Amfanin tafarnuwa ga azzakari

 Amfanin tafarnuwa ga azzakari

Tafarnuwa Garlic kenan a turance, wata ɗan itaciya ce mai kama haka kuma mai alaƙa da albasa watau onion. Sai dai ita tafarnuwa tafi albasa ƙanƙanta haka kuma warin tafarnuwa yafi na albasa ƙarfi da kuma gafi. 

Tafarnuwa ta kasance ɗaya daga cikin kayan mahaɗi na dafa abinci ko magani da aka fi sani a kowane gida. Domin tana da abubuwan ban mamaki na amfani da ake yi na yau da kullum. Babban darajar sinadarai da kayan magani na tafarnuwa shine tana iya warkar da cututtukan jijiyoyin jini dana numfashi da yawa a jikin ɗan adam.

Kamar yadda muka sani ne, tafarnuwa ana amfani ne da ita yawanci a ɓangaren spices na girki watau ire iren abubuwan nan da ake ƙarawa ko kuma nace ana sawa a abinci domin ƙarin ɗanɗano ko ƙamshi a wannan girkin. Haka kuma ana amfani da tafarnuwa a wurin haɗa yaji ko kuma duk dai wani spices da ake buƙatar ɗanɗanon tafarnuwar a cikinsa. 

Haka kuma ana amfani da tafarnuwa sosai wurin haɗin mgunguna kala kala, musamman magunguna masu magance matsaloli irin na sanyi. Saboda ita tafarnuwa bincike ya tabbatar sahihiyar magani ce ta sanyi. 

Tafarnuwa tana taka rawar gani wurin magance matsalar mura musamman ga mutane masu fama da matsalar ciwon wuya ko kunne ko kuma ciwon kai duk na sanyi. Haka kuma tana maganin matsalar sanyi wacce ta haɗa da majina. 

A yau a wannan zamanin akwai pharmaceutical preparations watau haɗaɗɗun magungunan bature da zaku ga ana sayarwa a shagunan magani, waɗanda ake kira natural home remedy to ire iren waɗannan magungunan idan kuka bincika zaku ga akwai tafarnuwa a cikin wannan haɗin maganin. 

Amfanin tafarnuwa ga azzakari
Amfanin tafarnuwa ga azzakari post#

Binciken kimiyya ya tabbatar da wanzuwar wani sinadarin anti histamine a cikin ƴaƴan tafarnuwa wanda kuma shi wannan sinadarin shine yake da alhakin yaƙar cutar sanyi da mura da kuma majina a jikin ɗan adam. 

Haka kuma tafarnuwa cike take da sirrika kala kala waɗanda idan mutum bai sani ba, bai kuma nema ba, to ba lallai ne yasansu ba. 

Kaɗan daga cikin ire iren sirrikan tafarnuwa sun haɗa da;

-yawan cin tafarnuwa na taimakawa namiji ƙarin kuzari da ƙarfin mazakuta. 

-amfani da tafarnuwa a wurin ɗiya mace yana ƙara mata tsukewar gaba da ƙarin ni'ima. 

-amfani da tafarnuwa yana ƙara gyarawa mace zaƙi da amon murya, bincike ya tabbatar da wannan. 

-amfani da tafarnuwa yana ƙara taimakawa kwarin gaɓɓan jikin ɗan adam. 

Kuma kunsan wani abu, bafa iya wannan bane! Yin amfani da tafarnuwa har ma yana iya taimakawa wajen magance matsalar rashin ƙarfin mazakuta. Matsalar rashin ƙarfin mazakuta lamari ne na sirri wanda zai iya sa rayuwarku ta zama damuwa da takaici. Amma lokaci yayi da zaku yi bankwana da matsalolin rashin ƙarfin mazakuta domin amfanin tafarnuwa ga azzakari idan kuna amfani da ita.

Wani bincike na Cibiyar Kiwon Lafiya ta Jami’ar Middle Sex ta gano, tafarnuwa tana ɗauke da furotin, mai, carbohydrates, fiber da ma’adanai masu mahimmanci kamar iron, calcium, potassium, phosphorus, potassium, da bitamin B6 da C.

Anan akwai bayanai masu ban sha'awa ga duk mazajen dake neman hanyoyin ɗabi'a don magance matsalolin mazakuta. Ku sani yin amfani da afarnuwa ga azzakari na warware muku matsalar mazakuta. 

Amfanin Tafarnuwa ga azzakari

Bincike ya gano cewa tafarnuwa na da sinadarin da ake kira Allicin wanda ke ƙara haɓaka kwararar jini zuwa ga azzakari sosai. Wannan na iya ƙara ƙarfin mazakuta da ƙara ƙarfin sha’awar jima’i. Maza masu matsalar rashin ƙarfin azzakari, suna iya yin amfani da tafarnuwa guda biyu zuwa uku kowace rana don ci. Ana iya ci ɗanye ko kuma a saka shi a abinci bayan an gasa shi.

Idan zaku yawaita cin tafarnuwa a cikin abinci tana taimakawa wajen magance matsalar rashin ƙarfin mazakuta ga namiji. Cin tafarnuwa tana taimakawa ko ƙarawa namiji kuzari da ƙarin ƙarfin azzakari. Duk namijin da yasan amfanin tafarnuwa ga azzakari ba zai yi wasa da ita ba.

GA MAZA MASU SAURIN KAWOWA KO KUMA SAURIN INZALI

Nasan dai zaiyi wuya ace zuwa yanzu bamu san matsala irin wannan ba, watau matsalar saurin inzali, haka kuma yawancin maza masu irin wannan matsalar baka raba su da rashin ingancin maniyyi, dalilin kuwa shine matsalar saurin inzali tana haɗe ne ko kuma tare suke tafiya da rashin ingancin maniyyi watau dai ma'ana suna tafiya ne hand in hand, inji bature. A wurin mutane da yawa wannan matsalar tana da sanannen magani a nau'in tafarnuwa haka kuma da yawa basu sani ba, to koma dai wannene kai a ciki, yanzu kazo wurin da za'a fayyace maka wannan sirrin. 

Ga maza masu fama da saurin inzali da kuma tsinkakken maniyyi mara inganci su riƙa haɗiyar tafarnuwa kamar aƙalla biyu a rana. Su jiɓanci yin haka na kamar tsahon mako ɗaya amma kar a ɗara hakan. 

ƘAIƘAYIN MARAINA KO AZZAKARI

Idan namiji yana jin ƙaiƙayi a jikin marainansa ko azzakarinsa, to sai ya sami garin farar kanwa cikin babban cokali ɗaya, ya dafa da ruwa kofi biyu, idan ya tafasa sai ya zuba man tafarnuwa babban cokali biyu ya gauraya sannan ya sauke, idan ya huce sai ya wanke gabansa gaba ɗaya da ruwan zai sami sauƙi.

WANDA BAYA IYA SADUWA DA IYALI

Wanda baya iya saduwa da iyali fiye da sau ɗaya ko kuma daya soma sai ya ji ya gaji, to sai ya sami dabino mai kyau guda ya dafa da ruwa mai kyau, idan ya tafasa sai ya tace da farko zai dafa da ruwa kamar kofi huɗu 4 bayan ya tace sai ya ɗebi kofi uku ya sake tafasawa yana cikin tafasa sai ya zuba man tafarnuwa babban cokali biyu 2 sai ya barshi akan wutar ta yadda ruwan zai dawo kamar kofi biyu 2 idan ruwan ya huce sai ya riƙa sha babban cokali biyu sau huɗu a rana, yayi kwana bakwai 7 yana yin haka.

GWAIWA KO TINJERE KO ƘANJAMAU KO FITAR WANI RUWA DAGA AZZAKARI .

Wannan ruwa akan ganshi da yauƙi-yauƙi kuma rawaya-rawaya, wannan ruwa ba ciwon sanyi bane, alamu ne da suke nuna cewa gwaiwa na tafe.

Maganin waɗannan abubuwa shi ne a samu zuma mai kyau tatacciya kofi uku (3) a sami man shanu kofi (2) a sami man tafarnuwa cikin babban cokali huɗu a haɗa su guri ɗaya a dafa, su cakuɗa sannan a sauke, idan sun huce sai a riƙa sha cikin babban cokali biyu (2) sau huɗu a rana.

WANDA AZZAKARINSA BA YA TASHI SOSAI KO KUMA IDAN ZAI KUSANCI IYALI SAI YA KWANTA

Amma kada ka manta akwai na aljanu idan ka gwada wanna sai ka nemi malamai. Ka samu garin kanumfari cikin babban cokali biyu, a kuma samu wani abu da ake kira da turanci ”TEMPLE INSENCE” a dake a deɓi cikin cokali (3) sai a samu madarar saniya kofi biyu (2) a zuba man tafarnuwa babban cokali huɗu (4) a gauraya sai a sha rabin kofi da RANA DA YAMMA RABI DA DARE RABI DA SAFE, idan ya aka yi haka sai ayi fashin kwana ɗaya, sannan a sake yin haka sau huɗu.

WANDA YAKE DA MATSALAR TSARGIYA

Cutar tsargiya dai ba wata ɓoyayyar cuta bace, ita dai cutar tsargiya cuta ce da mutum zai riƙa jin zafi mai tsanani a yayin da yazo yin fitsari, ko kuma ya riƙa ganin jini a tare da fitsarinsa, ko kuma fitsarin ya riƙa zuwa da kyar haɗe kuma da zafi sosai. Wannan cuta ta tsargiya dai bincike ya nuna cewa infection ne yake kawota kuma tafi kama irin mutanen nan masu yin fitsari ko bahaya a gefen hanya da kuma mutane masu yin amfani da public toilets irin wanda ake amfani dashi ana biya ɗinnan. To irin wannan matsalar ta tsargiya, bincike ya tabbatar cewa a cikin irin ababen da suke magance ta, tafarnuwa tana kan gaba. 

Anan ana yin haɗin tafarnuwa ne da zuma baƙar saƙa. Za'a daka tafarnuwa sosai ta daku sannan a kawo zuma baƙar saƙar nan kamar rabin kofi a haɗa a juya ya zamana mixture ɗin ya haɗe kansa, sai kuma a samu lemon tsami manya masu ruwa kamar guda uku haka, shima a yanka a matse duk a ciki. 

Mai fama da wannan lalura ta tsargiya zai jiɓanci shan wannan haɗin na tsahon mako ɗaya, a jarraba aga abin mamaki. 

MAI ƘURAJEN GABA MASU ƘAIƘAYI MAI TSANANI 

Kar mai karatu ya manta, a sama nayi bayanin wani sinadarin anti histamine, wanda shi wannan sinadarin ke da alhakin yaƙar majina ta mura ta sanyi dasu toshewar hanci da atishawa, to kasancewar shi wannan sinadarin na anti histamine yana da rukuni rukuni ne, misali akwai anti histamine A, akwai anti histamine B, haka kuma akwai C da D. To kowanne daga cikin rukunan shi wannan babban sinadarin, akwai irin matsalar da yake yaƙa a jikin halittar ɗan adam. Kamar a irin wannan matsalar ta ƙuraje masu ƙaiƙayi mai tsanani wanda su ɗinma yawancin su infection ne yake kawosu, to idan aka samu man tafarnuwa mai kyau aka kuma dace ana haɗawa da man zaitun ana shafe wurin da ƙurajen suke fesowa, lallai ina faɗa maka zaka sha mamaki domin wannan haɗin maganin ko tabon ƙurajen baya bari, bare kuma su kansu ƙurajen. 

MAI ƘURAJE MASU ƘAIƘAYI SUNA RUWA

Wanda yake fama da ƙurajen gaba masu ƙaiƙayi haka kuma masu ruwa, to anan fa ya kamata a sani cewa ƙuraje ƙananu masu ƙaiƙayi da kuma ƙuraje masu ƙaiƙayi kuma suna ruwa akwai banbanci. Idan waɗancan ƙananun ƙuraje masu ƙaiƙayi ana alaƙanta sune da infection to su kuma waɗannan masu ruwa anfi alaƙantasu ne da infection ɗin fatar gaban namiji. Amma su waɗannan anfi magancesu da ruwan dakakkiyar tafarnuwa ziryan basai an haɗata da wani abu ba. 

SIRRIN TAFARNUWA NA JIN DAƊIN JIMA'I 

A samu tafarnuwa mai ɗan dama sannan duk a ɓare ta daga wannan ɓawon nata, sannan kuma a samo man zaitun wanda aka tabbatar da kyau da kuma amincinsa. Daga nan sai a daddatsa wannan tafarnuwa gutsi gutsi sannan a watsa ta a cikin wannan man zaitun ɗin. 

A rufe wannan haɗin sosai yadda ko iska ba zata samu damar shiga ciki ba, kar a buɗe har na tsahon misalin kwana biyar. Yadda za'a riƙa amfani dashi kuwa shine; a riƙa ɗiban haɗin nan kaɗan ana shafawa akan azzakari ana murzawa ana massaging amma fa a yayin a ake yin wannan massaging ɗin, idan akaji sha'awa ta bijiro sosai har hankali yana neman tashi sai a haƙura a barshi domin idan ana cikin yi aka kai gayin inzali to bazai yi aiki ba. 

Aikin wannan haɗin kuwa shine yana ƙarawa azzakari tsaho da kauri da cikakkiyar lafiya. Kuma haɗin, haɗine ba na wasa ba domin duk wanda ya samu ya gwada bazai gushe ba shima sai ya fesawa wani abokin nasa labarin wannan haɗin mai abin mamaki. 

Da fatan za'a bi abin da rubutun nan ya ƙunsa daki daki a sannu. Idan an karanta kuma a fahimta sannan a aikata a aikace.

Post a Comment

0 Comments