Ya ake gane mace 'yar iska

Ya ake gane mace 'yar iska

Wanga rubutu ya ƙunshi bayani na ya ake gane mace 'yar iska ko kuma mace yar bariki da halayensu.

Wacece mace ƴar iska? 

Mace ƴar iskar kai tsaye a al'ummar hausa ita ce macen dake bin maza, musamman ma idan aka tabbatar ita ɗin tana bawa maza jikinta ko dai tana mu'amala da maza kuma waɗanda ba muharramanta ba, irin wannan macen ita ce ake yiwa kallon ko kuma ake bada shaidar ba nutsastsiyi bace ko bata da kamun kai ko kuma ace ba ƴar mutunci bace. 

Related articles

Yaya zan gane macen da aka taba saduwa da ita

Bin maza a wurin mace bashi ne kaɗai nau'in rashin ji, ko rashin kamun kai da nutsuwa ko iskanci daga wurin ɗiya mace ba. Musamman a wannan zamanin idan mukayi duba da taɓarɓarewar tarbiya da ruɗanin dashi zamanin yazo mana da shi. A cikin sauran nau'ikan iskanci da ɗiya mace zata iya samun kanta a ciki akwai harkar maɗigo watau lesbian akwai kuma abinda ya danganci shaye shaye na zamani haka kuma akwai ƙawalci irin na mata kenan. 

Yana da kyau iyaye mu kula da rayuwar yaranmu mata don guje wa faɗawa ire-iren wannan ɗabi'o'in. 

A duk lokacin da uwa ta fahimci yarinyar ta tana da ƙawa da suke yawan ziyartar juna, to ta yi ƙoƙari ta yi bincike sosai. Ko ta gan ta da sabon wani abu da ta san ba ita ta saya ba.

Duka wɗdannan halaye dana lissafo a sama suna da wasu alamomi da za'a iya gane mace dasu idan tana yin ɗaya daga cikin su. 

Alamomin da ake gane mace mai bin maza ko kuma take bawa maza jikinta sun haɗar da;

Hirar dare ta hanyar zuwa zance a daɗe tare da ita na awanni da suka wuce misali ko kuma har ƙafafuwa su fara ɗaukewa. 

Idan saurayi yazo wurinta zasu shiga mota su zauna a ciki su jima, musamman mota mai duhun gilashi watau tinted glass.

Mace mai yawan samari ma'ana zaku ga samari da yawa na zuwa gurin ta. Wannan yazo wurinta yau ta bashi lokacin ta, gobe wani daban ne zai zo haka jibi ma wani sabon fuskar yazo duk kuma tana saurarensu. 

Mace da maza suke ɗauka a mota suna fita har a riƙa jimawa ba'a dawo ba.

Mace mai fitowa zanje da ɗamammiyar shiga ko kuma fitinanniyar shiga. 

Waɗannan kaɗan kenan daga cikin alamomin da kusan kowa zai iya gani ya lura waɗanda wasu matan keyi a tare da samari. Duk macen da zaku ga tana da irin waɗannan ɗabi'un da aka jero a sama to karku raba ɗayan biyu, ita ƴar harka ce. 

Alamomin mace 'yar iska post Conti...

Alamomin mata ƴan maye watau masu shaye shaye;

Mata ƴan maye ko masu shan maganin tari watau codeine mata ne masu keɓewa waɗanda basu da ƙawaye sosai ko kuma ma babu ƙawayen.

Mace ƴar maye bata damu da kula da jikinta ba ko kuma kwalliya da kyalkyalin zamani, idan ma akwai masu yi a cikinsu to ƙalilan ne. 

Yawan bacci na rashin fasali da kuma rashin cin abinci sai dai wannan baccin da shan lemo wannan ma wata alama ce da zaku iya saka alamar tambaya akan yarinya. 

Keɓewa a ɗaki su kaɗai suna bacci ko kuma idan ma ba bacci suke ba suƙi fitowa.

Kaɗan daga cikin alamomin yara mata masu shaye shaye kenan. 

Alamomi da ake gane mace ƴar madigo:

Akwai alamomi masu tarin yawa wanda ake gani da ma wanda sai su kaɗai suke gane kansu. Kaɗan daga cikin wanda muke gani a zahiri sun haɗa da;

Suna da son yin kyauta ta bajinta ga mata musamman waɗanda suka gani suna so.

Suna da mugun son yin ɗinkin riga matsattse me bayyana nononsu.

Idan sun haɗu da wacce ta yi musu sun ɗinga yi ma ta farin ido wurin yi mata magana kenan don son jawo ra’ayinta.

Suna da son yabawa structure (kyan diri) na mace musamman wacce suke son jan ra’ayinta.

Sun fi koɗa kyau na mace fiye da namiji

Suna da mummunan kishi

Ba su damu da yin mu’amala da maza ba, kullum sun fi son su raɓi mace cikin nuna sha’awa.

Suna da son kyalli da tsabta ta fitar hankali.

Suna da son yin mu’amala da kalolin turaruka.

Suna son saka sarƙa a ƙafarsu da zobe a yatsar ƙafar, duk da yanzu kusan an mayar da yin hakan gaye amma nasu na musamman ne.

Macen da take bayyanawa ƴar uwarta mace tsiraicinta.

Macen da ke yaba kyawun ƴar uwarta mace ta fuskar sha’awa.

Macen da ke rungumar ƴar uwarta mace ko sumbatarta da nufin wasa.

Macen da take nunawa ƙawarta bidiyon ƴan maɗigo.

Macen da za ta kama hannun mace ƴar uwarta ta ɗinga shafawa babu wani dalili.

Macen da za ta ɗinga shafa gashin kan ƙawarta.

Mace mai lazimtar kwanciya kan cinyar mace ƴar uwarta ba tare da dalili ba.

Macen da a koda yaushe take son ganin surar jikin mace ƴar uwarta.

Yana daga cikin alamomin ƴan maɗigo keɓancewa ƙuryar ɗaki su kaɗai.

Ƴar maɗigo ba ta da wata hira sai ta mace ƴar uwarta.

Suna kyamatar yin mu’amala da namiji, ba su damu da yin saurayi ba.

Suna da sha’awar kallon fina-finan batsa, musamman na ƴan madigo.

Suna matuƙar zama a gidan da mata ne zalla, kamar zawarawa da ƴan mata.

Macen da ke tuɓe rigarta a gaban mata ƴan uwanta ba tare da jin kunya ba.

Mace mai yawan son shafa nono ko taɓa mazaunan ƙawarta maimakon musabaha.

Suna yawan kiran junansu da ‘Sweety’ ko ‘Darling’ ko ‘Dear’ ko kuma ‘My Love’.

Suna son saka zobe a babban ɗan yatsan su na hannu.

Yawancin su suna son ƙara tsawon gashin idonsu ko shafa masa kala.

Suna auren junansu kamar yadda namiji ke auren ƴa mace.

Ya ake gane mace'yar iska post conti...

Shaƙuwa mai tsanani tsakanin mace da mace, barci kawai ke raba su.

Mace ta mayar da gidan ƙawarta kamar wurin aikin ta, koda yaushe tana zuwa gidan.

Suna ba junan su abinci a baki kamar yadda mata da miji ke yi.

Suna tausasa lafazinsu yayin amsa wayar wadda suke harka tare ko suke so.

Sukan biya wa junansu buƙata ta hanyar kiran waya ko hira a kafar sada zumunta.

Ana gane su ta hanyar hotunan mata da suke ajiyewa a wayoyin su.

Suna kulla mummunar gaba ga duk macen da take nema ta yi musu kwacen ƙawa.

Suna yawan ɗaga gira ko yin ƙifce wajen nunawa ƴar uwarsu wadda ta kwanta a ransu.

Suna da yaren da suke yi a wajen hirarrakin su, ta hanyar kushewa ko yaba junansu.

Masu auren cikinsu suna yawan tafiye-tafiye da mu’amala da manyan mata.

Ba sa gamsuwa da ɗa namiji sai sun ayyana yadda suke saduwa da abokiyar harkarsu.

Suna tsanar aure duk sanda aka yi musu maganar sa.

Suna da kalaman gane juna, irin ‘Muna tare’, ‘Kin tayar min da tsumi’, ‘Za ki yi daɗin harka’.

Suna son amfani da kwayoyin da za su fitar da cikon halittarsu, kamar ƙirjinsu da mazauni.

Yawancin masu auren cikin su ba sa son haihuwa.

Mace ƴar madigo tana nesanta kanta ga kalaman batsa ga namiji, kuma tana kame kanta.

A kafafen sada zumunci suna ɗora hoton ƙafa, harshe ko kuma leɓen mace da sauransu.

Suna sha’awar saka ɗan kunne ko wata sarƙa a hancinsu (Duk da an mayar da shi ado).

Ba su damu da kulawa da kuma nuna kishin mazajen su ba.

Idan suna kallon fina-finan turawa sun fi mayar da hankali kan matan.

Ƴar maɗigo ba ta sanya kumbar kanti, kuma ba ta barinta ta yi tsayi a ƴan yatsunta.

Wasun su suna rage gashin kan su kamar na maza kuma suna sa masa kala.

Suna yin zanen tatoo mai kusurwa uku (triangle) a hannu ko ƙafarsu.

Waɗannan su ne kaɗan daga cikin alamomin da za a iya gane ƴan maɗigo da su, amma ba su kenan ba. Kamar yadda na faɗi a sama, akwai wasu alamomin da sai su da ke cikin muguwar ɗabi’ar ke iya ganewa ko kuma idan an yi la’akari da abubuwan da suke aikatawa da zarar sun haɗu a tsakaninsu.

Iyaye sai mu kula a duk lokacin da muka ga wata alama makamanciyar waɗannan ga yaranmu ko wacce ke mu’amala da yaranmu mata sai mu yi kokari mu yi wa tufkar hanci. 

Ki nisanci duk wata ƙawa da zata ɗinga bayyana miki tsiraicinta.

Kada ki yarda ƙawarki ta yaba ki ta fuskar sha’awa.

Ki guji ƙawar da zata ɗinga rungume ki da nufin wasa.

Ki tsoraci ƙawar da zata ɗinga kunna miki fina-finan ƴan maɗigo (Lesbian).

Kada ki yarda ƙawarki ta kama hannunki na tsawon lokaci don idan ta Jima tana shafa miki

hannu, da Sannu zata kai ga mabuɗin sha’awa shine ta fara shafa miki ƙirjinki.

Ki nisanci ƙawar da zata ɗinga yawan shafa gashin kanki.

Ki ƙuracewa ƙawar da za ta ɗinga yawan kwanciya a jikin ki bat are da wani dalili ba

Ki kyamaci ƙawar da a ko da yaushe zata ɗinga son ta ɗinga ganin jikin ki, kamar ƙirjin ki da bayan ki zuwa ƙasan marar ki.

Ki rabu da ƙawar da za ta ɗinga yawan yi miki kyaututtuka masu tsada ba bisa dalili ba.

Ki bar ƙawar da take yawan jan ki zuwa gidan ƙawayen ta waɗanda baki san su ba kuma basu da mazaje koma suna da mazajen, amma waɗanda kika ga suna yawan ƙulewa cikin uwar ɗaka ko suke yawan tafawa suna rungumar juna, ko kwanciya a kan cinyar juna ko suke yawan cire tufafinsu a gaban juna ko wanka tare.

Ki kyamaci ƙawar da bata da hira sai hirar mace ƴar uwar ta.

Ki guji ƙawar da Bba ta son yawan mu’amala da maza a matsayin samari ko masoya, amma ta fi mu’amala da mace ƴar uwarta matuƙa ainun.

Ki ƙauracewa ƙawar da take da sha’awar kallon fina-finan batsa musamman irin na mace da mace (Lesbian).

Ki fita sha’anin ƙawar da ake yaɗa jita-jitar tana maɗigo (Lesbian).

Ki rabu da ƙawar da take mu’amala da ƙawaye masu maɗigo (Lesbian). Koda ita ba ta yi domin kallon mai yi ake yi mata kema haka za’a yi miki kallo.

Ki guji ƙawar da take zaman kanta a gidan da ta kama take haya kuma mata ke taruwa a gidanta.

Ki fita sha’anin ƙawar da ba ta jin kunyar cewa aga-aga na ƙirji ko baya ko ƙasan marar Juna.

Wannan kenan game da alamomin mata marasa jin magana fandararru sai a rike kuma.

Alamomin mace 'yar iska
Alamomin mace'yar iska pic.

Post a Comment

0 Comments