Alamomin mace mai ciki

Alamomin mace mai dadi article post 

Shin waɗanne alamomi ne na shigar ciki gamida alamomin da mace zata ji ko ta gani a tattare da ita idan tana ɗauke da sabon ciki ta yadda za ta gane tun kafin ta ziyarci asibiti.

A rubutuna na yau zanyi magana ne akan wasu alamomi harda siffofin mace mai ciki, mata iyayenmu a koda yaushe muna girmama ku iya iyawarmu Allah ya ƙara muku lafiya da nisan kwana.

A binciken dana gudanar kafin wannan rubutu ya tabbatar mini da cewa ba kowace mace bace a cikin matan hausawa ta kwana da sanin babban abinda ke kawo ɓatan wata wato wanda muka fi sani da samun juna biyu ba saboda irin yawan tambayoyin da muke samu daga wurare daban-daban. 

Alamomin mace mai ciki
Alamomin mace mai ciki post#

Ayi cewa bawai iya juna biyu bane ke kawo ɓatan wata hadama wasu cutukan na iya shigar mace wanda ke ɗauke da ƙwayoyin saka rashin lafiya a cikin mahaifa, a yawancin lokuta ma sune kan gaba wajen kawo batan watan mata wato rashin ganin period, ko kuma muce rikicewar lissafin wata.

Har ila yau baya ga cututtuka akwai sauran abubuwan dake kawo ɓatan wata, waɗanda suka haɗa da;

1. Shayarwa

2. Yawan damuwa ko ciwon damuwa

3. Rashin zama wuri ɗaya

4. Rashin samun hutu yadda ya kamata, kamar masu wasanni mai tsanani

5. Shan magunguna barkatai walau na asibiti ko na gida.

1. Mace mai shayarwa: Shayarwa shine bayar wa jariri sabon haihuwa ko wanda ya kwana ruwan nonon mama. A wasu lokuta yakan kasancewa matan da suke shayarwa basa samun ɓatan wata, amma akwai matan da suke samun ɓatan wata lokacin da suke shayarwa kinga wannan ba kai tsaye za'a ce tana ɗauke da juna biyu ba. Saboda wasu dalilai zai iya kasancewa tanada ɗauke ciki ya danganta da sanin data yiwa kanta.

2. Yar uwa kiyi sani cewa bawai iya ɗaukar ciki ko cuta ke iya kawo ɓatan wata ba, domin kar ya kasance kina budurwa kiga bakya jinin al'ada ki shiga fargaba, wadannan yan damuwa dake cikin rai sukan iya kawo hakan, musamman idan ya kasance kin shiga matsanancin damuwa. Sai a kiyaye domin ta wannan bangare ba damuwa a rayuwa tanada illoli marasa adadi.

3. Rashin zama waje ɗaya agun mata wato gantali bakyanan bakya can, wanda hakan yana wahalar da jikinki da kuma wasu halittu dake jikin mace wanda ke buƙatar hutu, yanada kyau a matsayinki na mace ki kula da kanki da lafiyarki domin inganta jindaɗi da walwalarki.

4. Wasanni sunada matuƙar amfani ga lafiyar mace fa yawaita wasannin bashi da amfani, musamman wasanni masu tsanani domin sukan iya kawo ɓatan wata harma da samun cututtuka marasa ma'ana. idan zakiyi wasa ki yishi saffa-saffa wato tsaka tsakiya. 

5. Shaye shayen magunguna ba tareda izinin likita ba yakan taɓa lafiyar jiki har ya kasance mace ta samu ɓatan wata, a koda yaushe ki kasance mai bin umarnin likita wajen amfani da magunguna musamman na mata masu ƙarin ni'ima domin wasu sunada illa ga lafiya. Ta fannin magungunan gargajiya shima haka yake domin shan irin magunguna kwata-kwata bashi da amfani bawai ina nufin maganin gargajiya baya aiki bane a'a saidai a kiyaye sosai wajen amfani dasu. 

Menene zai tabbatar da kasantuwar ciki a jikin mace.

Akwai waɗansu alamu wanda mace mai juna biyu za taji a jikinta ko a halayenta dake tabbatar da juna biyu ne a tareda ita. Ga wasu daga cikinsu nan a ƙasa.

#.A watannin farko na alamomin mace mai ciki shine zata yi ɓatan wata, bayan yan satuttuka kuma sai ta fara samun👇

1. Tashin zuciya da sassafe harda amai a wasu lokutan, koda ma ya kasance bata ci komai ba

2. Saurin gajiya, da zarar anyi wani ɗan aiki ko kuma ta dinga jin jiri (dizziness) idan tazo miƙewa

3. Yawan zubar da miyau sakamakon tashin zuciya

4. Zazzaɓi mai zafi

5. Rashin son ƙamshin turare ga wasu matan.

A wane lokaci ya kamata ayi gwajin juna biyu.

Lokaci mafi muhimmanci daya kamata aje gwajin ciki shine lokacin da kika fara jin wasu daga cikin alamomin da muka bayyana a sama.

Idan anje domin gwajin ciki kuma ya kamata a tabbatar ta hanyar auna fitsari, sannan kuma sai ayi hoton ciki wato scanning, idan ma cikin ne to ta hanyar hoton cikin sauƙi za'a tabbatar a cikin mahaifa yake ba'a wajenta ba wato (ectopic pregnancy).

A watannin da cikinki ya fara tsufa kuma, wato yakai kamar wata 3, akan ga alamun mai ciki kamar haka: 

1. Girman ciki ya bayyana a zahiri wato kina ɗauke da ciki 

2. Yawan zuwa fitsari ko zaryar yin fitsari, saboda abin dake ciki ya soma danne mafitsara

3. A wasu matan kuma akan samu ciwon baya

4. Ciwon ƙirji ko zafin ƙahon zuci ko ƙwarnafi saboda (acidity solutions) din ciki na tasowa mata zuwa ƙirji.

5. Sai kuma a soma samun duhu haka a  fuskar mace da fitowar zane zane a fatar ciki, da buɗewar hanci a wasu matan ma da nauyi ko kuma ciwon nonuwa. 

Ba dole bane kowace mace ta samu dukkan abubuwan da muka lissafa, amma kusan akasarin mata suna samun a kalla rabin waɗannan alamun, mun gode.

Post a Comment

0 Comments