Maganin girman nono na budurwa

Maganin girman nono na budurwa

Nonon mace ya kasance wani asset, kadara kenan a gareta, duk macen da bata gyara nononta to fa tana yiwa kanta ta'adi ne, ba kuma zata gane hakan ba sai lokacin da tayi sakacin kula dasu har suka kai ga zubewa suka kwanta kamar silifas. 

Yake É—iya mace nonuwanki martabarki ne. Kuma kowace mace da irin tata baiwar nonon, kar kice ko kiyi tunanin ni nonuwana Æ™anana ne ko kuma kiyi tunanin ke kinyi aure ai yanzu shayarwa kikeyi ke babu ruwanki da wani gyaran nono, tunani irin wannan ba Æ™aramin kuskure bane. Ki riÆ™a gyara nonon ki wanda ya kasance wata ni'ima ce a gareki. 

Ire irenku masu ganin cewa Æ™irjinku bashi da girma bari kusha wani abun da zai sa Æ™irjinku ya cika, kuna nan da yawa na sani, amma duk ku dakata ku bani hankulanku, kuji ni da kyau; halittarku ta mata tana gama cika ne a dakunan mazajen ku, saboda haka idan kuka bi a sannu ko baku sha komai ba, zaku samo wannan girman nonon ne da kuma cikarsa ne a hannun mazajenku bayan kun shiga dakunan ku. 

Idan kika je kina shan magunguna na Æ™arin cikar nonuwanki ranar duk da nonuwanki suka cigaba da girma saboda taÉ“awar da mijinki yake musu, tofa saurin zubewa zasuyi. Wannan shine matsalar don haka ku gane kuma ku kiyaye. 

Yake É—iya mace gyara da kula da nonuwanki wajibi ne a gareki, abin nufi abu ne wanda yake dole, tilas ne. Nonuwanki suna daga cikin martabarki na budurwa ko kuma diya mace. Ki kula da nonuwanki sune fitulinki. Yaku mata da kunsan yadda maza suke son nono da kunfi kula da nonuwan naku fiye da yadda kuke yi a yanzu. Kamar dai yacce nake yawan faÉ—a nono shine kadararki ta farko akan idon É—a namiji.

Da farko dai kafin komai dolene ki kiyaye lafiyar nononki musamman a yanayin kwanciya. Kwanciyar rub da ciki ba taki bace indai kina son nonuwanki suyi karko kuma suyi inganci. A iyakar sanina babu macen da zata so nonuwanta su zube su kwanta kamar silifas duk da dai yau da gobe bata barin komai, sannan ko babu komai akwai tsufa. Amma idan ana kiyayewa sai kiga nonon naki ya jima kafin ki daina cin gajiyar wannan kadarar ta nononki a wurin maigida.

Maganin girman nono na budurwa
Maganin girman nono na budurwa

Abu na biyu, dole ne ki kiyayewa yin É—aurin Æ™irji. ÆŠaurin Æ™irji shima ba naki bane matuÆ™ar kin É—aura É—amarar kula da nononki. 

Idan kina da aure kuma ke mai jego ce nasan zakiyi goyo, to amma a goyon ma akwai irin abubuwan daza ki kiyaye ki kuma kula dasu duk a domin kiyaye lafiya da martarbar nonuwan naki. Ki riÆ™a sassauta goyon kuma karki riÆ™a barin goyon nan na tsahon lokaci musamman ma idan babyn naki yayi bacci sai ki sauke goyon ki kwantar dashi. 

Babban jan hankali anan shine; idan ku Æ´anmata ne ko kuma ke budurwace, ina nufin ke mai karanta wannan bayanin, ki sani cewa shan kwayoyin bature ko kuma wasu magungunan domin Æ™ara miki cika da girman nono, to kibi sannu a hankali, kar kiyi garaje domin hausawa suna cewa 'garin neman gira akan rasa ido kuma a wata faÉ—ar suka sake cewa zafin nema baya kawo samu. To kamar hakane akanki Æ´anmata ko Æ´ar budurwa. 

Ire irenku masu ganin cewa Æ™irjinku bashi da girma bari kusha wani abun da zai sa Æ™irjinku ya cika, kuna nan da yawa na sani, amma duk ku dakata ku bani hankulanku, kuji ni da kyau;  halittarku ta mata tana gama cika ne a dakunan mazajen ku, saboda haka idan kuka bi a sannu ko baku sha komai ba, zaku samo wannan girman nonon ne da kuma cikarsa ne a hannun mazajenku bayan kun shiga dakunan ku. 

Idan kika je kina shan magunguna na Æ™arin cikar nonuwanki ranar duk da nonuwanki suka cigaba da girma saboda taÉ“awar da mijinki yake musu, tofa saurin zubewa zasuyi. Wannan shine matsalar don haka ku gane kuma ku kiyaye. 

Ki sani a wasanni da duk abinda miji zaiyi da Æ™irjinki, ko da baki É—auki cikinsa ba dole zaki ga chanji a nonuwanki saboda zasu riÆ™a cika suna Æ™ara girma bayan wani lokaci idan yana taÉ“a su. Saboda haka yake budurwa, kifi maida hankali akan lafiya da kuma gyaran nonuwanki ba Æ™arin girmansu ba yayin da kike budurwa. 

Akwai mata Æ™alilan waÉ—anda ba lallai nonuwansu suyi girma ba koda sun haÉ—u da namiji, irin matan nan sune suke da buÆ™atar yin amfani da magunguna domin neman cikar Æ™irji, suma kuma É—in sai bayan sunyi auren ne zasu gane hakan. 

Tare da haka kuma har ila yau akwai wani abun lura daya rage mana guda É—aya wanda za'ayi magana akansa kafin a fara bayanin hanyoyin gyaran nono. Abin lura anan kuwa shine ba'a so mace ta riÆ™a saka riga ko bra wacce ta matseta sosai saboda haka zai riÆ™a danne glands É—in nonuwa, kuma daga waÉ—annan glands É—in sunyi weak to dole nono zai faÉ—i. Yana kuma saka jijiyoyin jikin nono suyi sanyi su saki, a irin hakane nono yake zubewa. Domin haka yaku Æ´anmata ko budurwar dake tare dani anan, ku riÆ™a sanya bra wacce take da faÉ—in hannu da baya saboda tafi balance kuma tafi support. 

Hanyoyin gyaran nonon budurwa.

Hanya ta farko

Waken suya

RiÉ—i 

Aya 

A samu waken suya a gyara shi a cire dattin cikinsa sannan a saka a wuta a soya. Ya zama suyar sama-sama kuma waken suyar kaÉ—ai kar asaka mai, Idan akaji ya fara Æ™amshi sai a sauke. Sannan a samu riÉ—i shima a soya sama sama a sauke, idan duka soyayyun waken suya da riÉ—in nan suka bushe sai a daka su. Kullum da safe sai a É—iba, wannan dakakken waken suyar a zuba a ruwan zafi a sha, sannan a samu kunun aya mai kyau a zuba garin riÉ—in nan shima asha sau uku a rana. 

Wancan na waken suya sau ɗaya za'a sha da safe kafin aci komai, na riɗi da kunun aya kuma sau uku, sannan a riƙa shafa man riɗin akan mama.

Wannan watau wani haÉ—i ne na bayyana muku shi yanzun nan, kuma shi É—in na musamman ne, domin duk abubuwan da aka lissafa muku tun daga; waken suya, riÉ—i, aya dashi kansa man riÉ—in sune abincin nono. Saboda haka za kiga yadda nonuwanki zasu ciko su riÆ™a cika Æ™irjinki da rigarki taf kamar yadda kike so kuma ba tare da kinsha wani maganin bature ko wani wanda zaiyi miki illa a gaba ba. Haka kuma jikinki zaiyi kyau sannan kuma ga ni'ima nasha-nasha. 

Hanya ta biyu 

Lalle na gargajiya 

Bagaruwa ta hausa

Garin habbatus sauda

Garin hulba 

A É—ebi kowanne cikin babban cokali sannan a zuba ruwa iya yadda zai isheki ki zauna a cikin sa. Sai ki dafa ruwan sannan ki bari yasha iska yadda zaki iya zama a ciki, sai ki tace shi a baho sannan ki shiga ciki ki zauna ya shiga jikin ki sosai, bayan kuma kin fito daga tsumuwar nan da kikayi sai ki samo man tafarnuwa ki haÉ—a da farin miski, kisa auduga a ciki sai ki cire kiyi tsome in ya kai tsahon awa É—aya sai ki cire. Kiyi wannan kwana biyar jere da juna babu fashi. Idan kika jure kikayi babu fashi to la budda babu makawa zaki bawa wasu labarin irin nasarorin da kika samu. 

Hanya ta uku 

Ki samu kankana guda É—aya, kwakwa guda É—aya da dabino kofi É—aya, sai ki yanka kankana da wannan gwandar gaba É—ayansu ki zuba su a guri É—aya, daga nana sai ki cire duk kwallayen dabinon nan ki wankesu suma ki zuba, sai ki samu wani abu mai Æ™arfi kamar ludayin Æ™arfe kiyi ta juyasu har sai kankanar nan ta zama ruwa, sai a rufe a saka a cikin fridge ya kwana. Idan ya kwana da safe sai a É—auko a saka madarar ruwa gwangwani É—aya da zuma daidai yadda ake so, daga nan kuma sai ayi blending yayi laushi. Idan yayi kauri za'a iya Æ™ara ruwa, sai a wuni ana shansa. 

Wannan haÉ—in yana saukar da ruwa a nono sannan ya cika taf ya kuma tsaya a tsaye gwanin sha'awa. Abi duk bayanin da akayi a sama ayi su daki daki, za'aga abun mamaki.

Hanya ta hudu

Dabino 

Madarar shanu 

Kaninfari (gari) 

Kirfa 

Za'a fara shanya dabino ya bushe sai a cire kwallon a daka shi ya daku sai a haÉ—eshi da garin kaninfari da kuma kirfa a cakwuÉ—a su, sai a riÆ™a zuba cokali uku ana haÉ—awa da madarar shanu, ana sha safe da yamma cokali uku uku kullum tsahon mako É—aya. 

Wannan haÉ—in zaisa su ciko idan sun yamushe. Zasu tsaya su cika suyi É“ul É“ul ko ina taf taf, ya gyaru yayi kyau da inganci. 

Hanya ta biyar:

Abubuwan da za'a nema;

Albasa

Zuma

Garin gero

Madara Peak.

A Samu albasa a yankata sannan a dafa ta har sai ruwan yayi baki sai a sauke a zuba zuma ludayi ɗaya da garin gero ludayi daya sannan a zuba madarar peak sai a riƙa sha da ɗumi har kwana sha tara(19).

Kar kuji Ina ta maganar nono nono. Nono yana da matuÆ™ar taka rawa wajan sha’anin zamantakewar ma'aurata musamman a wajan maigida, Domin yana cikin abun da ke jan hankalin É—a namiji a jikin mace.

Hanya ta shida

A samu;

gero

alkama

jar masara

farar shinkafa

Sai a gyara a hadasu a wanke a shanyasu a rana su bushe sai a soya sama sama, sai a juye a kai niÆ™a, gaba É—aya sai a É—inga É—iban cikin cokali daya da rabi ana sha da nono ko yoghurt mai kyau za ayi mamakin yadda nono zai canja ya cika taf. 

Hanya ta bakwai:

Za'a samu garin hulba a tafasa sai a rika gasa su idan an gama sai a samu man hulban a shafa musu wacce za'a ga yadda nonuwa zasu cika haka nan kuma su miÆ™e tsaye gwanin sha'awa. 

Hanya ta takwas:

Idan aka samu garin alkama sai a samu ruwan gyaɗa a kwaɓa sai a sheka ruwan zafi ko a zuba cikin tukunya a rika motsawa har ya dahu a sauke a zuba madara da sugar a sha.

Hanya ta tara:

Za a samu alkama a wanke a saka kayan ƙamshi a markaɗa idan ya kwanta sai a tace a dama, a samu farar shinkafa ta tuwo a wanke a shanya ya bushe sai a kai inji a nuko ko a daka sai a samu nono a sha kullum da safe kafin aci komai za a iya sha da madara ko yoghurt.

Hanya ta goma:

A samu garin aya da dabino ana sha da peak milk shima yana yi sosai.

A samu zuma mai kyau a haÉ—a da man hulba waje guda kullum a sha cokali 2 duk 10 minute kafin cin abinci.

Hanya ta goma sha daya:

A samu;

Habbatus-sauda 1 cokali.

Zuma farar saka 1.

Dakakkiyar tafarnuwa.

Ruwan zafi rabin kofi.

Sai a zuba a gauraya sosai a sha kafin a kwanta barci a sha kafin a yi karin kumallo sau biyu 2 a rana.

Hanya ta goma sha biyu 

Idan ana buƙatar nono su cika suyi laushi a samu;

Garin hulba.

Cukwi faranti 3.

Farar shinkafa.

Garin alkama.

Garin aya irin bula bula din nan.

Sai a hadesu waje guda a É—inga sha da madara peak ko kindirmo, sannan a dinga gasasu da hulba, sai kuma a shafesu da man hulba a É—inga saka rigar nono watau bireziya wacce zata kama nonon sosai. 

Hanya ta goma sha uku:

Idan ana bukatar manyan nono irin su cika suyi sutu sutu, domin hakan yana ƙayatar da maza.

Sai a samu;

Madarar Shanu

Zuma

Dan kalin turawa

Cucumber 

Kayan marmari.

A samu dankalin turawa a dafashi ya dahu sosai idan yasha iski a haÉ—a shi da cucumber sai a markade shi, a dinga sha da madarar shanu da zuma ana sha na tsawon wata. 

Sannan a dinga yawan shan kayan marmari.

Da wannan na kawo Æ™arshen yadda Æ´anmata ko budurwa zata gyara nonuwanta. A karanta a nutse, sannan a jarraba domin samun cikakken sakamako! 

Na barku lafiya.

Post a Comment

0 Comments