Alamomin mace mai dadi

Alamomin mace mai dadi

A cikin wannan rubutun zan amsa wannan tambayar alamomin mace mai dadi da maza suka kai gauro kuma suka kai mari suna yinta. Wannan tambayar dai ta daɗe tana yawo tana kuma damun zukatan ƴaƴa maza ba wata tambaya bace illa "waɗanne alamomine na mace mai daɗi? Wannan tambayar ta daɗe ko nace ta jima a cikin zukatan ƴan uwana maza. 

Yaku maza, ko daga ina kuke a faɗin duniyar nan matuƙar kuna jin yaren hausa, ko kuma zaku iya fassara wannan rubutun daga yaran hausa zuwa wanda kuke ji, to kusha kuruminku domin kunzo dai dai wurin da zaku gamsu cewar tambayoyinku sun amsu idan kuka biyoni a sannu cikin abinda zan muku bayani a rubuce har inda zan dasa aya tare a ajiye alƙalamina. 

Wannan tambayar dake damun zukatan ƴaƴa maza abun yana bani mamaki fa, to amma dai ban zargi maza ba musamman ma matasa watau samari, ko nace ahababu a yaren larabci, wadanda kuma zan iya kiransu da youth a turance, sakamakon sune ke auren mata, ba mata ke aurensu ba.

Shi yasa yana da kyau mutum ya san wace irin mace ya aura, ko kuma zai aura domin ya zabi daidai da shi.

Cigaban wannan rubutun an zaƙuloshi ne, watau extracts daga irin irin rubuce rubuce da akayi na irin abubuwan da suke da alaka da tambayoyin naku, watau alamomin yadda zaku gane mace mai daɗi. Hakan na nufin wannan rubutun zai kawo muku bayanai wanda aka binciko a cikin irin rubutun da akayi a baya. 

Alamomin mace mai dadi post Conti..

Wai Da gaske Ne Wata Tafi Wata Daɗi? 

Duk wata mace tana da daɗi sai dai idan itace taki ta zama mai daɗin. A taƙaice amsar wannan tambayar itace mata dukkaninsu sunabda daɗi amma sune zasu iya tabbatarwa mazansu hakan. 

Mata ƙananansu da manyansu an juya musu kwakwalwarsu da tunanin ai mata ba duka suke da daɗi ba. 

Wannan yasa maza suke raina musu hankali na nuna musu ita da yake tare da ita a yanzu tafi wacce ya baro wajenta daɗi. Hakan ya jawo mata suke yiwa junansu gori.

Haka nan idan namiji yana son ya wulaƙanta mace musamman idan neman ta yake babu aure zai ke faɗa mata bata da daɗi, hakan zai sa ta shiga cikin mugun tashin hankali ance mata bata da daɗi. 

Ƴan mata kina da daɗi amma dai hanyar tabbatar wa duk wanda zai sadu dake hakan ko akasin hakan.

Akwai kuma matan dama mazan da suke ɗauka cewa yawan ni'imar jikin mace suke sa tayi daɗi. 

Anan ma ziro ne amsar domin ba haka bane. Da akwai mazan da kwatakwata basu son yin mu'amalar kwanciya da macen da take da yawan ni'ima sosai.

Domin na tabbatar maka cewa duk wata mace tana da daɗi, sai na soma faɗa maka matakan dake sa mace daɗi da kuma abunda yake hana ta, waɗanda kuma sune alamomin da zaka bi ka gane ita ɗin mai daɗi ce ko a'a, kafin daga bisani nayi maka bayani filla filla. Gasu kamar haka;

Soyayya 

Buƙatuwa

Tsafta 

Yin abinda namiji yake so

Sakin jiki

Yanayin kwanciya 

Sadarwa a lokacin tarawa 

Sumbatu

Ni'imar mace 

Yanayin kawowar mace

Ya kai namiji ni ɗin nan namiji ne ɗan uwanka, kar ta san kar kenan inji hausawa, nasan maza suna jin daɗin mace idan suna soyayya da ita kuma kaima haka yake a gunka. 

Menene Yake Sa Mace Tayi Daɗi

Soyayya: Kamin namiji yaji daɗin tarawa da mace, sai har idan akwai soyayya ta gaskiya a tare dashi da wannan macen da zai tara da ita.

Duk namijin da zai tara da wacce yake sonta, babu makawa la budda kenan inji balarabe, sai yaji daɗinta. Amma idan babu soyayya a tsakaninsu zai biya buƙatarsa ne amma ba domin yaji daɗin tarawar ba. 

Saboda jin daɗin tarawa ga mutum namiji sai idan yana da natsuwa da wacce yake mu'amalar da ita. Saboda shi wannan abin watau jima'i jin daɗin sa ba a ɗanɗano ake jinsa ba daga zuci yake. A zuci ake jinsa. 

Buƙatuwa: Kamin namiji yaji daɗin tarawa da mace sai har a daidai wannan lokacin ya kamu sosai na buƙatar yin jimai. 

Duk wani ni'imar mace muddin namiji bai ji ya matsu ko zumuɗin ya sadu da ita ba. Koda yayi bazai ji daɗinta ba. 

Don haka kafin mace tayiwa mai saduwa da ita daɗi sai har in yana tsananin son tarawa da ita.

Ka lura, duk mutumin da bai jin yunwa ko sha'awar cin abinci ko wani kayan kwalama, idan aka tilasata shi sai yaci cushe kawai zai yi yana ci yana gunguni. 

Amma da zaka kawo masa waɗannan cimar a lokacin da yake tsaka da buƙatar su. Zaka ga irin zumuɗin da santin da zai riƙa yi a lokacin da yake cin wannan abun. Wannan shine misalin da zaka fahimta.

Idan da za a kawo maka macen data fi ko wacce mace kyaun halitta amma baka da sha'awar yin saduwa a wannan lokacin, sai dai ka biya wa kanka buƙata amma ba zaka ji daɗinta ba.

Tsafta: Shima abu ne da ke sa mace tayi daɗi ga mijinta. Da zaran mace zata tsaftace jikinta, da ɗakin da ake kwanciyar auren to tabbas zata yiwa mai tarawa da ita daɗi.

Daga lokacin da namiji yayi karo da doyi, wari ko hamami daga jikinki musamman ma gabanki. Daga wannan lokacin sha'awar mijin naki zai yi ƙasa. 

Wanda hakan shine abunda zai jawo miki rashin daɗi ga wanda yake sarrafaki.

Hakan yasa duk tarin ni'imar da mace take dashi muddin babtada tsafta mijinta ba zai taba yin saduwa da ita ba saboda ya ji daɗi, sai dai domin kwantar da sha'awar sa.

Yiwa Mijinki Abunda Yake So: Matan da basa yiwa mazansu abunda suke so kafin lokacin da bayan kammala tarawa abunda suke so, wannan macen bazata yiwa mai saduwa da ita daɗi ba.

A lokacin wasannin motsa sha'awa. Idan mace ta fahimci mijinta mai son abu kaza ne, ko kuma abu kaza yake so, ya kamata ta naƙalci waɗannan abubuwan ta riƙa yi masa su. Idan har mace zata kauda kunya da duk wani tunani a ranta tayi wa namiji abinda yake so a shimfiɗa to zaiji daɗinta. 

A lokacin gudanar da saduwa nan ma akwai wasu abubuwan da maza suke son matansu na musu, wanda hakan yana ƙara musu daɗin saduwa da su. 

Haka ma bayan kammala saduwa akwai abunda namiji yake son matarsa tayi masa.

Muddin mace bazata nutsu ta gano waɗannan abubuwan ba, koda shekaru nawa zasu yi zaman aure bazai ji daɗinta ba domin bata masa abunda yake so.

Alamomin mace mai dadi post Conti..

Sakin Jiki: Duk macen da ba zata saki jiki ba tayi saduwa da mijinta ba. Wannan takura kan nata datayi zai shafi jin daɗin da mijinta zai ji.

Akwai matan da sunanan kamar gawa sai yadda aka juyasu, idan aka nuna musu abunda ake buƙata daga wajensu basa yi. Saboda kunya ko kuma rashin sabo. Irin waɗannan matan sam basu da daɗi a wajen maza.

Saboda ana samun wasu matan musamman ma amare wai kada ace sun ƴan iska ne. Sai suki sakarwa mazajensu jiki. Wannan ba ƙaramin kuskure bane kada ki zama hakan muddin dai kina son mijinki yaji daɗin saduwa dake.

Yanayin Kwanciya: Mata da yawa basu iya ƙirƙiro yanayin kwanciyar saduwa ba. Irin waɗannan matan idan suka kwanta suna kallon saman ɗaki har mijinsu ya gama ya rufe basa motsawa basa cewa komai. 

Idan kinason mijinki yaji daɗin saduwa dake, ki gano yanayin kwanciyar da mijinki yake so ki riƙa masa kamin ma shi ya miki da kansa.

Muddin zaki rika ƙirƙiro muku yanayin kwanciyar saduwa daban da wanda kuka saba yi a kullum sai mijinki yayi kwaɗayin saduwa dake a kullum . Amma idan zaki zube masa kamar kayan wanki to ki sani bazai taba jin daɗin ki ba har abada.

Sadarwa A Lokacin Tarawa: Shi ma yana sa mace tayi daɗi a wajen mijinta. A lokacin tarawa maza suna son mace ta riƙa tambayar su yadda suke ji da halin da suke ciki da kuma abunda suke so a musu. Idan gaban namiji ya saɓule zuwa waje saboda tsantsin gabanki, kama ki mayar ciki tare da bashi haƙuri, da kuma neman sanin wannan yanayin ya masa ko dai ku sauya.

Sadarwa a lokacin tarawa ba ƙaramin samawa maza jin daɗi yake ba. Yana kuma tsayawa a ransu. 

Sumbatu: Daban yake da sadarwan tarawa. Domin shi sumbatu ga mata masuyi ba komai suke iya tunawa sun faɗa ba. Amma a sadarwa komai zata furta tana sane.

Haka zalika shi sumbatu yakan sa namiji ya fahimci cewa bada ƴar tsana yake saduwa ba ko gawa ba da mutum ce.

Maza masu son mace mai yawan sumbatu a lokacin saduwa wannan surutun nata na rashin kan gadon da ta keyi yake sama musu jin daɗin. 

Maza suna matuƙar ɗokin yin tarawa da mata masu sumbatu saboda yadda yake da tasiri a kwakwalwar su. Waɗannan kalaman na batsa da kambama maza da mata masu sumbatu suke yiwa mazajensu suna ƙarawa saduwa armashi. Wasu mazan koda sun fita harkokin nemansu bayan abun ya faɗo musu sai suji suna marmarin matansu. 

Ni'imar Mace: Tabbas mace mai ni'ima tana samarwa mijinta jin daɗin saduwa da ita. Duk da ba ko wani namiji bane yake iya jimawa yana saduwa da macen da take da ni'ima a jikinta sosai, saboda yadda ruwan gabanta yake da yawan da nan da nan zai sa tsantsin gaban mace zai kwasheshi ya kawo.

Maza na iya jin daɗin saduwa da mace mai yawan ni'ima ba kamar macen da gabanta yake a bushe ba.

Duk da hakan mace mai daskararren gaba zata iya jiyar da namiji daɗi musamman idan zata iya masa wasu daga cikin abubuwan da aka ambata a sama, tana da zaɓi da yawa da zata yi amfani dasu. 

Yanayin Zuwan Kanki: Ga mata masu zuwan kai na gaskiya ba masu ƙirƙiro shi ba saboda sun gaji ko suna son su daɗaɗawa mazansu ba. Maza na jin daɗin saduwa da su.

Kada kiyi zuwan kai haka nan kawai ba tare da kin alamtawa mijinki gaki nan zuwa ba.

Wannan ƙara ihun da ƙanƙame namiji da suke yi a lokacin zuwan kansu, wani lokacin shike jawo shima namiji yayi.

Kada ki zama kurma idan kika zo yin zuwan kai. Saki jiki sosai ki sanar masa yadda ya kaiki ƙololuwar jin daɗin saduwa. Kada sai bayan an gama ki riƙa cewa kinyi zuwan kai sama da ɗaya, alhali shi bai ga wasu alamun hakan ba.

Alamomin mace mai dadi
Alamomin mace mai dadi pic

Alamtawa mijinki zaki kawo, ihunki da kalamanki a wannan lokacin da yanayin suna sa namiji yaji daɗin saduwa dake. Irin waɗannan abubuwan ne suke sa maza zumuɗin matansu.

Da waɗannan alamomin guda goma dana lissafa nayi bayani akansu nake cewa a huta lafiya!

Post a Comment

0 Comments