Hanyoyin sace zuciyar budurwa

 Hanyoyin sace zuciyar budurwa

Wani kyakkyawan saurayi daga cikin masu ziyartar wannan gida namu na kayan marmari, ya tura mana saƙo akan mu taimaka masa da hanyoyin daya kamata yabi domin sace zuciyar budurwarsa, saboda miƙa girmamawarmu ga ma'abota ziyartar wannan shafi namu, shine muka yi nazari sannan muka gudanar da bincike mai zurfi akan wasu abubuwa daya kamata kabi domin sace zuciyar budurwa.

Kamar yadda kowane namiji yake son mace dason yin rayuwa da ita, haka suma matan suke, wato abun alfahari ne a nuna wane ace ai saurayin wance ne. Nima inason budurwata yadda ya kamata shiyasa ma nake yi mata hidima daidai gwargwado.

Hanyoyin sace zuciyar budurwa
Hanyoyin sace zuciyar budurwa post#

Maza ayi hattara sosai wajen sanin wacce zaka yi hulÉ—ar soyayya da ita, haka zalika kema yan'mata ki kula da kanki yadda ya kamata saboda samarin shaho.

Ta yaya zan sace zuciyar budurwa?

A gaskiya sace zuciyar mace abu ne mai sauƙi ga wanda yasan hannunsa sannan kuma abu ne mai matuƙar wuya ga wanda bai gane ba. Tabbas idan har kana so ka yiwa mace satar zuciya to dole ne sai kabi waɗannan abubuwa da zamu jero, ko kuma har dama ƙarin wasu hanyoyin.

Wasu daga hanyoyin sace zuciyar budurwa.

1. Jan aji

2. Haƙuri

3. Gaskiya

4. Kulawa

5. Rarrashi.

1. Jan aji: ka sani fa cewa mace ba zata iya mallaka maka kanta ba haka nan, dole ne saita ja maka aji dan ta gane halayenka da kuma yanayin haƙurinka sannan kuma zata so ta gane shin da gaske ne kake sonta ko kuma da wata manufar ne. Saboda mata sun tsani duk saurayin dake shirin yaudaransu, idan har kaga ka zowa mace kai tsaye ta amince da kai ba tareda jan aji ba, to fa a gaskiya ka tsoraci lamarinta domin mace idan har cikakkiya kuma gogaggiyar mace ce to zata ja maka aji yadda ya kamata har saika kusan yin kuka tukunna zata karɓeka.

2. Haƙuri: Tabbas dole ne saika zamo mai haƙuri idan ba haka ba, ba zaka samu damar lashe jarabawar da mace zata yi maka ba, saboda za kaga abubuwa da dama masu gasa zuciya, idan har baka zamo mai haƙuri ba, to kai dayin soyayya da mace sai dai a hankali...

 3. Gaskiya: mace tanason saurayin dake faÉ—a mata gaskiya kai tsaye, idan har ya kasance kai maÆ™aryaci ne to ina mai tabbatar maka da cewa idan tazo ta gane sirrinka zaka sha mamaki, dan haka ake kwatanta gaskiya dai-dai gwargwado. 

4. Kulawa: kulawa tana É—aya daga cikin hanyoyin sace zuciyar budurwa, dole ne idan dai har kanason zamanka da mace ya É—auki lokaci mai tsawo kuma yasa ta soka sosai fiye da kima to kuwa dolene sai ka kula da ita tamkar yanda zaka kula da kanka a lokacin da kake cikin rashin lafiya kai fiye da haka ma. Kulawa yana É—aya daga cikin siffofin abinda mata suke matuÆ™ar so. 

5. Rarrashi tareda girmama mace tana so idan har ka sanyata yin fushi saboda wani dalili to ka rarrasheta tamkar ka samu jaririya. Kuma budurwa zata ji daÉ—i sosai fiye da kima idan dai har kana girmamata kamar yadda take yima, kamar ta fannin yabon halayenta na kirki tareda nuna mata cewa babu wanda kafi so a wannan duniya sama da ita saboda tana da halin kirki. 

Har ila yau wasu daga cikin hanyoyin sace zuciyar budurwa akwai. 

#Iya zance

#Nemanta a ko yaushe

#San kasancewa da ita.

Post a Comment

0 Comments