Amfanin man zaitun a gaban mace
Da kinji ko kaji sunan wannan maudu'in namu na yau to kinsan ko kuma nace kasan cewa akwai bayani ko kuma nace bayanai a yau, a game da wannan maudu'in.
Mai yasa hakan?
Dalili shine ko ba'a faɗa miki ba ko ba'a faɗa maka ba kin ko kasan cewa man zaitun magani ne sahihi, kuma mai ne mai daraja a rayuwar ɗan adam. Kasancewar sa magani, man zaitun a gaban mace yana da alfanu masu yawan gaske. Tare daku zan kasance mai lissafo wasu daga cikin amfanin man zaitun, amma a ƙarshe zan fi maida hankali na akan amfanin shi man zaitun ɗin a gaban mace kamar yadda maudu'in namu ya nuna.
Man Zaitun (Olive oil)
Olive oil, wanda akafi sani da man zaitun, wani mai ne da ake samu daga jikin ƴaƴan wata itaciyar bishiya mai suna olive tree. Ƴaƴan itaciyar sun kasance wasu ƙananan korayen kwayoyi ne masu kwallo a cikinsu. Haka kuma yana cikin wasu zaɓaɓɓun mayuka guda biyar waɗanda suke natural ma'ana dai ba mutum ne ya ƙirƙire su ba.
WaÉ—annan mayukan sune waÉ—anda ake kira da essential oils, yawa yawan masu karatun nan zai yiwu sun san waÉ—annan mayukan, to olive oil watau man zaitun ya kasance É—aya daga cikinsu.
Wasu daga cikin amfanin man zaitun:
-Man zaitun mai ne da bincike ya tabbatar da muhimmancin sa wurin gyaran fatar É—an adam.
-Man zaitun yana gyara gashin mutum sosai, yana sawa gashi yayi laushi ya riƙa sheki. Mata gareku.
-Man zaitun kamar yadda aka ambata a baya, maganine sahihi yana maganin amosanin kai dana ido.
-Man zaitun yana maganin ciwon kunne musamman na sanyi.
-Man zaitun yana maganin abinda a turance ake kira da bad breathe. Watau ma'ana dai irin mutanen nan masu fama da matsalar warin baki, ko kuma nace wani odour da yake bugowa a yayin da duk suka buÉ—e bakinsu. To irin wannan matsalar mutane da yawa basu sani ba, amma tana farawa ne tun daga cikin mutum. Olive oil yana magance irin waÉ—annan matsalolin sosai.
-Zaku iya tambayar masu jurar lasa man zaitun a bakinsu suna haɗiya. Shan man zaitun yakan magance matsalolin gyambon ciki watau ulcer, yakan magance matsalolin indigestion ko nace kwarnafin ciki, har ila yau man zaitun na maganin stomach upsetting watau yawan ɓacin cikin mutum ko kuma danƙarewarsa ma'ana constipation.
-Man zaitun yana magance matsalar kaushin ƙafa da hannu dana jiki ma. Da yake man zaitun maganin ciwukan fata ne, kunga kenan sam ba abin mamaki bane dan kunji nace maganin kaushi da faso ne, haka ma ga masu gautsin fata ko waɗanda fatarsu take da rauni duk dai man zaitun yana taimakawa sosai wurin magance matsaloli irin haka.
-Man zaitun abokin tafiya ne a wurin masu son su tsufa da gaɓɓansu. Idan kana ko kina shafa man zaitun a jikinka ko jikinki musamman a gaɓɓai kamar; wuyan hannu watau wrist, da guiwowin hannu watau ma'ana dai elbow kenan, da guiwoyinku, knee kenan a turance, da idon sawayen ƙafafuwanku to kuwa zaku ga ko sanyi mai naci bazai riƙa baku matsalolin ciwon jiki dana gaɓɓai ba.
-Har ila yau man zaitun abinci ne domin kuwa a wasu sassa na duniya ana yin girke girken abinci tare da wannan kwallon na zaitun ko nace ƴaƴan itaciyar zaitun. Ƙasashen larabawa watau mutanen gabas na ɗaya daga cikin manyan misalan irin wuraren da ake amfani da man zaitun a girke girken abinci.
Amfanin man zaitun a gaban mace da ni'imarsa:
Munzo asalin kan zancen kai tsaye, live, kenan inji masu jajayen kunnuwa. Amfanin man zaitun a gaban mace. Shine asalin abinda wannan rubutun ya ƙunsa, duk abinda aka karanta a sama sharar fage ne.
Mata ku matso ku bani hankulanku domin bayanin duka naku ne. Matar aure ko bazawara ko ƴan mata duka dai, wannan rubutun yana da amfani a gareku, musamman masu neman ni'ima ko ƙarin ni'imar. Musamman masu infection na sanyi a gabansu da masu matsaloli irin na jini da ciwon al'ada da ciwukan mara, haka kuma a ƙarshe da masu neman juriya a yayin kwanciyar shimfiɗa.
Akwai haɗin da zaki iya yi da man zaitun domin samo duk waɗannan abubuwan da kika karanta a sama. Akwai wasu mata wanda zaku ga gabansu ƙandas yake ba ruwa, wannan wata alama ce dake nuna cewa irin waɗannan matan basu da ni'ima. Wannan ne dalilin da yasa a cikin duk irin matan dana lissafo a sama na fara lissafin da masu neman ni'ima ko kuma masu neman ƙarin ta.
Idan kin san gabanki ƙandas yake babu ruwa ko maiƙo ko danshi to kin rasa flora, flora kuwa shine wannan ruwan ko maiƙo maiƙon da yake riƙe gaban mace kuma yake yaƙar infections ɗin gaban mace haka kuma yake ƙara mata ni'ima. Idan kika jiɓanci amfani da wannan haɗin da zan bayar yanzu na man zaitun to sai kiga duk waɗannan matsalolin da kike fama dasu a gabanki sun rabu dake cikin sauƙi.
Ga mace ko mata masu neman ni'ima, ku samo man zaitun mai kyan ba irin wanda ake masa mix ba, idan kika samu man zaitun ɗinki sai ki samo ƴaƴan hulba ki dake su sannan ki zuba a cikin man zaitun ɗinnan ki juya sosai ya game kansa. Daga nan sai ki riƙa lakata kina gogawa a gabanki akalla sau uku zuwa biyar ko wace rana. Idan kika juri haka to za kiga idan ada kin kasance gabanki a bushe yake to yanzu za kiga gabanki yana da danshi haka kuma zaki samu ni'ima sosai a yayin tarawa da maigida, kuma shima maigida zai ji kuma zai gane an samu sauyi. Ke ƙila ma sai yayi miki babbar kyauta ina faɗa miki.
Amfanin wannan haÉ—in na man zaitun da Æ´aÆ´an hulba ba'a iya samun ni'ima ya tsaya ba domin kuwa zai taimaka miki sosai idan kina da matsalar ciwon mara a yayin da jinin al'adarki yazo ko kuma yake shirin zuwa. Haka nan ga mata masu infection na sanyi a gabansu ko kuma wani infection É—in na daban duka wannan haÉ—in zai iya magancesu.
Hakanan ga masu ciwon mara na al'ada watau menstrual cramps, kuga mace a yayin duk da jinin al'adarta zai zo, to ta ɗinga fama kenan da ciwon mara. Zasu iya amfani da ruwan zafin da aka ɗigawa man zaitun bayan an dafa ruwan, sai a samu towel a riƙa tsomawa cikin ruwan zafin sannan a matse towel ɗin sama sama, sai ake dannawa akan marar har zuwa jikin farji. Wannan massage ɗin yana da matuƙar muhimmanci ga mata masu fama da lalurar menstrual cramps.
Akwai kuma mata masu fama da matsalar warin gaba da kuma wasu matan masu vaginal discharge mai wari ko ƙarni. Vaginal discharge anan ina nufin duk abinda zai ke fitowa daga gabanki. To idan kina daga cikin irin matan nan masu vaginal discharge mai wari ko ƙarni to gareki, kisani wannan matsalar cuta ce kuma kamar yadda muka sani ko wace irin cuta da maganinta. Saboda haka ki samu man zaitun ɗinki da dakakken kanunfari ki riƙa ɗiba kina shafawa a wurin ya zamar miki man farjinki, ki saba da amfani dashi sosai idan aka dace sai kiga wannan matsalar taki ta zama tarihi kamar baki taɓa fuskantar matsala irin wannan ba.
A karanta a fahimtu sannan sai a aikata a aikace.. Za'a asha mamaki.
0 Comments