Maganin dadewa ana jima'i na Bature da shafawa

Maganin dadewa ana Jima'i na Musulunci

Da farko dai akwai buƙatar mai karatu ya tsaya ya karanta wannan rubutun a tsanake domin neman masalahar wannan babbar matsala idan har ya kasance kana daga cikin masu irin matsalar. 

Duk da kasancewar ba ita kaɗai bace take kawo jin daɗi da morewar zamantakewar aure ba, amma dai saduwa itace kan gaba a jin daɗin auren. Tabbas haƙiƙa saduwar aure a tsakanin miji da mata tana da matuƙar muhimmanci a zamantakewar aure. 

Duk yacce mace takai ga bawa mijinta kulawa a fannoni daban daban kamar; ladabi da biyayya, iya girki, ado da kwalliya, tsabta da dai sauransu, matuƙar ta gaza a shimfiɗa to sunanta sorry fa a idon maigida. Haka nan kuma duk yadda shima namiji ya kai ga nasa ƙoƙarin wurin sauke haƙƙin matarsa kamar; ci da sha, sutura, muhalli, lafiya, da duk wata kyautatawa da zaiyi mata indai ya gaza a wurin mua'malar auratayya tofa gaskiya zaman nasu bazai taɓa daɗi ba. 

Saboda tsabar muhimmancin kwanciyar aure watau jima’i, indai ɗaya daga cikin ma'auratan baya iya biyawa abokin zamansa haƙƙin auren to alƙali da kansa ne yake datse igiyar auren ma'ana dai alƙali yakan raba aure akan ire iren matsalolin nan. Irin wannan ya faru ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba, hakan ya faru fiye da shurin masaƙi. 

Maganin dadewa ana jima'i
Maganin dadewa ana jima'i post

A bisa wannan dalilin ne za kuga daga mazan har matan suke jajircewa wurin ganin sun gamsar sun kuma biyawa junansu wannan buƙatar ta kwanciyar aure. 

Da yawa daga cikin masana daga fannoni daban daban waɗanda suka haɗa da kwararru a fannin lafiya ko kuma ta fuskar addini, kai harma dana ɓangaren sanin halayyar ɗan adam, sun sha yin tata suyi rairaya akan ma'anar gamsar da juna a wurin saduwar aure. 

Amma duk waɗannan ɓangarori ukun sun tattara bayanan sune akan cewa ma'anar ɗaya ce, kuma itace; a samu nutsuwar da zata gusar da duk wata sha'awa bayan an gama saduwar, sai kuma wani lokacin idan buƙatar hakan ta sake tasowa. 

Da wannan ne da yawa daga cikin mutane suke tunanin mutum ba zai iya gamsar da iyalinsa ba sai;

1- Idan yana da al'aura mai kauri ko tsaho ko kuma duka biyun

2- Idan yana daɗewa a wurin saduwa

Hakan ne ya baiwa kamfanunka masu sarrafa magungunan bature, da kuma masu magungunan gargjiya damar samar da ko kuma ƙirƙirar magunguna iri iri wanda suke cewa suna bawa namiji ƙarfin gamsar da iyalinsa yadda ya kamata. 

Komai fa a rayuwa idan yayi yawa matsalane, kamar yadda bature yake cewa ne; too much of everything is bad.. 

To kamar haka ne, abin yayi yawa sosai ta yadda masu waɗannan magungunan suka cika ko ina da ina suna tallata hajojinsu, a chemist, tituna da kasuwanni suna cin karensu babu babbaka. 

Maganin dadewa ana jima'i na Bature

1- Kwayoyi (pills or tablets) 

Waɗannan sune magungunan da ake sha da ruwa ta baki, kuma suna da yawa. Ga misalan sanannu daga cikinsu; viagra, VigRX nitric oxide, Test RX, Gen f20 plus, semenax, prosolution plus, VigRX plus, extenze, da sauransu. 

2- Allura (injection) 

Waɗannan kuma sune rukunan magungunan da akeyin allura dasu, suma kuma misalan nasu suna da yawa domin kuwa kowane kanfanin sarrafa magungunan bature da irin tasu kalar allurar kamar haka; Papaverine, Prostaglandin E1 (PGE1), Phentolamine, Alprostadil, Trimix da sauran misalan da ban ambata ba. 

3- Tiyata (Surgery) 

Wannan shine aikin fiɗa na yanka mazakuta da ake aiwatarwa a ɗakin fiɗa wato theatre room, domin a ƙarawa mazakuta tsaho ko kauri ko duka biyun (Penile Augmentation Surgery) kenan a turance. Ta hanyar sanya wata roba mai kama da jijiyoyin mazakuta (medical grade silicone). Anfi aiwatar da irin wannan aikin a ƙasahen turawa, kuma ko ba'a faɗa muku ba, wannan aikine mai matuƙar tsadar gaske. 

4- Jiƙe jiƙen magungunan gargjiya (herbal concoctions) 

Irin waɗannan rukunan magungunan su suka fi yawa a cikin al'ummar mu. Suma kuma haka akwai na sha akwai na shafawa. Masu ilimin kimiyya basu cika yarda da tsabta ko kuma ingancin irin waɗannan magungunan ba, haka kuma basu yarda da sahihancin ƙa'idar amfani da waɗannan magungunan ba watau ma'ana dai (dosage) ɗin su. 

Maganin dadewa ana jima'i na Shafawa

Waɗannan shafawa akeyi akan al'aura, kuma suma kamar kwayoyi, suna da yawa. Ga misalan su kamar haka; Maxman delay cex cream, Viamax maximum gel, TITAN gel, Doc Johnson power plus delay cream, Man1 Oil Penile Health Cream, Lavender massage oil da dai sauransu. 

Tasiri maganin daɗewa ana jima'i 

Masu amfani da irin magungunan nan suna ganin tasirinsu. Hakan baya rasa nasaba da irin abubuwan da ake haɗasu da shi, kamar ginkgo biloba, ginseng, DHEA, fenugreek, maca da sauransu. 

Wasu chemicals ne watau sinadarai, wasu kuma ana tatso sune daga tsirrai, sa'annan suna sanya ƙaruwar zubar sinadarai (hormones) a cikin jikin ɗan adam. Amma a gaskiya sakamakon binciken kimiyya da yawa ya tabbatar da cewa daɗewa ana amfani dasu yana haifar da illa ga lafiyar mutum. Bayan wannan kuma, idan jikin mutum ya saba dasu, to zaiyi wahala ya iya saduwa da iyalinsa idan baiyi amfani dasu ba. Addition kenan, kaga matsala ta auku. 

Sirrin gamsar da mace wajen saduwar aure. 

Idan mutum yayi wasan motsa sha'awa sosai kafin ya fara saduwa da iyalinsa, mawuyancin abu ne kaga bai gamsar da iyali ba. Wasu sunayin kuskuren fahimtar cewa daɗewa ana saduwa shine kwazo da burgewa. A likitance wannan ba gaskiya bane, domin ana sone saduwa ta zama daga minti uku (3) zuwa sha bakwai (17). Idan takai minti ashirin (20) to tayi yawa domin zata iya sanya ni'imar matar ta ɗauke, daga nan sai ta fara jin zafi, ƙila ma ta sami rauni. 

Amma a lura ba wai ina nufin dole kada a wuce wannan lokacin da ilimin likitanci ya gindaya bane, domin wani ma yana iya kai mintuna sittin, awa ɗaya kenan kuma ba tare da matar ta takura ba. 

Menene abun yi ? 

1- Matsalar ƙanƙancewar gaba gaskiya ce. Idan mutum yana da ita, to ya kamata ya tuntuɓi likita a ɗora shi akan maganin daya dace, maimakon saye da kuma amfani da magunguna barkatai, wanda idan illar su ta taso bai san sanda zai magance ta ba. 

2- Idan ba ya zama dole ba, kada ka sabawa iyali da daɗewa ana saduwa, domin idan ka daina daɗewa daga baya akwai matsala fa. 

3- Ka ƙarfafa wasannin soyayya kafin ka fara saduwa, domin hakan shine babban sirrin gamsarwa a yayin jima'i. 

Ƴan uwa akwai fa’ida wajen jinkirta saurin kawowa a lokacin jima’i, musamman ga masu ƙarfi amma basa daɗewa lokacin  jima’i.

Wannan sirrin yana da matuƙar tasiri wajen hana inzali  da wuri a lokacin saduwa, kuma fa’idar tana da sauƙin haɗawa da sauƙin amfani.

Abinda za'a nema

-Man zaitun

-Vaseline

Za’a haɗasu waje guda a murza sosai sannan a riƙa shafawa azzakari dashi kamar awa ɗaya kafin a kusanci iyali, sai a wanke, muddin kayi haka a ranar nan to lallai baza ka kawo da wuri ba. 

Da farko ƴan uwa ina so kuyi duba zuwa waɗannan bayanai da zanyi muku domin sunfi maganin muhimmanci, kuma yana da kyau indai kana da matsalar da aka lissafa a sama kasan waɗannan abubuwan.

Matsalar mazan yanzu akasari wasu ba cuta ce dasu ba matsala ce wacce ta shafi zamantakewar aure, wasu kuma matsaloli na rayuwa na yau da kullum, amma idan baka san wannan ba, kowane lokaci kaji ana bayanin matsala irin taka sai ace sanyi ace basir ace hawan jini ace iska ce.

Amma idan ka karɓi maganin kasha ba wani bayani kamar kasha ruwa, kasha maganin amma matsalar ka tana nan, kuma mutum bazai zauna yayi nazari ya gano meke damun sa ba, domin munfi damuwa musha maganin matsala ba tare da munsan abinda ya jawo ta ba.

Daga cikin abubuwan da suke jawo saurin kawowa ko ɗaukewar sha'awa akwai waɗannan matsalolin:

1. Gajiya.

2. Damuwa.

3. Rashin bacci isasshe.

4. Matsalar zaman aure tsakanin mata da miji.

5. Rashin samun abinci masu gina jiki.

6. Rashin motsa jiki.

Waɗannan a taƙaice na kawo muku su, idan kuka duba zaku ga duk cikin waɗannan abubuwan babu wata lalura ko cuta a ciki, amma suna daga cikin manyan dalilai da suke jawo rashin sha'awa, rashin jin daɗi da saurin kawowa a lokacin saduwa.

Kana buƙatar bacci mai kyau domin kwakwalwarka ta samu hutu da nutsuwa, kana buƙatar abinci masu gina jiki domin samun sinadarai da jikin ka yake buƙata, kana buƙatar daidaito tsakaninka da iyali domin a duk lokacin da kake buƙatarta, ka zama kana da kwanciyar hankali.

Ɗaya daga cikin abubuwan nan idan ya tafi ba daidai ba, tofa ba yadda za ai a samu jima’i mai amfani, kodai ayi shi babu jin daɗi ko ayi saurin inzali ko kuma ayi amma maniyyi yaƙi yazo, ko azo za ai jima’i gaban yaƙi ya tashi duka irin matsalolin da ake samu kenan.

Saboda haka ƴan uwa ina bamu shawara mu riƙa kiyayewa waɗannan abubuwan, sai ka jika kowanne lokaci da ƙarfin ka da kuzarin ka, a lokacin aiki da kuma jima’i.

Sannan bayani na gaba zan kawo abubuwa da za'a haɗa idan an samu matsala irin wannan domin a samu waraka a rabu da matsalar baki ɗaya.

Duk shekarun ka haka kuma duk rashin ƙarfin ka, duk raunin mazakutar ka, kasha wannan haɗin zaka bada wuta a daren da kake so.

Zaka jima kana jima’i, zaka kuma samu ƙarfi da nishaɗi, zaka samu erection sosai da sosai idan kasha wannan sirrin.

Za'a nemi wadannan abubuwa:.

1. Garin kusbara (Coriander seeds) chokali (3)

2. Garin dabino chokali 1 da rabi

Za'a haɗe su waje ɗaya a chakuɗa a riƙa zuba ƙaramin chokali teaspoon a cikin madara rabin kofi ko nono mai kyau, ana sha awa ɗaya kafin jima’i.

Na tsawon sati uku (3) ko wata ɗaya domin samun ingantaccen ƙarfin jima’i.

Maganin daɗewa ana jima'i da ƙara ƙarfin azzakari.

Wanda yake buƙatar yaga ya jima yana saduwa da mace to yayi ƙoƙari yayi wannan haɗin amma fa idan baka da aure kar ka jarraba.

Zaka samu waɗannan abubuwan;

Carrot guda daya 

Tumatur rabi

Citta ɗanya

Za’a wanke su sai a yayyanka ƙanana sannan ayi blending nasu (a markaɗe su) sannan a zuba zuma chokali ɗaya a ciki a juya asha awa ɗaya kafin a kusanci iyali.

Zakai mamaki kwarai ranar da kasha wannan.

A wani bincike an gano cewa yin jima’i sau uku zuwa huɗu a sati, na taimakawa matuƙa wajen inganta rayuwar soyayyar ma’aurata, ya kuma ƙara danko da ingancin auren shi kansa. 

Wani binciken kuma ya nuna cewa jima’i na ƙara ƙarfafa lafiyar garkuwar jiki ta hanyar samar da wani tsaro na musamman ga kwayoyin halitta hawa na farko dake kare jiki daga kamuwa daga zazzabi da mashaƙo (mura).

Har-ila-yau, jima’i, na ƙara hauhawar kwayoyin halittar Immunoglobin A (IgA). Shi wannan Immunoglobin A na ɗauke da sinadaran “Antibodies” da ke baiwa jiki wata kariya ta musamman daga ƙananun kwayoyin cututtuka dangin bacteria, da virus da toxins (bacteria, viruses, toxins)”. 

Jima’i na taimakawa mace (matar aure) wajen daidaita lokacin al’adarta ya kasance babu tangarɗa tare da inganta samun lafiyayyen bacci.

Jima’i na sanya jikin ɗan adam ya saki wani sinadari mai suna Oxytocin da ke ƙarawa mutum walwala da nishaɗi tare da inganta kusanci tsakanin ma’aurata biyu da kuma barinsu cikin farin ciki a duk lokacin da suka kammala jima’i.

Jima’i na tsawon minti 20 kacal na taimakawa jiki ƙona calories 150 (wani sinadari da ke samar da makamashin zafi ga jiki).

Jima’i shi ne mafi ingancin hanya da ga mutane don samar da nishaɗi, walwala da kuma ƙarfafa danƙon zumunci tsakanin ma’aurata. 

Duk auren da ma’auratan basa iya gamsar da junansu ta fuskar jima’i, aure ne da kai tsaye zaka iya kira da mataccen aure. 

Rashin gamsar da abokin zaman aure, ko shakka babu yayi sanadiyyar mutuwar aure babu iyaka. 

Da fatan za'abi wannan rubutun a nutse daki daki domin fahimtar duk wasu muhimman bayanai daya ƙunsa. Bayan an karanta an fahimta kuma sai a ɗaura niyyar aiwatarwa. 

Da fatan an ilimantu, idan kuma akwai ilimin da fatan an ƙaru. 

Na barku lafiya!

End# maganin dadewa ana jima'i.

Post a Comment

0 Comments