Siffofin mace harija guda 8

Siffofin mace harija ko me tsananin sha'awa

Wacece Mace harija? Kuma waɗanne siffofi ne siffofin harijar mace waɗanda zaku iya gane ku gane cewa ita ɗin harija ce, da kuma siffofin da ba zaku iya gani ba. Duka dai idan kuna tare dani a cikin wannan rubutun zan zayyano muku siffofin ita harijar mace kuma nayi muku bayani daki daki, sai dai kuma kafin nan aɗan taƙaice ya kamata ayi duba akan ainihin ko kuma asalin ita kalmar "harijar" menene ma'anar ta kuma me take nufi. 

Da farko dai kalmar harija an samo tane ko kuma an aro tane daga kalmar "harij" a larabce kenan kuma tana nufin rashin gajiya ko kuma wanda baya gajiya ko kuma idan a keɓantacciyar ma'anarta ne za'a iya cewa wanda ko wacce basa gamsuwa. Wannan a taƙaice shine literal meaning watau asalin ma'anar kalmar kenan. Ina fata an fahimta. Sau da yawa mutane suna amfani da kalmar harija.. harija.. ko kuma idan namiji ne kuji ana ai hariji ne, amma kuma mutanen da suke amfani da waɗannan kalmomin basu san cewa mata a fagen daga ko kuma nace a bisa shimfiɗa ko kuma inyi muku gwari gwari yadda zaku fi fahimtar karatun; mata a wurin tarawa ko kuma saduwa da ɗa namiji sun kasu ko kuma ana kasa sune zuwa gida uku kamar haka; 

1- dakila

2- munkila

3- harija 

Ko ban faɗa ba, haka kuma ko ban tambaya ba, nasan makaranta basu san kaso biyun farko ba, na ukun kawai suka sani watau harija wanda kuma akan siffofin harijar mace wannan rubutu zai yi tsokaci akai, sai dai kuma anan ɗin ma idan kuna tare dani zanyi bayani a gurguje ko a taƙaice game da kashe kashe na mata guda ukun dana lissafo a wurin tarayya ko kuma kwanciya da ɗa namiji a shimfiɗa. 

1- Dakila

Ita dai mace dakila sune irin matan nan wanda sam kwata kwata basu da ƙarfin sha'awa. Ire Irensu waɗannan matan zai yi wuya kuga sunzo sun kawo kansu ga mazajensu wai da sunan sha'awar su ta bijiro kuma suna san a biya musu buƙatar su. Dakilar mace sexual feelings ɗinta watau bijirowar sha'awarta ta aba ce mai matuƙar wahala. Ire iren matan nan a duk lokacin da namiji yazo musu da sunan kwanciya dasu sukan ji cewar su fa ana takura musu ne. Kai abar ma maganar kwanciya dasu domin ba'a kai nan ba, dai dai da wasannin soyayya kamar irin su kiss da taɓe taɓen jiki ko kuma sassan jiki masu tsokano ko kuma bijiro da sha'awa, mata dakilai basa maraba dasu. A taƙaice dai zamu iya cewa mace dakila ko kuma mata dakilai sune matan da basu da sha'awa ko kuma sha'awar mai mugun rauni ce. 

2- Munkila 

Munkilar mace ko mataye da suka kasance munkilaye sune kaso na biyu cikin kashe kashen mata a fagen kwanciya ko saduwa da namiji. Munkilan mataye sune waɗannan matan da sha'awar su ke zuwa jifa jifa. Idan mace munkila ta haɗu da harijin namiji to lallai ne zata riƙa takura matuƙar ba dacewa akayi ba sha'awar tasu ta bijiro a lokaci ɗaya ba, wanda haka bai cika faruwa ba ko kuma nace yana matuƙar wahala hakan ta kasance. Munkila kamar yadda na bayyana, bijirowa ko kuma tasowar sha'awar ta sai lokaci zuwa lokaci ne watau jifa jifa kuma akan ɗauki lokaci kafin tazo. Sai dai kuma idan sha'awar munkila ta bijiro to kuwa taka bada haɗin kai yadda ya kamata ba kamar dakila wacce nayi bayani a sama ba, wacce ita bijirowar sha'awar ma ba'a zancen ta. 

3- Harija

Harijar mace ko kuma nace harijan mataye waɗanda a kansu ne wannan bayanin ya tara mu, sune kaso na uku a cikin kashe kashen mata a fagen kwanciya ko kuma saduwa da namiji. Harija ko harijan mataye sune masu tsananin ko kuma matuƙar sha'awa. Aƙalla ba ƙasaru ba, sha'awar mace harija takan tashi ta kai maƙura sau babu adadi domin abun nasu babu ƙiyastawa. Haka kuma, sha'awar harijar mace tafi motsawa ko nace tafi kaiwa ƙoluluwa da kuma neman buƙatuwa idan tasan akwai namijin da yake ɗebe mata kewa ko kuma dai zamu iya cewa tana da namijin da duk lokacin da taji buƙatar ta ta motsa to shi wannan namiji zai agaza mata. 

Wannan shine ɗan taƙaitaccen bayani game da yadda aka kasa mata a fagen mu'amalar saduwa da ɗa namiji. 

Siffofin mace harija bayani dalla dalla

A yanzu kam mun iso gaɓar da nasan cewa makaranta sun zaƙu azo kuma gashi a sannu mun iso, kun san dama masu iya magana kan ce; sannu bata hana zuwa, sai dai a daɗe ba'a je ba, kuma masu jajayen kunnuwan watau turawan yamma, suma a tasu faɗar suke cewa; slow and steady wins the race. To kamar haka ne gashi munzo dai dai kan gaɓa, watau siffofin mace harija. Kai tsaye yanzu zan lissafo muku siffofi watau signs waɗanda idan kun lura kun gani a tare da wata mace to kar ku rabe ɗayan biyu cewa ita ɗin harija ce, haka kuma akwai wasu siffofin da duk saka idon sa'idawa ko kuma duk kwakwar mai sa ido to bai isa yaga alamomin ba sai dai idan ita harijar ce da kanta ta ga dama ta bayyana muku. Idan makaranta suna tare dani zan lissafo muku siffofin ko kuma nace alamomin domin ku zaɓa ku darje a ciki kuga waɗanne ne a ciki zaku iya gani ku gane kuma waɗanne ne zaku iya lura ku gane da kuma waɗanda na faɗa muku duk sa idon mai sa ido to ƙaryar sa ya gane su. 

Ba tare da ɓata lokaci ba ga alamomi ko siffofin harijar mace kamar haka;

1- Alamomin harijar mace ta yan yatsun ƙafarta 

2- Mace mai wasa da maza

3- Mace mai son jiki

4- Mace mai son bacci

5- Mace mai yawan lumshe idanu 

6- Mace mai yawan kallo ko kuma tsawaita kallon namiji

7- Mace mai sauƙin kunyar maza

8- Mace mai jan ragama a yayin saduwa.

Ga bayanin siffofin mace harija a ƙasa

1- Alamomin mace harija ta yan yatsun ƙafarta

Idan yatsar ƙafar mace na kusa da babban ɗan yatsa yafi babban ɗan yatsan tsawo to hakan yana nuna cewar mace mai irin wannan yan yatsun kafar tana da tsananin sha'awa mai ƙarfi. 

-Idan kuma babban ɗan yatsan ƙafar mace dana kusa dashi ya zamana tsayin su ɗaya to hakan yana nuna mace mai irin wannan yan yatsun kafar tana da sauƙin sha'awa sosai. 

-Idan babban ɗan yatsan mace na ƙafa yana da girma da kuma tsawo sosai to hakan yana nufin vagina ɗin wannan matar watau farjinta yana da ƙofa babba da kuma tsayi. 

-Idan mace nada wushiryar ƙafa watau abin nufi idan a ƴan yatsun ƙafarta akwai spaces to hakan na nufin wannan mace mai irin ƙafar nan da ƴan yatsun tana da ni'ima kuma tana da daɗin jima'i ga ɗa namiji. 

-Idan diddigen mace yana da cika, ma'ana bashi da rama to hakan yana nufin tana da juriya a wurin jima'i, duk kwakwar namiji irin wannan macen za ta iya dauke bukatar sa. 

A dunƙule ko kuma a taƙaice duk macen data faɗo a cikin waɗannan rukunan to kai tsaye zaku iya kiranta da harijar mace. 

2- Mace mai wasa da maza

Hausawa suna cewa; mace mai wasa da maza karya ce. To koma dai karyar ce ko ba karya bace ba, a ɗabi'a irin ta mace harija za kuga bata iya haƙura yayin da take tare da namiji, ko da babu saduwa ko taɓe taɓen juna, wasa na fatar baki da kuma tsawaita magana tare da maza musamman hakan ya bata damar yin zantuttukan batsa dasu haka yakan rage mata tension na irin jarabar sha'awarta da kuma buƙatar ɗa namiji da take samun kanta a kusan kowane lokaci. 

3- Mace mai son jiki

Mace mai halin mage watau son jiki itama binciken masana da manazarta ya nuna cewar tana da sha'awa mai ƙarfi wanda ake alaƙanta yawan kwanciyar ta a jikin mutane  da ragewa kanta tension ɗin sha'awar nan tata. 

4- Mace mai son bacci

A ƙoƙarin ku na gano mace harija, idan kun san wata mace mai son baccin tsiya ku ɗauko ta ku saka ta cikin jerin mata harijai. Binciken masana da manazarta da kuma kwararru a fannin sanin halin sha'awar ɗan adam sunyi tata sunyi rairaya sun kuma jefa mace ma'abociyar bacci cikin rukunin mata harijai. A cikin baccin nan mace mai tsananin sha'awa ta kan sawa ranta tarawa da namiji har ta kai ga yin mafarki ko kuma masturbation watau istimna'i. 

5- Mace mai yawan lumshe idanu

Ire iren matan nan masu lumshe idanu kamar sun sha sinadarin nan na codeine ? To gareku makaranta ire irensu duka suna cikin rukunin harijan mataye ne matuƙar kun tabbatar babu sinadarin codeine ɗin da suke kwankwaɗa. A duk lokacin da abun ya motsa watau jarabar buƙatar namiji ko kuma nace sha'awa to zaku ga tana lumshe lumshen idanu. 

6- Mace mai yawan kallo ko kuma tsawaita kallon namiji

Yawan kallo ko a ina ne yaku makaranta ko banyi bayani ba, kuma kunsan akwai abinda yake nufi. 

Mace kamar yadda aka santa da kunya amma kuma sai ya zamana idan ta kafe ɗa namiji da idanunta irin kallon nan da idan namiji ya ɗago sai yaga yarinya tana kallonsa ya ɗauke kai, haka kuma idan ya sake ɗaga kansa zai kuma ganin tana kallonsa. Wannan kallon da take wa ɗa namiji itama yana rage mata tension ne na irin addababbiyar sha'awarta. Itama irin wannan macen kuyi gaggawar saka ta cikin jerin harijan mataye. 

7- Mace mai sauƙin kunyar maza

Duk macen da kuka ga bata jin kunya ko kuma nauyin maza to akwai abin dubawa a lamarinta domin a bisa halitta da kuma al'ada irin ta mata akwai kunya da kuma jin nauyin namiji, saboda haka idan kuka ga kunyar ɗiya mace tana da sauƙi a game da namiji to akwai yiwuwar ita ɗin harija ce. 

8- Mace mai jan ragama a yayin saduwa

A yayin tarawa da namiji bisa ga al'ada an san mace da jin nauyi musamman ma kafin abubuwa suyi nisa a tsakanin masoya biyu, amma kuma mace harija a wurin ta abun ba haka bane, da zarar an fara wasannin soyayya to kuwa mace harija bata sakarwa namiji ragama ne yayi abinda yake so da ita. Mace harija za take bada gudun mawa ne ɗari bisa ɗari ba tare da jin nauyi ko kunya ba.

Siffofin mace harija complete post

Post a Comment

0 Comments