Hanyoyin samun ciki da wuri

 Hanyoyin samun ciki da wuri ga ma'aurata*

A yau darasin namu zaiyi duba ne akan abunda ya shafi haihuwa wato daga aure zuwa ɗaukan ciki har haifewa, A wannan darasin zanyi bayani dalla dalla domin kowa ya samu wayewa gameda wannan tsarin da yake shirye ga dan Adam.

Yadda Ake Ɗaukar Ciki:.

Ciki na haihuwa ya kasance shine cikamakin auratayya, wanda dashi ne ake cin ribar aure. Idan akayi aure tsakanin namiji da mace, to babu abinda yake fara zuwa tunanin ma'auratan nan irin samun ƙaruwa watau haihuwa. Wannan shine burin duk wasu ma'aurata, suyi aure su samu haihuwa su tara zuri'a, su bar baya. Idan ba'a samu ciki ba dole zaku ga an samu damuwa tun daga ɓangaren matar kanta har zuwa maigida tare da iyayensu da sauran ƴanuwa. 

Idan aka jira aka jira zuwa wani lokaci mai tsawo sai damuwa tayi yawa kuga an fara neman taimakon addu'o'i da magunguna, ga masu tawakkali kenan dom fai domin kuwa wasu ma zuciyar takanyi rauni har afara kauce hanya ana shiga yan tsubbu duk don neman haihuwa bayan fa duk ansan cewa bokaye basu zasu bada haihuwar nan ba. 

Yadda ake samun ciki shine hanyar saduwa tsakanin mace da miji wato waɗannan jinsi biyun su suke haɗuwa su samar da ciki ta

hanyar jima'i.

A yayinda mata da miji sukayi jima’i wannan maniyin dake fita daga jikin namiji wanda an tabbatar da cewa akan samu maniyyin da yawansu yakai miliyoyi wanda suke fita a lokacin da ɗa namiji yayi inzali amma sai dai kwaya ɗaya ne tak ke nasarar isowa cikin ovaries wato mahaifa inda ita kuma macen zata sako nata kwan wanda anan zasu haɗu, shi wannan maniyyin ne zai kyankyashe wannan kwan kuma hakan shine mafarin samun ciki.

Hanyoyin samun ciki da wuri:.

Ko akwai wasu dabaru da akeyi domin samun ciki da wuri saɓanin yadda kowa ke samu? amsar itace eh akwai dabaru sosai na kimiyya wanda idan mutum ya ɗaukesu yayi aiki dasu za'a iya dacewa cikin ƙanƙanin lokaci wanda a wannan gaɓar zanyi bayanin waɗannan hanyoyin idan kuka biyoni a sannu. 

Ku samu likita yaku ma'aurata masu neman haihuwa domin yayi muku duba da nazari akan sinadaran vitamins masu kawo ciki da kuma isasshen folic acid wanda wannan yanada tasiri sosai yana kare duk wani lahani dazai hana mace ɗaukan juna biyu. Folic acid yana daga cikin babban abunda ya zama mataki na farko na ɗaukar ciki ko rashin ɗaukar sa, saboda haka yanada kyau ayi binciken wannan folic acid ɗin da sauran sinadaran vitamins dashi likita zai iya yi muku bayani akansu.

Wannan shine matakin farko, a riƙe a kuma lura. 

A lokacin da jinin haila ya ɗaukewa mace yawanci akwai wani ruwa da zai riƙa biyo gabanta bayan tayi tsarki, wannan alama ce dake nuna wannan matar tana ovulation. Jinin da mace take fitarwa a yayin haila ba komai bane illa matattun kwan da maniyyin namiji bai kyankyashe ba a wannan lokacin. Ovulation kuwa yana nuna cewar matar nan ta samu sabbin kwayaye masu lafiya waɗanda suke buƙatar kwan namiji wato sperm ko maniyyinsa, yana nuna cewar kuma shima lokaci ne mafi dacewa da a riƙayin jima'i, saboda wannan lokaci ne da ake ɗaukar ciki da wuri saboda haka ne ma yasa ya kamata mace tasan lokacin da take jinin hailar ta.

Sannan akwai abubuwa da hanyoyi masu dama wanda mace zata auna ta gane lokacin da take al'ada ko kuma lokacin tsayawar al'adar tata, wanda wannan zai taimaka sosai wurin samun ciki saboda haka ya kamata ace kafin ayiwa yarinya aure a nuna mata yadda zata kula da jinin ta.

Zama kan gado bayan an gama jima’i shima wannan wata babbar hanya ce dake taimakawa wajen samun ciki da wuri, ana buƙatar bayan jima'i abin nufi namiji da mace sun kammala jima’i kenan, anaso su bada ratar minti sha biyar zuwa ashirin kamar haka domin miniyyi ya ƙarasa ya kuma sauka zuwa mahaifa.

Hanyoyin samun ciki da wuri
Hanyoyin samun ciki da wuri

Kada ku zama masu yawan yin jima'i domin neman haihuwa, yawan yin jima’i bashine zaisa mace ta ɗauki ciki ba, abunda ake buƙata shine a riƙa samun tazara koda na kwana ɗaya ne saboda a bincike maniyyi yakan kai kwana biyar bayan fitarsa daga jikin namiji, kafin ya gama ƙarasawa mahaifa ya kuma haɗu da kwan mahaifa take note!

Ma’aurata duka biyu anaso su rage damuwa ko wannensu ya rage damuwa da tunani saboda hakan yakanyi tasiri sosai wurin samun juna biyu, saboda haka a lokacin da kuke jima’i domin samun juna biyu kuyi ƙoƙari ku cire damuwa a ranku domin shine yafi.

Samun lafiya anan ana buƙatar daga kai har matarka ku kasance masu motsa jiki kada ku riƙa zama haka kawai babu motsa jiki. Cimar ku ta kasance mai kyau kuma ku jiɓanci cin kayayyakin ƙaro ni'ima a yayin jima'i. Akwai rubuce rubuce da akayi akan wannan, zaku iya dubuwa ku karanta domin fahimtar duk wani nau'in kayan cima dazai iya taimaka muku wurin ƙarin ƙarfin gaba da juriyar kwanciya a ɓangaren namiji kenan da kuma ƙarin ni'ima a ɓangaren mace. 

Hanyar samun ciki da wuri da magani

Shin ko akwai magani da ake sha domin samun juna biyu, amsar itace eh akwai irin magunguna da suke tallafawa mace idan tasha bayan anyi jima'i, su ire iren magungunan nan zasu taimaka wurin ɗaukar cikinta kuma za suke taimakawa wurin kare lafiyar cikin a farkon samuwarsa. Bugu da ƙari kuma yawanci ire iren magungunan nan, supplements ne watau dai suna maye gurbin irin nau'in abincin da mutum ya rasa a jikinsa. Suna da muhimmanci sosai. A tuntuɓi likita domin shi ko ita ne wanda zasu iya yi muku cikakken bincike ko bayani a game da hakan. 

Sannan kuma akwai magani na bature dake aiki ta sigar ƙara ƙarfi, inganci da yawan maniyyi saboda shima ƙarancin maniyyi da rashin ingancinsa shima yakan hana samun juna biyu saboda haka idan kasan cewa ba kada ƙarfin azzakari ko kana inzali da wuri ko kuma ka fahimci cewa kana da tsinkakken maniyyi to lallai ina baka shawara ka rika shan maganin bature na ƙarfin maza wanda hakan zai taimaka maka sosai wurin fitarda ruwan maniyyin nan mai yawa da inganci. Amma a kula banda sha da yawa watau ina nufin banda overdose. Overdose din magani bashi zai baka guarantee nayin aikin da akeso maganin yayi ba. 

Ba kuma lallai sai maganin bature ne kawai zai baka abinda kake buƙatar samu ba. Akwai haɗe haɗe da za'a iya yi a gida ana gwadawa kamar haka;

Da farko za'a samu ƙaro/arabic gum

sai a niƙashi kamar gari sai a riƙa zuba chokali biyu a baki ana binshi da ruwa haka za'a riƙa yi safe, rana da yamma. Wannan namiji da mace duka zasu riƙa shan sa. 

Sannan kuma a tafasa ƙaro sai a ɗebo ruwan zafi a riƙa shiga cikin ruwan ɗumi dashi. Wannan na mace ne kawai. Sannan kafin ta kwanta barci ta jiƙa ƙaron ta riƙa shafawa a al'aurarta ta kwanta dashi wannan magani ne mai kyau. 

Matsalar haihuwa ɓangaren maza

Za a samu abarba/pineapple

Sai a samu madarar saniya kindirmo ko tsala duk wanda aka samu

Sai a markaɗa abarba a tabbata ta markaɗu sannan a haɗa ta da madarar saniya a riƙa sha kofi ɗaya safe da yamma.

A karanta a fahimta sai a aikata a aikace! 

#end

Post a Comment

0 Comments