Matsi da kanunfari

 Yadda ake matsi da kanunfari 

Menene kanunfari?

"Kanunfari dai sinadari [ɗan itace] ne da ake amfani da shi a abinci don ya ƙansasa shi, ana daka yaji da shi don ya ƙansasa shi, ana saka wa a shayi don ya kansasa shi, sannan ana mahadi [ko] maganin sanyi da shi hadi da saka shi a sauran abinci."

A dunÆ™ule dai Kanunfari yana É—aya daga cikin irin Æ´aÆ´an icen nan da ake kira" Spice".. Watau dai, masu Æ™arawa abinci Æ™amshi ko É—anÉ—ano. 

Amfanin Kanunfari

Likitoci sun tabbatar da cewa kanunfari na da matuƙar amfani ga ɗan adam. Bugu-da-ƙari, yana motsa sha'awa, yana ƙara wa maza lafiyar mazakuta da ƙarfin ta, eh kuji ni da kyau, wannan na ɗaya daga cikin sirrikan kanunfari, yana inganta lafiyar maniyyin namiji haɗe da inganta kwararar jini zuwa ga mazakutar namiji.

Bafa a iya nan amfanin kanunfari ya ƙare ko ya tsaya a jikin ɗan adam ba, a'a, akwai ƙarin alfanunsa.

Kanunfari Æ™unshe yake da sindarin dake yaÆ™i da cututtuka da bunÆ™asa garkuwar jiki. White blood cells, watau wasu kwayoyin halittu dake da alhakin yaÆ™i da cututtuka a jikin É—an adam suna Æ™ara Æ™arfi ne sosai idan mutum ya jiÉ“anci amfani da kanunfari. A riÆ™e wannan. 

Shan ruwan kanunfari kuwa yana taimakawa kwarai wurin narkar da abinci cikin sauri da daƙile cutar ulcer.

Ga maza da mata waɗanda ke fama da matsalar ƙiba da teɓa, to shan ruwan kanunfari na bada muhimmiyar gudunmawa wurin rage ƙiba da teɓa ga mata da maza.

Matsi da kanunfari
Matsi da kanunfari post#

Shan ruwan kanunfari na yin maganin cutar kwalara, da jiri, da saisaita sukari a cikin jini, ga masu cutar sikari kenan, watau diabetes da kuma masu lafiyar ma, yana kuma tabbatar da lafiyar hanta.

Kanunfari na ƙara lafiyar ƙashi, da daƙile kamuwa da cutar sanƙarau ko ciwon cancer.

Haƙika amfanin kanunfari a jikin ɗan adam yana da matuƙar yawan da idan lissafi za'a yi, to sai ayi littafi guda a kansa. Anan dai zan tsaya a nan domin shiga wani babin.

Kanunfari na da matuƙar amfani ga mata. Shi yasa zai kyautu mace ta rinƙa shansa [ko da jifa-jifa ne] domin irin alfanun da yake da shi.

Daga cikin amfanin kanunfari ga mata akwai ƙarin ni'ima; duk macen data juri shan kanunfari [kada ta sha sama da itace huɗu kullum] to lallai zata yi ni'ima kuma maigida zai ji daɗin mu'amalar jima'i da ita.

Ga macen da kuma take fama da matsalar rashin kwakkwaran kwan haihuwa [wanda shi ke jawo rashin É—aukar ciki] to ta juri shan kanunfari kullum [kada ta sha sama da itace huÉ—u] idan ta dage sai a ga ta samu rabo.

Bugu-da-ƙari kanunfari na rage saurin tsufa. Kai yana ma taimakawa wurin rage ƙiba da ƙarin kuzarin mata yayin jima'i.

Ga macen da take fama da ciwon mara yayin jinin al'ada ko kuma kwanakin da take shafewa tana al'ada suke tsayi, to ta juri shan kanunfari domin yana rage tsayin kwanaki da ciwon mara yayin al'ada.

Har ila yau kada ku yi zaton shi amfanin kanunfari iya ga mata ya tsaya, a'a, har maza ma yana yi musu amfani.Yanzu zamu tsallaka zuwa babi na gaba.

Yadda ake matsi da kanunfari.

Idan mace ta jiÉ“anci yin matsi da kanunfari to lallai zata sha mamakin irin yadda zata magance matsalolin da take fuskanta a gabanta. Kanunfari ko ban faÉ—a ba sahihin maganin sanyi ne ga É—an adam. Mace kuwa ai Æ´ar adam ce. Mata kuji wannan batun da kyau, kanunfari da kuke ji da gani yana Æ™arawa mace ni'ima. Yawan shan ruwansa zai saukar miki da yalwar flora a gabanki. 

Menene flora a jikin mace? 

Flora shine wannan ruwan da zaki ga yana fitowa a gabanki wanda zaisa gabanki ya kasance cikin danshi kusan ko yaushe. Wannan danshin na flora alama ce babba dake nuna cewa ke É—in kina da ni'ima. Tare da haka kuma, wannan flora É—in zata riÆ™a taimakawa wurin yi miki kariya daga wasu infections É—in. Zuwa yanzu nasan kun fahimci irin muhimmancin rubutun nan a gareku, har ila yau dai ku biyo ni a sannu domin jin yadda zaku yi matsi da kanunfari. 

Matsi da kanunfari 

Zaki samu kaninfarinki ki dake shi yayi lukui sai ki samu É“aure ko nace arabic gum ki cakwuÉ—e shi da wannan dakakken kanunfarin. Idan kika haÉ—asu kika cakwuÉ—asu sosai, sai ki samu zumar ki farar saÆ™a, a duk lokacin da zakiyi amfani da wannan haÉ—in ki zuba babban cokali biyu ki juyata da wannan haÉ—in dakakken kanunfarin da arabic gum. Idan haÉ—in nan ya haÉ—u sosai za kiga yayi danÆ™o sosai to haka dama akeso yayi. Lakata zaki riÆ™ayi kina shafawa a gabanki, amma ki lura da lokacin daya kamata ki riÆ™a shafa shi a gabanki. 

Lokacin daya dace shine awa É—aya zuwa biyu kafin kiyi wanka, sannan kuma zaki iya applying wannan gagarumin haÉ—in ki kwanta dashi, dakin tashi daga bacci sai ki wanke. 

Wannan haÉ—in dana gama bayanin sa a sama "manta uwa" kenan. Idan baki sanshi ba to yau kin samu labarinsa, kuma ina mai baki shawarar lallai ki hanzarta zuwa ki haÉ—a shi, ki kuma jarraba amfani dashi. Wannan haÉ—in haÉ—ine na gaske indai ta É“angaren matsi ne. Idan kika juri shafa shi a gabanki zaki sha mamakin yadda zaki koma ki haÉ—e gam gam. 

Dabino da Kanunfari

Shin ko kin san cewa yin haÉ—in kanunfari da dabino na Æ™arawa mace ni'ima ta Æ™ololuwa kuwa? To ga haÉ—in, "Ki samu kanunfarinki da dabinonki sai kisa a mazubi ki jiÆ™a su. Bayan sun tsumu sai ki na É—iban ruwansu kina sa zuma a ciki kina sha. Hakan zai Æ™ara miki ni'ima kwarai da gaske. 

Shin ko kin san cewa kanunfari ba iya matsin gaba ake yi da shi ba? 

To in baki sani ba ana amfani da shi wurin ciko gaba.

Ta yaya ake yi? Ga bayanin nan kasa.

Domin ciko gaba da kanunfari, sai ki samu kanunfari ki kakkarya ko daka shi sama-sama, sai ki samu garwashi ki kai daki, ki debo kanunfarin nan ki zuba akan garwashin. Daga nan sai ki tsugunna a kan hayakin.

Kamar yadda aka shaida mana, yana maganin warin gaba da matsin gaba.

Kuma shan kanunfari [in an jiƙa shi] yana sa gaban mace ya ciko, sannan yana maganin sanyi.

Amfanin Tsarki da Kanunfari

Ana yawan samun mutane waÉ—anda ke yin tambaya game da tsarki da kanunfari, shin ko menene amfaninsa?

Tabbas in dai tambayarki kenan, to yau nazo miki da cikakkiyar amsa.

Ruwan kanunfari ana yin tsarki da shi ne domin magance infection na mata. Da fari dai za ki samu kanunfarinki da ganyen magarya sai ku zuba su a mazubi, ki kawo ruwa ki zuba musu, sai ki barsu su yi kamar [ko fiye da] sa'a ɗaya ma'ana dai awa ɗaya. Bayan lokacin ya cika, sai ki ɗebi ruwan ki rinƙa tsarki da shi, in son samu ne ki yini kina yi.

Kuma ba sau É—aya za kiyi ki dena ba, ki cigaba har sai kin tabbatar kin rabu da infection É—in.

Wannan shi ne amfanin tsarki da kanunfari. Da fatan kun amfana da wallafawar nan tamu.

Mata ku jiÉ“anci amfani da kanunfari zaku sha mamaki 

A karanta a fahimta sosai sannan a aikata shi a aikace domin neman yayewar matsalolin gaba da neman ni'ima. 

End#of matsi da kanunfari

Post a Comment

0 Comments