Yadda ake ma saurayi shagwaba

Yadda ake ma saurayi shagwaba complete

Matan wannan zamani sun ƙware wajen yadda ake ma saurayi shagwaba musamman idan ya kasance saurayin yana son budurwar sosai. Akwai hanyoyi ba adadi wanda zaki iya yiwa saurayi ko nace sahibinki hakan a sauwaƙe tareda bashi nishaɗi. 

Yana da matuƙar muhimmanci kisan dai dai lokacin da yake farinciki da kuma akasin hakan yayin yin shagwaɓar saboda hakan zai matuƙar ƙara shaƙuwa a tsakaninku. Domin sanin yadda ake ma saurayi shagwaba don sashi farinciki, ki karanta waɗannan dabaru nawa taƙaice.

menene shagwaɓa a soyayya

Shagwaɓa a soyayya tana da matuƙar amfani sosai domin tana ƙara shaƙuwa da danƙon soyayya a tsakanin masoya biyu. Shagwaɓa a soyayya yana nufin yin abubuwa cikin iyawa da jan jiki a wajen mace domin janyo hankalin saurayinta domin ya ƙaro tsantsar kulawarsa gareta a daidai lokacin da take yin shagwaɓar Tata, wannan sabon lamari tsakanin masoya yana ƙara shaƙuwar soyayyarsu. 

Matsawar a soyayya akwai shagwaɓa tsakanin masoya biyu, to koda ace masoyan najin kunyar juna, shagwaɓa dake tsakaninsu zai saka har su iya gaya wa juna sirrinkansu a sauƙaƙe. Kuma mafi yawancin yan-mata a yanzu suna yawan yiwa samarinsu shagwaɓa dan su gane irin soyayyar da suke musu, kuma suna samun nasarar akan hakan.

Abin ban sha'awa gameda shagwaɓa shine idan kin san wata baki san wata ba. Mata sunada salo salo daban daban nayin shagwaɓa ga samarinsu a kowane lokaci. Yanzu har takai in mace nasan abu wajen saurayinta kafin ta samu abun saita masa shagwaɓa, abun mamaki kuma shine sai kaga saurayi ya bayar ba tareda yasan ya bayar ba. 

Yadda ake ma saurayi shagwaba
Yadda ake ma saurayi shagwaba post#

Wasu mazajen ma gani suke idan budurwa batasan yadda ake ma saurayi shagwaba ba, to hakan na nuna cewa bata sonshi ko kaɗan. Idan akwai shagwaɓa, to akwai yarda da ƙara ƙaunar juna sa'anan kuma akwai nishaɗi da farinciki. Mafi yawancin lokuta idan samari na cikin damuwa ko ɓacin rai samun shagwaɓa daga wajen abun ƙaunarsu na iya kawar da wannan halin da suke ciki. 

Amfanin yadda ake ma saurayi shagwaba ga budurwa ga saurayinta

Meyasa muke da gaske gameda rashin zama da gaske? dalili shine, dariya tana da daɗi, kuma dariya tareda wani ya mafi daɗi. Muna so mu kasance tareda mutanen da zasu iya samu dariyar farinciki, musamman ma idan zasu iya taimaka mana muyi dariya gameda abubuwa da yanayin dake samu damuwa. 

Daga cikin amfanin shagwaɓa agun budurwa zuwa ga saurayinta , akwai abubuwa haka:

shagwaɓar budurwa na sanya zuciyar saurayi ta narke, yaji babu abinda yake so ya gani sai masoyiyarsa.

shagwaɓar budurwa tana ƙara shigar da zuciyar saurayinta a duk lokaci da hankalinsa ya tuna masa da ita sai yaji wani daɗi a cikin ransa

shagwaɓar budurwa har ila-yau tana taimakawa wajen amincewa tsakanin masoya. Sanadiyar shagwaɓa kuma sai masoya suji sun yarda da kansu sosai. 

Amfanin shagwaɓar mace ga saurayinta akwai kawar da zargi. Idan soyayya ta kasance cewa akwai shagwaɓa sosai daga ɓangaren budurwar to hakan yana kau da tunanin saurayin daga zargin budurwar tasa ta wani abun dabai kamata ba a cikin soyayyarsu.

shagwaɓar a wajen budurwa tana haifar da gaskiya, amana, kawaici, yarda, nuna soyayya ta haƙiƙa, sadaukar da_ rai ko jiki_, zaman daɗi da kuma rashin son kai.

Ita shagwaɓar budurwa tana sanya kusanci tsakaninta da sahibinta, a ƙullum shi saurayin yanason yaga masoyiyarsa tareda shi. Zai ji baya jin daɗi idan babu ita a kusa dashi.

Salon yadda ake ma saurayi shagwaɓa:

Bayan sanin amfanin ita kanta shagwaɓa da mece ce ita, yanzu kuma zamu duba izuwa yadda akeyin shagwaɓar wato salon yadda ake ma saurayi shagwaba a aikace a soyayya.

Akwai hanyoyi da dama da mace zata iya yiwa saurayinta shagwaɓa amma a wannan rubutu nawa, zanyi dubi zuwa ga salon shagwaɓa a soyayya guda goma sha daya (11).

_____________________

1. Ki bashi suna mai ban dariya:

Samari na matuƙar son suji budurwa tana kiransu da wani suna sabo wanda ba'a taɓa kiransu dashi ba. Wannan salon shagwaɓar yafi aiki yadda ya kamata a sanda kikeson saurayinki ya miki abinda kike ganin zaiyi matuƙar wahala a wajenshi. 

Idan kika kira saurayinki da suna mai ban dariya, hakan zai saka dukanku farin ciki harma yayi miki abu fiye da yadda kike tunanin zaeyi. Saboda haka yanada matuƙar amfani kisan yadda akema saurayi shagwaɓa. 

Kafin hakan, ki kwantar da hankalinki sosai kisan irin abubuwan da yake so, daga-nan ne za kiyi iya sanin sunan da zaki saka masa. Misali idan mutum ne mai san kwallo, sai ki kirashi da sunan dan ƙwallon da yake so, daga nan sai ki nuna mai kina kishi da hakan a cikin shagwaɓa.

_____________________

2. Ki ɗauki hoto mai ban dariya ki nuna mishi:

Ɗaukar hoto mai ban dariya kamar selfi haka ki nuna wa saurayinki musamman inya bukaci ki turo masa hotunanki itama wata salon shagwaɓarce wanda ke ƙara shaƙuwa tsakanin masoya. idan yadda ake ma saurayi shagwaɓa shine muradinki ta fari, kibi wannan hanyar domin tanada sauƙi. 

In saurayi yaga hotanki mai ban dariya, hakan zai sashi ya fara miki dariya kuma hakan zai sashi cikin farinciki musamman in kin tambayeshi in hoton yayi kyau, komai ya faɗa a lokacin zai  sa ki gane matsayinki a wurinshi. Idan ma kin nuna mai ɓacin rai, sai kiga ya lallaɓeki kamar ƙwai tunda farincikin ki itace muradinsa a koda-yaushe.

____________________

3. Ki zama mai yawan yi masa bazata:

Ga sirri gareku yan-mata, idan kina son sanin halin saurayinki, ki zama mai yawan yi masa bazata. Kamar kice fito ina anguwarku, gani a kofar gidanku. Idan akwai abinda yake ɓoye miki to bazai fito ba. Amma inya fito, mai gaskiyane shi. 

Yima saurayinki bazata wani salone na shagwaɓa wanda zaki gane idan saurayinki ya dace ko kuma bai dace ba. bazata itace hanya mafi sauƙi ta gasgata maganarsa. Amma kuma idan hakan zakiyi, yanada kyau kisan yadda zaki kula da al'amarin. 

______________________

4. Ki ɗauki abubuwa masu muhimmanci kamar basu dashi:

Yan-mata adon gari, farincikin ku muradin samarinku, ɓacin ranku damuwa ce. Wata kalar sabuwar salon shagwaɓa ce ɗaukar abubuwa masu muhimmanci kamar basu dashi. Nuna shagwaɓa ta wannan sigar nasa ki gane matsayinki a wajen masoyinki. 

In dai yana sonki har zuciyarsa, kome kikayi a wurinshi itace dai-dai. Misali ace zaku fita shopping ko wajen shakatawa haka yace maki karfe 3, sai yazo ƙarfe 3 kice masa kefa kwalliya kike ya bari sai karfe 4, kinga shagwaɓar tasa makullin soyayyarsa ta dawo hannunki sai yadda kika juyashi. 

Dama kuwa mulki a soyayya, mace aka sani a matsayin sarauniya kuma komai ta yanke ya zauna.

_____________________ 

5. Kisa ya fara yaƙin kaska  a lokacin da baya so

yana daga salo na yadda ake ma saurayi shagwaba idan kina tareda saurayinkinki dinga yin abubuwa waɗanda zai kara kusanci a tsakaninku to sune abubuwan da zaki ringa masa. Wata salon shagwaɓar ce fara masa da wasa ta yaƙin kaska. 

Wani lokacin za kiga kuna magana da saurayinki amma kiga magana ta ƙare a bakinsa ya rasa me zai fada, kema haka ta bangarenki kin rasa abun cewa. Zaku iya samun abun magana akai idan yaƙin kaska ta shigo tsakanin ku. In hakan ta faru, zaki iya kawo wata maganar da zaisa ku fara gardama. 

Kuma baida wani zaɓi wanda ya wuce abinda kika zaɓa. Zaki iya ɗaukar abu kisa masa a gefen kunne ko kuma a saman hularsa kice bake kikayi hakan ba. A zahirance yasan kece, amma soboda yasan shagwaɓa kikeyi masa sai yace miki ya yarda da hakan. Hakan nada matuƙar nishaɗantuwa.

_____________________

6. Ki dinga masa wasa da abinci:

A wasu lokutan idan kun ɗan fita wajen cin abinci, za kiga mafi yawanci shi zai riƙa saka maki abincin a baki, amma a zuciyarsa shima yana son hakan. Idan kika ɗebo abincin zaki sa masa a baki, da zarar ya buɗe bakinsa sai kiyi maza ki ɗauke cokalin ki cinye kuma kisa shi yasa miki a baki. 

Sai dai kuma ba dukkan maza akema shagwaɓa ta wannan sigar ba, saidai in mace ce wacce tasan hannunta sosai.

_____________________

7. Ki saka ya biyo ki ta hanyar ɗaukar abunsa:

Wannan ma yana daga cikin yadda ake ma saurayi shagwaba. Zaki iya yiwa saurayinki shagwaɓa ta hanyar ɗaukar masa abu kamar in kun fita shaƙatawa kodai kuna tare a wani waje na masoya. In kinaso kuɗanyi wasa amma yaƙi, sai ki ɗauki wani abu nasa ki gudu kisa shi ya taso har ya biki. 

Da kinyi gudu kaɗan sai kice masa ƙafafuwanki da hannayenki na miki ciwo. Kinga yasan bada gaske bane, amma zai faɗa maki kalamai masu ɗaɗi da zasu faranta miki rai, kawai dan yaga kina cikin farinciki in kuna tare.

____________________

8. Ki katse shi a yayin da hankalinsa baya tare dake:

A mafiya yawancin lokuta, za kiga saurayi yaje gurin budurwa amma sai kiga hankalinsa baya tareda ita, kuma hakan na matuƙar ɓata rai. In saurayinki ya miki hakan, ta hanyar shagwaɓa ce kawai zaki iya kar kato tunaninsa. 

Misali ki soma yi masa kuka (amma fa na wasa) kinga ai zai fara lallasanki yana tambayanki meyasa kike kuka, a hakan kinyi nasarar karkato da tunaninsa gareki.

_____________________

9. Ki zama budurwa mai kishi:

Ana yawan cewa mata sunfi samari kishi, amma gaskiyar magana itace maza sun fi mata kishi sai-dai su basu cika nunawa a fili ba. Maza na matuƙar son suga budurwarsu tana nuna kishi akansu, kuma suna kiran hakan da shagwaɓa.

______________________

10. Nuna halinki na musamman:

Shima yana daga cikin yadda ake ma saurayi shagwaba ki nuna masa wani hali naki na musamman, mafi yawancin lokuta, saurayi sai ya ringa cewa yafi budurwarshi wani abun, kuma hakan baya yi mata daɗi. Amma daga sanda suka nuna masa irin sabon abu haka wanda bai sani ba, sai kiji shi yana cewa ashe dama yarinyar nan ta iya shagwaɓa haka. 

Misali kamar ace kullum sai yace kin cika iya yi kamar wata yar ƙauye amma kuma hakan wasa ne a wurinshi, to ke kuma sai kiyi masa hali irin na yan ƙauye wanda zai gane cewa ke ɗin ta daban ce. Ki nuna mai ubangijin daya halicce ki ya baki baiwa yayin abubuwa daban-daban a lokuta daban.

______________________

11. Yin mai magana da lafazin waje:

In kina ma saurayinki magana da lafazin waje, hakan na janyo farinciki da nishaɗi idan kuna tare. Kinga in kika fara magana ta lafazin waje dariya zai fara miki yace biki iya ba. 

Kuma sai kice masa kinyi magana dan yace kin iya kuma shine zai ce baki iya _ba. Sai yayi murmushi ya kalleki ya fara maki daɗin baki. Hakan na yiwuwa ne kawai idan shagwaɓa ya shiga tsakanin masoya biyun.

Post a Comment

0 Comments