Alamomin mace mai tsananin sha'awa

  Alamomin mace mai tsananin sha'awa post pic#

Alamomin mace mai tsananin sha'awa

Alamomin mace mai tsananin sha'awa

A yau da izinin Allah ubangijin talikai, za muyi magana ne akan alamomin mace mai tsananin sha'awa. Kamar yadda muka sani cewa sha'awa wata ɗabi'a ce wadda ubangiji ya halitta a jikin kowane ɗan-adam kama daga mace ko kuma namiji. Kuma yayi hakan ne domin gwada hikimarsa mai girma da ayarsa ga masu fahimta. 
Related articles

Kai tsaye sha'awa ɗabi'a ce ta son kwanciyar jima'i tsakanin mace da namiji, wanda muke cewa saduwa a wata kalmar, wato namiji zaiji yana buƙatar ya sadu da mace ko kuma ita macen taji haka. 

Sha'awa tanada bambanci a tsakanin mutane domin kuwa wasu sunfi wasu, wato abinda nake nufi shine zaka iya samun wanda a rana yana jin sha'awa sama da sau biyar amma kuma wani ba yayin sha'awa sama da sau ɗaya. Kai wasu ma basa jin sha'awa sai bayan lokaci mai ɗan tsayi kamar duk bayan kwana uku ko bayan mako.

Haka zalika ta ɓangaren mata akwai wanda suke da sha'awa ta daidai misali, akwai kuma masu mai zafi. Kuma za muyi magana ne akan mai zafi wato alamomin mace mai tsananin sha'awa, a matsayinmu na hausawa a duk lokacin da muka ji ance tsanani a wani abu, to munsan abun yayi yawa ake nufi.

Zamu jero waɗanda bincikenmu ya tabbatar mana da cewa suna daga cikin alamomin mace mai tsananin sha'awa a wannan rubutu namu, amma kuma zata iya kasancewa saboda yanayi na bincike ba zamu iya samo komai da komai ba. Amma lokaci zuwa lokaci zamu dinga inganta rubutun saboda masu karatu.

Ga jerin alamomin mace mai tsananin sha'awa kamar haka:.

1. Kasantuwar jajayen idanu.

2. Mace mai yawan nishi.

3. Yawan fushi a tareda mace.

4. Mace mai yawan lalaci.

5. mace mai son shafa gabanta.

Ga bayanin waɗannan alamomin mace mai tsananin sha'awa.

1. Kasantuwar jajayen idanu: 

A yawancin lokuta yadda muka sani shine mata basa da jajayen idanu, kamar yadda maza ke dashi. Yawanci mata koda idanunsu junyi tofa ba sosai yake yiba. To amma ita mace mai tsananin sha'awa zaka sameta da jajayen idanuwa, wanda hakan yana yi maka inkiya da cewa wannan budurwa fa tanada sha'awa sosai. Amma kuma akwai matan da basa da jajayen idanuwa kuma sunada matuƙar zafi ta fannin saduwa. 2/3 biyu bisa uku na mata masu jajayen idanuwa to yana nuni da alamomin mace mai tsananin sha'awa.

Har ila yau kar kayi tunani cewa kowace mace mai jajayen idanuwa wai tanada tsananin sha'awa, a'a akwai wacce ba tsananin sha'awa bane haka halittarta yake.

2. Mace mai yawan nishi

Yawan yin nishi a yayinda ake saduwa da mace yana ɗaya daga cikin alamomin mace mai tsananin sha'awa, domin kuwa wannan nishi da gurnani da take fitarwa a lokacin kwanciya yana faɗa maka cewa tana jindaɗin abinda ke wakana a lokacin jima'in. A duk wani bayani ya kamata ka fahimci cewa zata iya yiwuwa kuma ba tsananin sha'awa ne ya kawo hakan ba, kawai tsari da zubi na halitta ne a haka.

3. Yawan fushi a tareda mace: 

Fushi yanayi ne na ɓacin rai da muke shiga sakamakon faruwar wani abu, to amma fa yana ɗaya daga cikin alamomin mace mai tsananin domin kuwa ita mace mai yawan sha'awa to zaka sameta tana yawan shiga fushi ba gaira balle saba, wato ba abinda aka yi mata da ɓacin rai saika ganta tana neman yin masifa ita kaɗai. Dama hakan ya zame musu kamar jiki musamman harijan mata, idan ka auri mace ka ganta da irin wannan halin to ka tabbatar da cewa tana matuƙar buƙatarka a koda yaushe kamar yadda tuwo ke buƙatar miya.

4. Yawan lalaci: 

Lalaci da yawan kasala yana ɗaya daga cikin alamomin mace mai tsananin, duk da a bincikenmu bamu samu ingantaccen bayani ba, amma mun tabbatar da shigowar lalaci yana daga cikin halin mata masu matuƙar sha'awa. Kuma kasan mene matsalan shine su bawai sai sunyi aikin wani abu suke jin gajiya da kasala ba, a'a hakanan kawai suke shiga cikin wannan hali ba tareda dasu kansu sun san meke faruwa ba, wata kuma daga baya tana fahimtar meke faruwa da ita.

5. Mace mai son shafa gabanta: 

Kayi sani cewa wannan shafar gaban da sukeyi tana ɗebe masu kewar jima'in da basu samu bane, bawai suna saka hannu bane suyi ta kwakule-kwakule a'a illa iyaka dai suyi amfani da tafin hannunsu su shafi saman gaba, domin su ragewa kansu sha'awa, wannan yana ɗaya daga cikin alamomin mace mai tsananin sha'awa. Wasu matan kuwa suna yawan matse matse koda ba suyi amfani da hannu ba.

Ɓangare na biyu a cikin bayanin alamomin mace mai tsananin sha'awa:.

Shi wannan ɓangare yawanci yayi magana ne dangane da rawar da ƙafar mace ke takawa wajen nuni da ɗabi'ar sha'awarta.

Yar uwata ga shawara kyauta kuma mai matuƙar amfani. Ki ɓoye ƙafarki yafi ki saka niƙabi domin ɓoye fuskarki idan zaki fita waje.

Yan'mata kiyi sani cewa Idan namiji ya kalli ƙafarki indai yanada ilimin sanin abun, to tamkar ya kalli ƙasanki ne, jindaɗi ne kawai ke dashi baku yi ba.

Ga wannan asirai na alamomin mace mai tsananin sha'awa ta fannin ƙafarta.

1. idan yatsar ƙafar mace ta kusa da babban ɗan yatsa tafi babbar ɗan yatsar tsawo to hakan yana nufin wannan macen tanada ƙarfin sha’awa.

Haka zalika idan kuma babbar ɗan yatsar data kusa dashi suka zo tsawo ɗaya to macen tanada saukin sha’awa.

2. idan babbar ɗan yatsar mace tanada girma sosai da kuma tsayi to hakan yana nufin gabanki yanada ƙofa babba da kuma tsayi.

Idan kuma ya kasance babbar yatsarki ba babba bace sosai kuma batada tsawo to hakan yana nufin gabanki bashi da ƙofa babba wato a matse kike, kuma baki da zurfi gaba sosai.

3 idan kuma mace tanada wushirya a ƙafarta wato duk tsakanin yatsunta akwai yar ƙaramar tazara ba sosai ba, to hakan yana nufin kinada ni’ima, kuma kinada daɗi a jima’i, haka zalika kuma kinada sha'awa mai ƙarfi.

4. Idan diddigen mace yanada cika babu rama a cikinsa to shima hakan yana nuni da tanada juriya wurin jima’i, duk ƙwawar namiji zata iya ɗauke buƙatarsa.

End of the alamomin mace mai tsananin sha'awa article.

Post a Comment

0 Comments