala a gabanki ko kuma bakya gyarashi sosai kuma kice dole sai kinyi matsi donki ki ƙara ɗanɗano ko ki mallake miji ba wannan matsala zai ƙara jefa ki ko kuma kice dole sai kin matse kin dawo kamar budurwa..

Rashin iya matsi shi zaisa kaga wata matar bakin farjinta ya matse amma kuma cikin a buɗe saiya zama mijinta idan zai sadu da ita zaiji kamar ya saka azzakarinsa a cikin tulu wato ya shiga da kyar amma ciki kuma a buɗe haka kuma wasu matan suna shan wahala wajen neman maganin ni'ima amma shiru babu alamarta saboda basu gyara wajen da zai tara ni'imar ba mata a kiyaye irin wannan.

Yadda ake matsi da bagaruwa
Yadda ake matsi da bagaruwa.

FARJI BUƊAƊƊE MAI WARI

Wasu matan idan ana jima’i dasu sai kaji bakinsu na fitarda wani wari wari, kuma kaji gindin ya buɗe da yawa.

Kisamo waɗannan abubuwa kamar haka

1. Ganyan magarya

2. Ganyen bagaruwa

Sai ki niƙe su ki jiƙa su da ruwa ɗan kaɗan, sai kimatse lemon tsami guda 1 a ciki ki sanya ɗan sabulun salo kaɗan aciki sai kisamo ƴar auduga ko tsumma mai kyau mai laushi ki tsomashi ciki ki ɗinga goge farjinki dashi. 

Idan aka samu mace mai zafin gaba, ko namiji, wanda zaisa inya kusanci mace sai taji kamar gishiri

ko barkono taji mara na ciwo sai ta rasa ya za tayi to don magance. Wannan matsala sai a samu.

Bagaruwa

Kwa kwa

Dabino

Sai a markaɗa su da abun markaɗawa sai a saka shi inda zai yi sanyi sai a rinƙa sha a daddare zai ƙara sinadarai masu lafiya a jiki sannan kuma yana karawa mace daɗi.

DAN GYARAN GABAN MACEN DA TA HAIHU

Wannan wani bayani ne mai muhimmanci musamman ga matar data haihu take son gyaran jikinta da kuma matsewar jikinta ko gabanta cikin sauƙi, sannan kuma zai kame jijiyoyin da suka saki, kuma yana maido da martabar ‘ƴa mace kuma gaskiya wannan haɗi ne mai ban mamaki yanda za’ayi shine sai a samu.

Lemun tsami

Ƴaƴan bagaruwa

Gishiri

Sallaja

CIWON MARAN NA MATA

Ga matar da take fama da ciwon mara musamman lokacin al’ada, ko idan zai zo yana zuwa da ciwon mara, wata ma za kuga har tana birgima a ƙasa, ko taji kamar ana soka mata wuƙa, ko rikicewar haila, ko jinin ya rinƙa zuwa da wari, ko ƙarni, ko baƙi, ko yana zuba sosai to sai a samu:

Bagaruwa

Rumzali na asali

Lemun tsami

Sai ruwa lita biyar (5lrt)

Sai a dafasu a rinƙa sha ƙaramin kofi sau biyu (2) a rana za'a samu nasara.

DOMIN TSAFTACE MAHAIFA

Ga mai buƙatar tsaftace mahaifarta da kuma karramata da kashe duk cuta ko kwayar cuta dake zama bakin mahaifa, to wannan haɗin da zanyi bayani yana da muhimmanci musamman ga mai zafin mahaifa, ko kuma yara suna mutuwa a ciki, ko mai fama da toshewar bakin mahaifa ko kuma matsalar ta faru ne sakamakon amfani da waɗansu

magunguna na hana ɗaukar ciki ba bisa ƙa’ida ba, ko shan wasu miyagun kwayoyi, ko kuma yawan zubar da ciki, kuma hakan yana iya faruwa idan aka samu mace mai yawan bin maza, hakan zai iya haifar da kamuwa da manyan cututtukan da zasu iya lalata mahaifar.

Bagaruwa

Ganyen gwaiba

Ganyen lemun tsami

Garin rumzali

Na’a na’a

Kanunfari rabin gwangwani

Da ruwa lita biyar(5lt)

Sai a haɗa su wuri ɗaya a dafa su, sai a tace idan antace sai a rinƙa shan ƙaramin kofi sau biyu a rana safe da yamma, zai wanke mahaifa da tsaftaceta da kuma kashe duk wata kwayar cuta da zata iya shiga cikin mahaifa ta kawo illa ga lafiyarki.

Post a Comment

0 Comments