Yadda ake gane sha'awar mace ta tashi
Shin kunsan alamomin yadda ake gane sha'awar mace ta tashi?
Abu ne mai sauƙi fuskantar sha'awar mace ta motsa musamman lokacin da take buƙatar namiji ya sadu da ita.
Sai dai yana da muhimmanci ku gane cewa kowane mutum yana da bambanci kunsan kowace mace da salon irin nata yadda take nuna alamu a lokacin da sha'awar ta ke motsawa.
Amma duk da haka masana ilimin jima'i sun bayyana wasu alamomi na gama gari kan yadda ake gane mace idan tana cikin sha'awar jima'i. Idan kuka karanta wannan darasin za ku ji su.
Amma dai kafin nan idan kuna tare dani zan fara yin bayani akan sassan jiki ko kuma wuraren da ake tsokano sha'awar mace a jikinta domin saurin fahimtar alamomin da ita macen zata nuna idan sha'awar tata tazo.
Sassan jiki ko wuraren tado da sha'awar mace
Da wuya kaji ma'aurata suna zancen wadannan wuraren a yayin da suke zancen motsa sha'awa.
WaÉ—annan wuraren, wurare ne dake motsa wa mata sha'awar su da zaran anyi hakan yadda ya dace.
WaÉ—annan wuraren sun haÉ—a da;
Kai
Shafa kan mace a lokacin wasannin motsa sha'awa abu ne da yake motsa mata sha'awar ta nan take.
Shi yasa maza suke son mace mai gashi, baya ga ƙarin kyau da yake yiwa mata, maza suna son suga suna wasa da gashin matansu a lokutan soyayya.
Sai dai abun takaici ba duk ma'aurata bane suka san hakan kuma suke amfani da hakan ba.
Haɓa
Nan ma waje ne da muddin za a yi wa mace wasa da shi nan take za a motsa mata sha'awar ta.
Mata suna son jin mazansu na shafa musu haɓarsu wajen fuskarsu cikin sanyin rai haɗe da soyayya. Nan take za a ga mace ta soma lumshe idanuwa.
Ƙirji
Shima wuri ne dake motsa sha'awa amma ma'aurata suna watsi da shi.
Tsakiyar ƙirjin mace tsakanin nonuwanta waje ne shima dake motsawa mata sha'awar su.
Kada ka taɓa mata nonuwa. Kawai shafa mata nan ka kura mata idanuwa za ka ga halin da ka tsomata.
Hammata
Nan ma lungune da yake da saurin motsa sha'awa da ma'aurata suke burus da shi.
Hammata mai gashi ko marashi waje ne da idan aka yiwa mace wasa da shi ta hanyar shafa wuje ko lasa nan take yake motsa mata sha'awa.
Tafukan hannu
Ma'aurata bama sa É—aukansa a matsayin wajen dake cikin jerin wuraren da suke motsawa mutum sha'awa.
Yin wasa da tafukan hannun ta musamman ma idan aka shafawa tafin hannun man shafawa mai kamshi da santsi.
Ƙasan cibiya
Duk mutumin da za a taɓa masa ƙasan cibiyarsa da manufa na soyayya sai sha'awar sa ta motsa.
Waje ne da yake da saurin aika saƙon sha'awa ga wanda ake da niyar motsa masa. Don haka ma'aurata su kasance suna amfani da wannan wurin domin motsawa juna sha'awa.
Ƙugu
Shima wajen da yake motsawa mutum sha'awa amma sam ma'aurata hankalinsu baya zuwa nan.
A lokacin da ma'aurata suka rungumi juna, su kasa yatsansu a ramin ƙugun juna musamman babban yatsa suna shafawa wajen kamar ana tausa. Nan take zasu ji sha'awar su ya motsa.
WaÉ—annan suna cikin jerin wasu abubuwan dake saurin motsawa mutum sha'awar sa da akasarin ma'aurata basu cika amfani dasu ba a lokutan su na soyayya.
Sai dai ba ana nufin kowa aka masa wasa da waÉ—annan wuraren zai ji ya motsu ba. Abunda zai iya motsawa wani sha'awar sa wani kuwa kashe masa sha'awar zai yi.
Don haka ma'aurata sai suyi la'akari da wanne yake motsasu kamin suyi amfani da shi.
kowace mace da salon irin yadda take nuna alamu a lokacin da sha'awar ta ke motsawa.
Yadda Ake gane sha'awar mace ta tashi
Kallon Namiji
Idan mace na cikin sha'awa zaka ga tana kallon namiji sosai, za ta ƙura masa ido ba tare da ta ɗauke ba musamman idan irin namijin da take so ne. Irin kallon da za ta yiwa namiji a lokacin da sha'awar ta ke motsawa ba irin kallo bane da aka saba yi koda yaushe ba.
Yanayin Yadda Take Wasa Da Jikinta
Yadda mace ke yin wasa da jikinta idan tana sha'awa ya sha bamban da sauran lokutan, misali za kaga tana yin wasa da gashin kanta, tauna leɓenta, ko rungumar wani abu mai laushi.
Yanayin Murya
Idan kaji mace muryarta ta canja ba yadda aka saba jinta a koda yaushe ba kuma babu wani ciwo ko rashin lafiya a tare da ita alamu ne dake nuna sha'awarta ta mosta, a cewar binciken.
Yanayin Saka Kaya (Dressing)
Yana daga cikin yadda zaka gane sha'awar mace ta tashi idan ta saka kaya masu nuna surar jikinta ba tare da jin kunya ba kuma ba'a saba ganin tana yin hakan ba.
-Wawan Zama
Ka lura ka kuma kula da kyau, idan har mace ta motsa to bata da damuwa don tayi wawan zama a gabanka. Wannan wawan zaman da zata riƙayi a gabanka da saninta ko babu duk bashine a lissafin nata ba, abinda kawai take so take kuma muradi shine samunka a bisa shimfiɗarku, don haka wawan zama na ɗaya daga cikin alamomin farko da zaka fara ganewa daga macen da sha'awarta ta taso.
-Ta hanyar yawan raɓar namiji;
Yawan kai kanta inda namiji yake sau tari kuma da taɓa shi tana kai hannunta jikinsa. Wannan shine babban makamin mace ta wannan sigar domin ai tasan zaiyi wahala namijin yayi resisting ɗinta idan ana samun body contact a tsakaninsu. Saboda haka ta yadda yarinya zata riƙa taɓa namiji, ku sani tsananin sha'awarsa ce zata kawo dalilin hakan, domin idan ba ita ba, to ba koda yaushe bane zata riƙa taɓa jikinka ba. Wasu lokuta mata kan yi wuya su bayyana ra'ayoyinsu, kamar yadda na bayyana a baya, saboda haka a matsayinta na mace, tana tunanin cewa ikon da take da shi shine jikinta, kuma shine makaminta na cimma wannan manufar.
Yadda ake gane sha'awar mace ta tashi post Conti..
-Miƙa A Gabanka;
Ita dama miƙa idan kaga anyi ta to mafi akasari tanayin nuni ne da abubuwa guda biyu; na farko shine sagewar gaɓoɓin jikin mutum, wanda mutum zai riƙa jin jikinsa a daɗɗaure duk ba daɗi har ya kaiga sai mutum ya mimmiƙe gaɓoɓin jikinsa sun amsa sannan ya samu nutsuwa. Idan kaga mace ta cika yin miƙa a gabanka to ba gaɓɓanta ne sukayi sanyi ba, a'a kawai dai tana buƙatar kaci tane. Za kaga tana yin miƙa tana banƙaro ƙirjinta a gabanka, da zarar kaga hakan to da walakin!
-Yadda take kallonka akai-akai
Ka lura da yadda take kallonka a koda yaushe, bari in gaya maka wani abu idan kana burgeta, to ka sani kullum zata riƙa kallonka da tsokana. Don haka idan matarka ko yarinyar da kake nema tana yin haka to ka sani cewa tana sonka kuma tana son yin wani abu da kai. "alamun mace tana sha'awarka da jima'i, irin kallon da zata riƙa aiko maka dashi yasha bambam da ragowar kallon data saba yi maka, kai kanka idan ta fara yi maka irin wannan kallon dolene zaka ankara cewar akwai wani abu.
-Kullum zata so yin magana da kai.
Wani abu game da mata shine yana da wuya su ɓoyewa sarrafa yadda suke ji ga wani. Don haka idan ka lura cewa yarinyar koyaushe tana son tattaunawa ko tattauna wani abu da kai, ko da baka da abin da zaka ce mata, za tayi ƙoƙarin neman wani batu ko wani abu don kawai ta tattauna da kai. Don haka kar kayi tunanin tana yin haka don yin magana kawai don ba haka bane. Akwai dalilinta, kuma ɗaya daga cikin manyan dalilan nata shine sha'awarka.
-Yabon ka akai-akai.
Idan mace tana sha'awar ka tana kuma son kaci ta, zata iya tabbatar da yabon ka a kowace rana. Galibi, ƴan mata basa karimci wajen yaba wa wasu. Duk da haka, idan ta kasance tana yabon ka akai-akai, to tabbas ta kai ƙololuwa ne, akwai wani abu fiye da hakan. Sha'awarka da take yi shine dalilin yaba maka da zata keyi a koda yaushe. Komai kayi burge ta kakeyi idan kana magana birgeta zakayi, haka nan yanayin shigarka ma yana burgeta, don haka akwai sha'awarka a zuciyarta idan har kana samun yabonta sosai.
-Yawan tambaya da maida hankali akan yanayin halittar jikinka
Kullum zata so ƙarin bayani harma ta riƙa yi maka tambayoyi akan wasu abubuwan game da halittar jikinka, misali idan mace ce wacce saje ko ƙasumba suke burgeta to za kaga tana yawan yi maka magana a kansu idan kana da saje ko ƙasumba. Idan kuwa bata son ka ko sha'awarka to duk ba zaka ga hakan daga gareta ba. Idan ka lura za kaga cewa irin wannan zantuttukan ko tambayoyin suna da nauyi idan har tana jin kunyarka to amma ƙarfin sha'awar da take yi maka shine ya danne kunyarka har take iya yi maka zance irin wannan.
Yi maka murmushi akai-akai.
Idan tana kallonka kullum tana murmushi? Ko kuwa tana murmushi idan kuna magana da ita? Duk waÉ—annan hanyoyi ne, kuma tana tunanin hakan zai sa ka fahimce ta da kuma hanyar da zata gaya maka ka sami Æ´anci da kwanciyar hankali da ita. Babu wani abu da zai iya motsa mata murmushi duk lokacin data ganka inba soyayya da sha'awarka ba, don haka ka daina tambayarta ko tana son ka a lokacin da ta riga ta nuna maka alamun murmushinta.
Za taso ta zauna kusa da kai
Idan kun kasance tare, tana ƙoƙarin zama kusa dakai a kowane lokaci? Sannan dole ne ka fahimci cewa babu wani abu da zai sa tayi duk abin da ba soyayya ba.
Za ta so samun hankalin ka
a duk lokacin da kuke tare da ita, tana neman hanyoyin da zata bi don samun hankalin ku? Shin har yanzu tana yin abubuwan da zasu sa ka lura da kasancewarta a kusa da kai? Hakan ya nuna tana so, kuma ita ma tana sha'awar samun wani abu da za kayi da ita. Domin idan bata son zama da kai, ba zata nemi abin da zai ja hankalinka gare ta ba. "alamun mace tana sha'awarka ta jima'i."
Za taso ziyartar wuraren da kake zuwa
Idan ka lura cewa kullum tana zuwa wurin daza kaje, ko kuma har yanzu tana son halartar duk wani taron taron da zaka halarta. Ko kuma ace tana duk inda kaje. Hakanan alama ce mai kyau don sanar da kai cewa wannan matar tana sha'awar ka ko kuma tana son yin wani abu da kai.
Yana da muhimmanci ku gane cewa wadannan alamomin ba lallai bane a same su daga wajen kowace mace ba. Domin kamar yadda na bayyana tun a farko kowace mace da irin nata salon don wasu matan ma ko mazajensu basu san yadda ake gane sha'awar matansu ta mosta ba don babu wasu alamu da suke nunawa.
0 Comments