Yadda ake kwanciya da mace a daren farko

Yadda ake kwanciya da mace a daren farko

Kai daga jin wannan batun kasan da amarya ake. Ah! To wacece ake kwanciyar farko da ita idan ba amarya ba? Ai dai ko bazawara mai rai da lafiya ka samo ka aura to dai a wannan daren naku na farko a matsayin amarya take, idan kun isa kuce ba haka ba.

A saboda haka kamar yadda aka taɓa wallafa muku irin abubuwan da amarya zata yi domin tarbar angonta a daren farko, to haka yake a wurin ango ma. Ango yana da irin tanadin da zaiyi domin tarbar amaryarsa a daren su na farko.

Idan kai ɗin ka zamo ɗaya daga cikin masu son angwancewa da amaryarka, koma ka riga da ka angwance ɗin amma kana shirin ƙara angwancewa to duk dai ire iren ku wannan rubutun naku ne, domin ku na zauna na rubuta shi. Ku biyo ni a sannu domin jin irin abinda kuke buƙata a yayin da daren angwancin naku yake gabatowa.

Ya kai ango ko magidancin da zai ƙara aure ina kira gareku da kusan cewa kamar yadda kuke gani, kuma kamar yadda kuka sani mata suna da hidindimu da suke yi a yayin da bikin aure ya gabato, ina nufin hidindimu da suka haɗa da kwalliyar jiki da gyaran amare irin wanda zaku ga sunayi da kuma duk wani abu da za'a yiwa amarya a gidansu duk dominka ne ango, kuma nasan kasan hakan ne.

Yadda ake kwanciya da mace a daren farko
Yadda ake kwanciya da mace a daren farko

Duk irin waɗannan hidindimun ana yin sune domin a kankarowa amarya mutunci da ƴancinta a wurinka, haka kuma anayi ne domin a fita haƙƙin ka ta hanyar gyara maka amarya ciki da wajenta domin jin daɗin harƙalla. To fa kamar haka ne kaima daga gareka, akwai buƙatar kai ma ka yiwa amaryarka irin naka tanadin domin kankarowa kanka mutunci a shimfiɗa, tare da haka kuma ka sauke haƙƙin dake kanka wanda yake nata ne, a wurin auratayya ta shimfiɗar aure.

Duk wani ango mai lafiya wanda yayi auren son ransa, kai koma dai tilasta masa auren akayi indai shi ɗin mai lafiya ne kamar yadda na ambata, to a yayin da ƙurar biki ta lafa aka ɗauko lafiyayyar amaryarsa daga gidansu aka kawo masa ita muhallin daya tanadar mata na zaman wannan auren, to fa abu na gaba da zai fuskanta ba komai bane illa yadda zai kasance da ita amaryar tasa a wurin shimfiɗa, watau jima'i ko saduwa.

Ina kira a gareka ya kai ango, kar wannan mararin da shauƙin yadda zaka kasance da tsaleliyar amaryarka yasa ka mance da wasu abubuwa masu muhimmanci, waɗanda sune matakin farko da zasu sa ka samu rayuwar auratayya mai daɗi daga tarawar farko har zuwa ƙarshen rayuwar auren naku indai ta fannin jima'i ne.

Waɗannan abubuwan da nake ƙoƙarin hasaso maka ya kai ango sun haɗa da;

-Gyaran jiki

-Ƙamshi

-Inganta lafiyarka ta ɗa namiji

-Nazarin wasannin soyayya da kuma salo salo na kwanciyar aure

-Kalamai

Waɗannan abubuwan dana lissafo a sama, sune ire iren abubuwan da zaka tsaya tsayin daka domin ganin ka gabatar dasu kafin wannan daren da kake marari, haɗe da zakwaɗin sa, wanda a cikinsa ne kake fatan shan romon amaryar taka. Zan ɗauke su ɗaya bayan ɗaya domin yin bayanai a kansu ta yadda zaku fi fahimtar karatun.

-Gyaran jiki

Gyaran jikinka a lokacin da auren naku ya gabato ya kai ango, ya ƙunshi aski, shaving ɗin gashin gaba dana hammata, da ƙara ƙaimi wurin gyara da tsaftace sauran sassan jiki musamman kula da lafiyar bakinka da kuma gyaran ƙafarka, a sannu zamu zo wurin da zan bayyana muku mai yasa nace wannan kula da lafiyar bakin da za'ayi da kuma gyaran ƙafa su ɗin na musamman ne.

-Ƙamshi

Kamar yadda na taɓa bayyanawa game da ƙamshin jikin amarya to kazalika kaima ango lallai ya kamata kasan cewa kana buƙatar ƙamshi a koda yaushe idan kana son kasancewar da zaku keyi da amaryarka ya riƙa yin armashi. Irin ƙamshin nan daka sabarwa hancinta dashi a lokacin da kake zuwa zance wurinta, to shi wannan yama fishi, saboda a wancan lokacin ita ɗin budurwarka ce, zance kake zuwa kawai, yanzu kuma amaryarka ce, saduwa ko kuma nace kwanciya zaka riƙa yi da ita, don haka ka tanadi ƙamshi mai ɗan karen daɗi a jikinka at all times.

-Inganta lafiyarka ta ɗa namiji

Kunga a wannan gaɓar lallai ne ango ya zama mai lissafi, watau ina nufin ango a ƙoƙarinsa na yiwa amaryarsa tanadi, dole ne ya riƙa samun cima irin wacce take ƙara inganta ƙarfin namiji (akwai rubuce rubuce da dama da mutum zai duba yayi nazarin irin wannan cimar musamman ƴaƴan itatuwa). Haka kuma kowane irin ango yasan kansa. Idan ka kasance cikin irin angwayen nan masu rauni ko matsakaicin ƙarfin gaba sai ka nemi irin magunguna na islamic chemist, na bature ko irinsu dauri watau haɗin gargajiya domin inganta kwazonka a yayin tarawa da amarya. 

Anan zanyi jan hankali kaɗan, kada kuji nace a nemo maganin ƙarfin mazakuta kuje kuyi ta bunkuɗawa kanku irin waɗannan magungunan fiye da ƙima. Yin hakan zai sa ka cutar da kanka ka kuma cutar da amaryar ka. Idan kaje kasha wani abin daya birkita ka, ka samu yarinyar mutane a daren farkonta kayi mata mummunan ta'adi to bada ni ba, kaga hanyata nan. Atoh! 

-Nazarin wasannin soyayya da kuma salo salo na kwanciyar aure

Munzo dai dai wurin yanzu. Karku manta gaba ɗaya wannan rubutun anyi shine domin karantar daku yadda Ake kwanciya da mace a daren farko. To ka sani ango, idan kazo angwancewa da amaryarka duk waɗannan abubuwan dana lissafo nayi bayani akansu kawo yanzu, sune abubuwan da zakayi applying kayi aiki dasu a dai dai wannan lokacin. Idan kayi gyaran jiki mai kyau irinsu shaving, ka kuma kula da lafiyar bakinka da kyau, to ina mai tabbatar maka, ba kai bama, ita kanta amarya za taji daɗin irin salo salo na kiss da zaka riƙa mata. Kamar yadda na bayyana maka, dama ka tanadi ƙamshinka wanda shine zai ƙara sururuta maka ita ta shigo hannunka yadda kake so, bayan ka ruɗa sassan jikinta da irin kalolin wasannin soyyayar da nace maka lallai ka nazarta. Idan kayi duk wannan to babu abinda ya rage maka sai saduwa da ita. 

Ango kar ka manta ita ɗin amarya ce, ƙila ma yarinya ce ƙarama, ƴar sha bakwai ko sha takwas kayi mata wayo kayi wuff da ita, to ai kuwa ko don haka ka tausayawa yarinyar mutane ka bita sannu a hankali. Ka daure ka bita a hankali ka shigeta da kaɗan kaɗan, idan ma kaga irin amaren nan ne masu raki ko kuma irin yaran nan ne waɗanda suke gabansu a matse ko a tsuke yake sosai, to karka ce zaka afka mata gaba ɗaya ka fasa ta a wannan daren, haba malam ! Easy, ka buɗe ta da kaɗan kaɗan tunda dai ta riga ta zama taka, abin ba guduwa zaiyi ba. 

-Kalamai

Ko shakka babu kai ango akwai buƙatar kayi nazarin kalamai masu taushi da zasu ke daɗaɗawa amarya haɗe da kwantar mata da hankali. Kana buƙatar irin waɗannan kalaman soyayyar ta fuska biyu. Na farko dai zaka keyi mata kalaman soyayya na yabo da fasa mata kai, tare da haka kuma duk a cikin irin wannan kalaman kayi amfani dasu ta yadda zata samu sakar maka jikinta. Fuska ta biyu kuwa lallai ka tanadi kalaman rarrashi waɗanda za kayi amfani dasu bayan ka ɓarje guminka a shimfiɗa. Ma'ana bayan ka sadu ko nace bayan kayi jima'i da amaryarka. 

Wannan kenan!

Post a Comment

0 Comments