Yadda ake wankan janaba a rubuce
Wannan jawabi ƙunshe yake da yadda ake wankan janaba a rubuce cikin jerin matakai shida, amma da farko, zai fi kyau muyi bayani akan shi kanshi wankan tsarki a musulunci.
Menene wankan janaba ko tsarki ?
Wankan janaba ko wankan tsarki wani wanka ne da ake gudanarwa domin samun tsarkin jiki da kuma damar cigaba da ibada a addinin musulunci, kuma hakan yana biyo bayan wasu abubuwa kamar kusantar matar aure, ga masu aure kenan wato saduwa da matarka, ko kusantar mijinki, fitar maniyyi wanda ya fita ta saduwa ko istimna'i shima yana wajabta wanka, haka zalika bayan ɗaukewar jinin al'ada da kuma jinin biƙi ga mai jego kenan. Wankan janaba farilla ne ga duk wani baligi ko baliga wato dole ne ayi shi idan buƙatar hakan ta taso.
Ayi sani cewa wankan janaba farilla ne daga cikin farillai da aka farlantawa musulmai gaba ɗaya.
Ire-iren wankan tsarki:
Wankan tsarki yanada ire-ire guda biyu wanda sune:
1. Siffatul kamal -wanka na kamala
2. Siffatul ijza -wanka wadatacce
Ga bayanin ire-iren yadda ake wankan janaba a rubuce:
1. Siffatul kamal__
Wanka ne wanda ake yinsa ta bin hanya a aikace, wato ɗaya bayan ɗaya za'a bi lunguna da saƙuna na jiki a wanke, irin siffar wannan wanka shine yafi kawo lada fiye da siffar wanka na biyu.
2. Siffatul ijza__
Siffar wanka ne na yadda ake wankan janaba a rubuce wanda mutum yake gabatar dashi, bayan yayi niyyarsa sannan kai tsaye ya faɗa cikin ramin wanka kamar swimming pool ko kududdufi yayi ninƙaya, hakan ya halatta daga cikin sahihul muslim, sannan wannan wanka, zaka iya yinsa idan ka samu bokitin ruwa, sai ka zubashi a jikinka, shima hakan ya wadatar. Sai dai kuma ayi sani cewa wanda ya gabatar da siffar wanka na fari, yafi kamala akan wannan na biyun dalilin kuwa shine yafi cika dukkan sharuɗa.
Dalilin yin wankan janaba ko tsarki:
A wannan ɓangare na yadda ake wankan janaba a rubuce zamu kawo maƙasudin ko dalilin da yasa ake wankan tsarki a musulunci. waɗannan abubuwa sune kamar:
1. Ɗaukewar jinin al'ada.
Ya zama wajibi ayi wankan tsarki bayan an samu ɗaukewar jinin haila ko al'ada wanda mataye suke yi duk bayan wani lokaci, domin su samun damar cigaba da yin ibadar sallah dama sauran wasu ibadun.
2. Ɗaukewar jinin (haihuwa).
Da buƙatar uwargida mai haihuwa tayi wanka bayan ficewar duk wani jini daga jikinta, domin yin tsafta da kuma dalilan addini.
3. Fitar maniyyi.
Matsawar baligi ko baliga ta fitar da maniyyi bayan yin sha'awa ko kusantuwar jima'i ta iyali, to ya zama wajibi su gabatar da wankan janaba, haka zalika koda bayan anyi istimna'i.
4. Shiga musulunci.
Bayan shigar wanda ba musulmi addinin Islama shima ya zama wajibi yayi wanka, wato abun nufi anan shine idan kafiri ya shiga addinin Musulunci to fa zai yi wanka gwargwadon iyawarsa a matsayin wankan tsarki.
5. Wankan zuwa sallar idi.
Wannan shi muke cewa wankan sallah, wato da buƙatar idan za'a je idi ranar sallah, to kayi wankan tsarki domin tsaftace jiki.
6. Domin zuwa masallaci ranar juma'a.
Masallacin juma'a na ɗaya daga cikin abubuwan dake kawo wankan tsarki a musulunci, shima malamai sun bayar da fatawa mai yawa akan yin wanka yayinda za'a je masallacin juma'a.
Yadda ake wankan janaba a rubuce cikin matakai shida:
1. Da farko Za'a samo ruwa me kyau mai tsarki, idan ba'a rufe wannan ruwa ba to sai a ajiyeshi a gefen hannun dama, idan an rufe wato me murfi ne a gefen a hannun hagu.
2. A fara da bismilla sannan a wanke hannu sau uku (3) sannan ayi niyya, amma niyyar a zuci ake yi. ko ba’a yi ba, babu laifi, domin niyya tana somawa ne tun lokacin aka ɗauki abinda za'a yi wanka, buta ce ko bokiti da dai sauransu.
3. Na uku, sai ayi tsarki sannan a wanke al'aura da kewayensa, bayan wannan sai kuma ayi alwala, sai dai kuma za'a jinkirta wanke ƙafafuwa sai zuwa ƙarshen wankan. Malamai sun ce anyi hani ga barin sunnah a lokacin yin wankan tsarki, domin barin sunnah makaruhi ne, wato da buƙatar ayi cikakken wanka tareda farillansa da kuma sunnoninsa. Wato kaga kenan alwalar za’a gabatar da ita cikakkiya kamar za’a yi sallah.
4. Mutum ya haɗa hannu biyu ya nutsar dasu a cikin ruwan sai ya debo sannan ya zuba a kansa tareda murzawa har sau 3, idan kuma ya kasance ruwan a cikin bokiti yake kenan. Idan kuma a buta ne to sai a ɗaga a zuba.
5. Lokacin da ake wanke kai za'a haɗa harda wuya, da wankin fatun kunne cikinsu da waje, mata kuma zasu zuba ruwa a cikin gashin kansu sannan su bubbuga sai ruwan ya shiga ko ina sosai. Amma idan matar tana da larura to da buƙatar ta shafa kanta sau uku shikenan. Daga nan kuma sai a wanke tsagin jikin dama tun daga kafaɗa har ƙafa, sannan a wanke shima tsagin jikin hagu tun daga kafada har zuwa ƙafa, a cuccuɗa sosai yadda ya kamata.
6. Sannan daga ƙarshe kuma sai a game dukkanin ilahirin jiki da ruwa a tabbatar an wanke ko'ina.
0 Comments